NA CANCANTA
Na
Halimatu Ibrahim Khalil46..
A tsaye ƙofar gida na hangoshi ina fitowa daga cikin gidan namu idanunsa na kaina hakan yasa na maida kaina ƙasa ina jin faɗuwar gabar data zarce wacce nasha jinta a baya game da Juraid addu'a nake a zuciyata har na ƙara sa inda yake ɗin sallama na gabatarmasa muka gaisa shiru ya ɗan ratsa tsakaninmu
"Sumayyah!"
Jin ya kira sunana gaba ɗaya abinda bai taɓa yi ba yasani saurin ɗago kaina na kalleshi da ƙaruwar faɗuwar gaba, Kallon da naga yayimin ya sani ɗan sakin masa murmushi domin kallon baya nuna alamun komai a yanda kwayar idanun nasa ta nuna bai kai ga sauke idanuna ba daga garesa naji ya furta
"Zaki kalleni mana gaba ɗaya kin manta da zancen Jurayd rabuwata dake tun a asibiti ko ɗan flashing ba zaki taɓa yimin ba ko?,na ɗaga miki ƙafar zuwa ko waya saboda yanayin jikin Mama kawai"
Murmushi harda fiddo haƙora na aikawa Jurayd jin baiyimin zancen da nake tsammanin zaiyimin ba a raina nayi godiya ga Allah inasan Jurayd da bansan yaushe na fara ba bare na san yaushe zan daina soyayyar Juraid daga Allah ce gareni amma nasan akwai wadda takasance dalilin kyautayinsa a kaina Jurayd wani jigo ne da ya kawomin yayuwar wani zafin da nakeji zafin da yake zama dalilin kassara matasan ƴammata a yau zafin da bana komai bane face na talauci nasan waɗanda basu ɗanɗanesa ba zasu kalli dukkan maganata a haukace sai dai dukda hakan ba zan musu fatan kasantuwarsu cikinsa ba su ɗanɗanesa ba saidai fatan ubangiji ya shiryar dasu bisa fahimci zancen nawa ko hakan zai kawo canje canje masu ɗumbin yawa da nake fata ya wanzu ga al'umma musulmai mu zama masu koyi ga shugaba abin koyinmu ba wai ya zama ta iya faɗa a baki kaɗai muke da tabbacin halayyoyinsa ba maɗaukaka
"Sumayyah!!"Zan iya cewa har firgita naji da kiran sunana da Juraid yayimin a tsakiyar kaina,Da hakan ya fargar dani tabbas gaban Juraid nake ba a ɗaki nake kwance ba
"Na'am"Na iya furtawa a tsanake
Tsareni yayi da ido sannan ya ce
"Amma baki tare dani ko?,Bansan ma ko kinji abinda na furtaba?""Naji mana kuma ina tare dakai"Nayi maganar ina cire nawa idanun daga nasa da na fahimci kallon nazari yakemin
Juraid bai kasance mutum mai san ƙure mutum ba hakan yasa ya ce
"Shikenan yanzu dai ya mai jikin?"A hankali na furta"Alhamdulillah ta na samun afuwa"
"Alhamdulillah naji daɗin hakan insha Allah zamu dawo anjima dubata"
Jin maganar da yayi ta ƙarshe ya sani saurin kallonsa,Shima kallon nawa ya keyi yayi Murmushi ya ɗagamin kai
"Eh zamu zo duba ta ko ba kyason mu sami lada"
Kai na girgiza na maida kaina ƙasa ina cewa"A'a inaso amma gani nayi kamar hidimomin da kakeyi damu suna yin yawa"Na ƙarasa maganar ina ɗago kaina idanunmu ya sake haɗuwa kallon da naga yana yimin ya sani hanzarin sauke idanuna ƙasa magana naji ya fara a hankali
"Karki damu komai na miki kin cancanta ne,tunda inada halin yi miki zan yi miki da iya ƙarfina"
Murmushi nayi kawai haka muka cigaba da firarmu har zuwa sanda aka kira sallahr isha'i ya faɗama zaije masallaci ya dawo daganan zasu shigo gidan ciki nakoma na shiga ɗakin Mama na sanar da ita Abbah da yake ɗakin faɗa ya fara jin na ce Juraid zai shigo duba jikin Mama
"Sumayyah gaba ɗaya bakya jin magana ko?,duk ɗawainiyar duniya sai ki ce Juraid yayi miki ita saboda baki da imani ko?,Na hanaki kinƙi hanuwa kina jin labaran da ake samu ga irin wannan samarin masu hidima ga ƴammata har yanzu ƙinƙi jin zancena,ki koma kice nace karya shigo"Jin ƙarshen maganar Abbah yasa na ɗago na kallesa sai dai na kasa furta komai dan nasan babu wani laifi da yayi a cikin maganarsa
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.