16

42 7 0
                                    


16.

Da tunanin wayarmu da Hamid na farka na Fara yini na da ita ina sake jin shi kamar mun jima da Fara soyayya daga ha'duwar mu zuwa yanzu na bashi matsayi mai girma nake ji a raina,zullumina 'daya a yau 'din wani kallo zai samu daga ni harshi wajen Abbah Hashim da tunanin na cire ta gumin da nayi na shiga toilet wanka na yi nayi alwalar sallar walha,dan kafin na shiga naga 9:30am lokacin Kam yama da'de dayi,shirina nayi cikin riga da siket atamfa mai black da coffee,batik ban tsaya dogon kwalliya ba,na fara tada sallahr sai da na idar na shafa powder da lipgloss a baki nasa brush na gyara girata kwalli ma ban tsaya nemanshi ba,dan bani da ma shi Dan kwali nayi zaman daurawa na nemi farin mayafi na aje gefena,kiran da naji wayata ya sa gabana fa'duwa sunan ubangiji na kira kafin na duba na ga mai kiran,Yaya Samir ne hakan yasa nayi saurin 'dagawa

"Kin manta da break fast yau kenan naga baki fito amsa ba ko duk murnar wayar ne"

Murmushi nayi kafin na bada amsa naji muryar Fatimah
"Yaya yaushe kuma tayi waya,Ni inata fama ko Kai ko Abbah wani ya siya min sabuwa kunqi,nasan ma kaine zaka siyama ta"

Tsaki naji yayi"Tanbayata kikeyi ko meye idan zakiyi shiriritarki kuyi da AbdulMalik"

Naji yana "kina jinah Sumayyah kizo ki dauki abincinki"

Murya a sanyaye "toh Yaya Samir"

Wayar ya katse ni ma na cire wayar kunne ina kallanta a raina ina sake ayyana ni da ma ya barta, ni takamaimai bansan anfanin da zata yimin,gani ma ina da gudun rigima akan waya,dama duka suna Yaya Samir ya fi sona a kansu,tom Ina ga sunji kawunsu yama siya min wayar gwiwa a sake na miqe na fita a qaton Dining Table na wuce su ina gaida Ummi da Abbah da Yaya AbdulMalik,Yaya Samir,duka da lafiya suka amshe dama nasan Yaya Samir baya tsawaita amsa gaisuwa duka harara suke miqamin musamman Abbah da Fatimah,ita dama exactly halin babanta gare ta,har gwara Yaya AbdulMalik yafi da na Umminsu,kawai saboda Fatimah ne da yadda Abbah ke nunamin suma suka fara tom bai nuna ina da muhimmanci ba a wajenshi bare su,har na shiga kitchen na gaishe da Baba Indo na dauki abincina na fito,zan wuce na na koma 'daki naji muryar Yaya Samir
"A'a Sumayyah shigo ki zauna falo,na ga ma kinci kwalliya haka Abid ko yau ma Ummi zata aike kune"

Ina koqarin qarasawa na zauna Ummi ta fara"Samir bani son iskanci fa a aiken zan qare,sun janyomin Mahmud na tamin sababi na aikesu cikin rana nasan ana matsalar abin hawa unguwar nan,ni kuma nasan da mashiririciya na ha'da aiken kaga uwar kwalliyar da take fa"ta nuna masa ni ina qoqarin zama da dai mamaki tom tunda ni mashiririciya ce baga Fatima ba ta aiketa maganar Fatiman naji

"Ummi sai da nace ki Bari zanje,ni da mai ma ban tsaya shafawa, gashinan ai tayi sabar waya wa ye ya sani ma ko Kawu Mahmud ya siya mata saboda Aunty Asma'u,an bi an damemu suna Kama,har banasan zancen mukaje Gwarzo ma,su Khairat su bi su damu mutane,ni Aunty Asma'un ma haushinta nake ji"

Ummi naji ta fara magana cikin fa'da"Kinga fatima ki kiyayeni da zancen Asma'u karta kirani waya ta nemi cimin mutunci ki tsaya kan Mahmud shi take wasa daku,kinsan halin Asma'u batun waya ko ta millions zai siya mata ba ruwana,a cikin ku idan akace da munafukin da yake shirin fa'dawa Asma'u ma ke ko recording zasu iya yi,har Abban naku da kike biyewa,indai maganar Asma'u ne ware ki zaiyi,ba zan iya da halin Asma'u ba, shiyasa hanyar gidantama banaso na sani"

Abbah naji ya fara"Kinga Khadijah,idan kina magana da 'yar ki ki daina sani a ciki,kunfi kusa da Asma'u da ta zauna nan wanne shiri ba kuyi ba,sai yanzu,dan bata auri naki ba ki kasan da rashin mutuncinta"

Ummi na ji ta daura"To ni dama ai nasani, Asma'u ba tada mutunci,dana ga Kamar da gaske zasu dai daita da Mahmud ne da farko,tom ta raina arziqinshi lokacin ana zugata ana sai mai wasu trillions gefe, gashinan Mahmud shima yana dasu,har ya siyawa 'yarku waya da kuka kasa ubantama baku rufamasa 'dakuna ba,a cikin gidanku ya dawo ya zauna,sai nan gaba kunu na iko kan 'ya'yan shi,sun gama wahalsu"

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now