7

58 7 0
                                    

7
Da farin cikin da yakasa 'buya a gareni har ya bayyana ga fuskata dashi na isa gida ina kwa'da sallama Mama da naci Karo da ita tsakar gida tana zuba ruwa tukunya ta amsamin tana mai maida kallonta gareni
"Lafiya kuwa, Sumayyah irin wannan fara'a haka?"
Na 'dan turo baki nace
"Kai Mama kin manta yau muka gama exam ta qualifying"
Ta ce
"Yo ai harna manta yi haquri Sumayyah"
Murmushi nayi a raina ina ayyana mama kenan ita ba ruwanta ko yaron goye idan bata masa dai-dai ba tana iya basa haquri tunanin da nake na katse na ce
"Mama ina Khalil,ko har yau ba'a taso su makarantar ba"
Mama da take qoqarin 'daukar tukunya ta ce
"Na aikesa ya siyomin fulawa,jeki ki 'dauki Humaira na barota ita ka'dai 'daki"
"Yawwa Mama yau wainar fulawa za'ayi ko?"nayi maganar ina fara tafiya
"A'a sai dai wainar qwai qarewar ta fulawa,yadda rayuwa tayi tsada zaki ce wata waina tama fulawa za'ayi to yarinya 'dan wake za'ayi"
Na zun'buri baki jin abinda Maman ke fa'da na ce
"Kai Mama daga tanbaya"
Tsaki tayi tare da cewa"Au tanbaya ce kenan,ki jini da yarinya 'yar rainin wayau,ni wuce ki 'daukarmin 'yata karta tashi taji ba motsi,ki je da'kinku da ita,ki shirya ki ki kawan ita kizo kiyi kwa'bin 'dan waken"
Ba tare da nace komai ba ina qunkunai na shiga 'dakin Maman tamu da inaji Maman na cewa
"Oho dai yau yin 'dan wake babu fashi"
Saina iya cewa a rayuwata bani qaunar 'dan wake shiyasa ko kusa bana ci idan ko naci sai dai idan inajin yunwa
Aisha na kinkima kawai na baro 'dakin kayan na cire na koma kitchen da na tarar dawowar Khalil kenan daga siyo fulawar kwa'bin mama ce tayi daganan ta anshi Humaira tabar kitchen din badan naso ba na jira tukunyar ta tafasa na fara sakin 'dan waken cikin minti talatin na kammala na taqo plat da abuna na shiga 'dakin Mama  ina ci
Mama ta dubi 'dan waken da nake baza uwar loma
"Ke Sumayyah keda ba kya son 'dan wake ya zakiyi da wannan da kika zubo,khalil yasa hannu kuci tare"
Na ce
"Mama yunwa na keji shiyasa,da khalil 'din zanci abinci yayi ta'be ta'be da hannun nasa"
Mama ta ce
"Kya yi dai gulmarki kya gama,kuma Khalil 'din bawan Allah mai ya ta'ba"
Nace
"Kai Mama muma ai bayin Allahn ne,kawai dan yaron yaci sunan Abbanku shikenan aita gatantasa,mu Kuma kakanmu ne fa, both side"
Dariya Mama tayi ta ce
"To ya ranki"

Nima nayi dariya ba tare dana bata amsa ba
Na kalli Khalil da yake ta kallona nace masa
"Jeka ka wanko hannunka da ragowar klin 'din da nayi wanke wanke da safe,saura kuma ka karar da klin 'din"
Kamar jira yake nayi maganar ya fice da gudu na bisa da da kallo Allah sarki Khalil idan ban mantaba yau cikinmu ba wanda ya karya muka tafi makaranta yau dole ne ma muji yunwa,nasan yanzunma da alama bashin fulawar aka ciyo sai abunda Abba ya samu yau idan ya dawo za'a bada kudin
Shiru ne ya ratsa tsakanina da Mama da lokacin har Khalil ya wanko hannunsa ya fara cin abincin
Mama ce tayi qoqarin katse shirun namu ta hanyar cewa
"Sumayyah kina addu'a kuwa akan qualifying 'dinnan taku kinsan komai kokarinka su irin wa'dannan jarabawowin sai da addu'a,tunda kuka fara jarabawarnan bana iya rintsawa saina kaiwa Allah buqatata akan jarabawarnan da kukeyi,yau ko da kanada yaqinin za'a samu ku'din biyama jarabawarnan kowa yanada burin yaga yaci,bare kuma ke da babu yaqinin hakan idan baki ci ba sai dai ki haqura da karatunnan dan kinsan ko gona Abbanku baida ita tasa takansa"
Kai na 'daga da hawaye suka wankemin fuska tunda mama ta fara maganar nan dan nima zullumina kenan murmushi nayi ina share hawayena na ce
"Mama ina addu'a duk abinda zaifi zama alkhairi a rayuwata ya ha'dani da samunsa"
Mama ta jinjina kai tare da cewa
"Haka ne Sumayyah kinyi tunani mai kyau,Allah ya baku sa'a ke da su Halima da sauran qawayenki dama duka musulmai"
Nayi murmushi nace
"Amin Mama"
Mama kenan rayuwarta tana burgeni tasan yakamata ita dai inada yaqinin da Allah zai azurta mamanmu ba makawa zata kyautatawa 'yan uwanta fiye da tunanin mai tunani sai dai ita haka tata jarabtar take,da inada yaqinin suma masu ku'din jarabtarsu ce Allah ya basu ku'din da a dalilinsu idan basuyi wasa ba sai su halakar dashi
"Anjima idan an taso su Rumaisa makaranta saiku shirya kuje gidan Mama Atika ku yinar mata,kun da'de baku je ba"maganar da mama tayi ta katsemin tunani na na kalli Maman sororo jin kalmar da take fa'da
"Kike kallona ko ba kiji mai nace bane"fa'din Mama
Na 'dan rausayar dakai na ce
"Naji Mama amma gaskiya banason zuwa gidan Mama Atika,dukda bata da matsala amma 'ya'yanta ko gaishesu mukayi basu amsawa kuma na fa'damiki irin abunda suke mana a banzace suke kallonmu gaskiya mama kiya haquri nidai ba zani ba"
Mama cikin fushi ta fara magana
"Sumayyah na gaji da kalmomin 'batanci da kike jifan dangina,danni dangina ba irin dangin ubanku bane,da dai danginku kikace suyi haka ina iya yarda,amma kowa yasan Mama Atika irin alkhairin da take mana dukda ba cikinmu 'daya ba amma qannen Abbanku da suke ciki 'daya ba wanda zai iya bugar qirji ya kawo muku koda kwancen 'ya'yansu kusa,ina laifin Mama Atika wannan atamfar holland ta jikinki ba kwance Malika 'diyarta bane,da wulakanci suke maku idan kunje ina zasu baku kaya,dan haka saikinje bazan zura ido aqi zumunci ba idan dangin Abbanku basu sanku ni nawa suna sanku"
Baki na zun'bura na ce
"Mama ba zaki gane bane,amma 'ya'yan mama Atika idan mukaje wulaqanci suke ma..."
Mama data kawo hannu zata bugemin baki nayi saurin rufe bakina da qunshe sauran maganata
"Idan kika qara yimin magana saina mareki sakarai kawai"fa'din Mama da nasan a dalilin ita Bata zuwa gidan Mama Atikar sai dai ta turamu ta fa'di haka amma irin kallon banzar da ake mana da yada mana magana da akeyi idan mukaje abin ba 'karamin 'konamin rai yake ba shiyasa rabon da muje mun da'de tun sanda mukaje da kwancen kayan Aunty Abida 'diyar Mama Atikar a jikina muna shiga gidan Aunty Abida da tana ganina cikin 'kawayenta ta fara cewa

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now