22
A washe garin ranar dana dawo Aunty Asma'u ta dawo daga Katsina da zallar abunda yafaru dani acan ta dawo qarya da gaskiya,haka suka tattara maza da mata a gidan suna maida yadda akayi Abbah ne da yaji Hajiya ta fara zaginshi akan zancen har tana cewa bai bamu tarbiyya ba mu tattara mu bar mata gida baza ta iya ba kar a 'debo mata abun fa'da a gari ashe shine sakamakon komawa kanon da Abbah yayi saboda mu zamar masa jari yanaso yaji da'din mu zama 'yan iska har yaran 'ya'yan masu ku'di suna sona inba da lalata ba dame zasu so ni ina 'yar matsiyata tana sake jaddada zasu ga qaryar Hamid Fatima zasu ha'dashi da ita suga ko gaskiya yakeyi zancen ni dama munsa ba lalata a Kano bincikeshi zasuyi inko suka samu bahaka bane Kuma yaqin amincewa da Fatima to itama bada yawunta ba akan Abbah ya aura ma Hamid ni saboda ban cancanci aure a zuriyya irintasu Hamid ba,su Aunty Asma'u da Abbah Jafar qanin Abbah bane shima sai Abbah Imran suke sake zuga Hajiya suka rufarwa Abbah da cin mutuncin su Aunty Luba kuwa su tunzurawa sukeyi da sake cin mutuncin Mamanmu suna fa'din sun yafeshi ga Hauwa'u,ina tsakar gidan ina share bangaren Hajiya nake jiyo zancen nasu har nagama basu gama ba, shiko Abbah sun hanashi tasowa dama nayi tunanin haka zata faru ko fiye da hakan maganar wayar da banji anyi ba tunanina ya bani ko basu san zancen ba inako Shirin barin wajen naji Aunty Asma'u na cewa"Ai iskancin Sumayya harda tsohon saurayina qanin wannan matsiyaciyar matar ta Yaya Hashim, matsiyata ne fa ba suda komai indai ba lalata sukeyi da Sumayya ba,ina xai kwashi maquda ku'di ya siya mata waya iPhone kunsan tulin ku'din da ake siyan wayar kuwa"
Hajiya naji tana qoqarin rushewa da kuka"Abdullahi yanzu mazinaciya kake qoqarin maida 'yar ka ta tabbatar shine dalilin turata Katsinan kenan,Hashim kuma yayimin waya namanta ma yace ko ku fito masa da 'dansa ko ya maka ku qotu"
Abba murya rau rau naji yana cewa"Hajiya Dan Allah ku daina jifan 'yata da kalma Mai muni kalmar zina,duk talaucinmu da halin da muke ciki da rashin taimakonku insha Allah bazan haifi mazinaciya ba,koni nasa ta ta yi zina dakaina ni uba,danasan abinda Hashim zai sakamin dashi kenan da ban amince Samir ya daukarmin 'yata ba,sun tozartata a qarshe ya Mata dukan da koni uba ban ta'ba yimata ba,Kuma yana jifana na boye masa 'da,ina kiranshi yazo yayi min duk abunda yaga zai iya yi,kuma Ni ban ta'ba ma 'yata sha'awar aure nan kusa ba bare ma mai ku'di"
Abba Imran naji muryarshi yana kuma tafa hannu"dama Abdullahi ina zakayi sha'awar aurar da Sumayya kana qoqarin maidata karuwa tana kawoma ku'di,wallahi Hajiya fitinar da ke damun al'umma kenan yara 'yan 17,18 zuwa sama sun zama karuwai qarfi da yaji saboda sun ha'du da uba mai matattar zuciya,kuma mata da maza yaran manyan ke wannan shai'dancin dasu wayasan mai Mahmud 'din yayi da ita ya bata wannan wayar"
Hajiya tasake rushewa da kuka"Abdullahi ka cuceni kuwa ashe da mazinaciya nake zaune a cikin gida,shegiya munafukar yarinya kalar uwarta,tunda na haifeka abun goma bazan ce wannan 'dana Abdullahi ya bani ba,wallahi bazan iya zama da ku ba inko na zauna daku tsinke na daina daukewa saidai mazinaciyar 'yar ka tayi shi"
Abbah a fusace naji ya fara magana"Hajiya ki dakata iya nan da izinin ubangiji ban haifi mazinaciya ba kaf 'ya'yan dana Haifa da zuriyyar su Kuma ba Wanda cikinku nake bi da baqin baki,Kuma rashin taimakon da kuka kasa yimin , aiki kuka kasa samarmin bai hana Ina kyakkyawar rayuwa ba Mai tsafta zama cikin ku Kuma na barshi kenan,ke uwata ce amma kan talauci na gaji da munanan kalman da kike jifana dashi da matata harda 'ya'ya ma yanzu,kuma ni Hauwa'u ko wacce 'ya zata haifarmin wallahi ta fiyemin harke a gurina na gaji da cin mutuncin da kukeyi min,bani na halicci kaina ba,kuma 'ya'ya na wallahi sun fiyemin kaf 'ya'yan ku daga yau Zan iya cewa babuni babu ku gida kuma ku Bari mai gidan yazo ya koreni da kanshi bazan rasa inda zan tsugunna ba da talaucin nawa, za'a kar'be ni"
Kofar 'dakin na je na tsaya ina zubar da hawaye inajin yadda Abbah ke fa'da a fusace ban ta'ba jin haka daga Abbah ba yana juriyar abunda ke faruwa kai kace bai San wani abu ba'cin rai bare yadda akeyi ba
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.