NA CANCANTA! 50
Na
Halimatu Ibrahim KhalilAdabi Writers Association
Masu buƙata daga farko su duba a wattpad ga username ɗina ko su tuntuɓeni ta whatsApp numberna amma shima iya 43 Pages gareni document ɗin shi
Wattpad: HalimatuKhalil
whatsApp Number:08124915604Masoya wanda na sani da wanda bansani ba ina godiya bisa biyayyar littafin nan da kukeyi da haƙuri bisa yawan tsaikon da ake samu
**
50Da sauri na na ƙara so cikin ɗakinmu inda nake jiyo ƙarar wayata inda take na nema da sauri sunan da na gani ya sani ƙara faɗaɗa fuskata da murmushi
"Aunty"nayi maganar ina saka wayar kunnena
"Assalamu alaikum Aunty ina yini"
Tsaki naji Auntyn tayi"sallama dai na amsa Wa'alaikumussalam kada ladanta ya kubcemin amma batun yini bansanshi ba"
Da damuwa fuskata ƙarara na yi saurin cewa"Aunty mai muka aikata haka,kiya haƙuri?"
"Au kun manta abinda kuka yimin oya jeki ki kaiwa Mamarku wayar nan,naji matsayina a yanzu a wajenta,ace abun alkhairi ya sameku saboda bata hannuna ya samu ba taƙi shaidamin nice kaɗai mai san tarena da Hauwa'u na sani tuni batun yau ba.."
Ni dai tunda na gano bakin zaren maganar na cire wayar kunnena jin faɗan Auntyn bazai ƙare ba nayi saurin miƙewa harda gudu guduna na nufi kitchen dani ma daga Kitchen ɗin na jiyo ƙarar wayartawa kasancewar Kitchen ɗin jikin ɗakin namu yake
"Mama ga waya Aunty na magana"
Mama ta zaro ido ta miƙo hannu na miƙa mata waya
"Rumaisah kuma lallai yau na bani wajen Rumaisah nasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi"Ni dai murmushi nayi na furta"Ki saka a kunne tanata magana fa"
Ina gama faɗin haka na fice daga Kitchen ɗin ɗaki na koma na naja filo na kwanta dan a mugun gajiye nake tamkar anyimin duka ayyuka mukeyi a gidan kullum yini muke aiki tunda zancen komawarmu ya gabato sa'armu ɗaya anyi hutun babbar sallah ma da gajiyar zata fi haka
Tunani tsundum na faɗa musamman na Juraid babu ƙarya naso Juraid kuma ina ƙara sansa bansan ranar da zan bar hakan ba dukda yanayin rayuwa bansamu damar nuna masa hakan ba a zahirin gaskiya kusan kullum faɗa yakeyi
"Sumayyah kamar bakya so na nake tunani"
Idan ya faɗi hakan nakanyi murmushi"Mai kagani a tare dani"
"Kawai hakanan na faɗa sainaga kamar bakya maraba dani wani lokacin ina samun ƙarancin kulawa a gareki"
Ni dai saidai nayi murmushi inasan Juraid fiye da yadda zan fasaltasa a raina sai dai inada yaƙinin Juraid a yanzu ya tafi babu lallai ya dawo dukda bai nunamin haka ba a lokacin da abun ya faru amma a yanzu shirunsa na kwana biyu yana sake tabbatarmin da cewa ya barni ɗin kamar yadda akafi son hakan gareni hakan nacigaba da saƙa da warwara tunanin ya cigaba da addabar ƙwaƙwalwa ta
"Ungo wayarki Halima na bugowa"
Da sauri na juyo jin furucin Mama na amsa wayar a hannunta ina ƙoƙarin duba wayar Mama ta kalleni
"Ta katse ai saiki jira ta sake kira idan tunanin naki ya barki kinji ƙarar wayar"
Mama na kalla tare da saurin nuna kaina
"Mama ni kuma ke tunani?"Mama ta nemi waje gefe na ta zauna dafani tayi sannan ta fara magana
"Nayi sallama aƙalla sau uku shigowata amma hankalinki baya tare da jikinki kin sallamawa zuciyarki shi hankalin naki,Sumayyah kan Juraid duk kike wannan damuwar ko?"
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.