24...Haka muka gama kwashe kayanmu da ba yawa garesu b dama muka qarasa lodasu a akori kura dukkanmu ba wanda yanayinsa yake cikin dad'i muka bar gidan kafin su fito ma su sake 'bata mana rai a qasa muka tafi ha'de da Abbah Musa da shine yasan gidan,ba laifi tafiya ce mai 'dan nisa ba ma 'da ba mai nisa ce ma ba sababbin unguwanni bane ba,gidane ginin qasa Abbah Musa ya nuna mana shi da muke qoqarin qarasowa,ba shida ko filasta ma amma Alhamdulillah yafi mana gidansu Abbah da suka cire soyayyar iyaye da 'dansu suka wulaqanta shi kanshi Abbah ma bare mu da mama a qofar gidan muka toge muka jira Abbah Musa ya bude kofar da a zauren muka isar da kayanmu harma an kawo su gidan sun juye da Abbah Musa ya basu 'daya daga cikin key din gidan gaba ɗaya muka shiga cikin gidan da cikin azama muka fara kinkimar kayan zuwa cikin gidan mai da'kuna uku da banɗaki sai kitchen na langa langa da alama muguwar zuba yake yi kitchen 'din amma gaba ɗaya muna farin ciki da samun canjin da Abbah ya kasa ɓoyewa ya dubi Abbah Musa"Musa bansan da wanne ido ko kalmomin da zan dubeka ko na furta ma ba nagode sosai ka taimakeni lokacin da nake jin a yadda matsalar ta tasomin nafi kowa buqatar taimakon"
Abbah Musa ya girgiza kai"Haba Abdullahi ai yiwa kaine duk wanda zai taimaki wani to yasa a ranshi kanshi ya yiwa ba wani ba,kamar wanda yaƙi taimakon kanshi ya yiwa,ladan bai isheni ba ai da zan gaza yi ma taimako dan ko da ƙarfin jikina zanyi ma ,muma a harkar karatu ka taimakemu ai kayi karatu amma ka bari muyi exam tare da saboda mu karatun baima dame mu ba ,sai gashi mun rigaka cin moriyarshi,Abbah Musa ya fa'da murya raunane da alamun rayuwar tamu ta dameshi da muke ciki" ni da nayi tsaye kusa da su hawaye naji suna zubomin cikin rashin shiri
Abbah ya dafa shi"Haba Musa karka damu dan Allah samunku ai nawane ba gashi ba ka fahimceni ka dubemu abin da a cikin gidan mu hatta da iyayena sun kasa wannan fahimtar,ni haka rayuwar ta namun da'di ina fahimtar abubuwan da a cikin yalwar arziƙi ne yayi ka'dan na fahimta"
"Allah ya mana suttura Abdullahi wucewa zanyi akwai rijiya a makwabta nan gida jikin nan 'din kusa su samo muku ba matsala batun ruwa sai dai ko su yaran suqi zuwa danni sai na siya sanda muka zauna yarane masu qyuya Allah ya bani"cewar Abbah Musa yana koƙarin ficewa
Abbah ya ce"sunga kana samunka ne niko karsu ɗebo ma su ga ni"
Abbah Musa ya tsaya da fara tafiya "na shafa'a ba muyi sallama da Hauwa'u ba,nasan sai tama ciwan baki kasan mata"
Abbah yayi dariya kawai ya kira Mama ta fito t sake ma Abbah Musa godiya sukayi sallama ya qarasa fita Abbah n biye da shi zuwa rakiya waje
Sai sannan na shiga ɗakunan ina leƙawa da babu isassun siminti a ƙasa duk ya cire tabarmi muka shishshifiɗa da ba manya bane dandanan muka shiga ayyukan gidan da share share muka yi muka gama su Rumaisa suka shiga ɗebo ruwa nima har dani ba laifi daga shigarmu gidan matan gidan suna da kirki gidan kuma mai kyau ne babu laifi ba kamar wanda muke ciki ba akwai yarinya kusan sa'ata a gidan Malika da shiga ta muka fara fira ta nada kirki kamar iyayenta dana ga alamar hakan haka muka dinga kinkimo ruwan saina zauna ma nice nake jawowa suna kaiwa gidan Malika dake wanke wanke a gefen rijiyar tana ɗan san muyi fira na dai ɗan sake da ita muna firar makarantah,ita ma mate 'daya muke bata samun qualyfying ba amma shirin biya mata akeyi ma kuma tana tunanin ɗora karatu ma ,naji ina ma nice ita haka na taya ta murna tana tanbayata wanne course ya kamata idan tazo jamb tasa ka nayi dariya na aje gugar dana gama jan ruwan
"Wallahi bansani ba duka fa tare za muyi candy ai sai dai ki tanbayi yayunki da suka ta'ba jamb ɗin,suka samu wucewa University ai"Tayi dariya"ok na tuna fa hakane,zan tanbaya zumuɗi ne fa kawai kinsan ba'a tashi farawar ba ma"
Na jinjina kai "Nace hakane kuma,Allah ya taimakemu,bari na tafi,mungode"
Malika ta ce"Amin tom sai na shigo ko anjima ne,na qarasa aiki,kina kitso ne?"
Nayi murmushi"A'a banayi Mamarmu dai tanayi,inkinaso zan mata magana saikizo ta miki"na lura dai Malika surutu gareta har ya wuce nawa da da ma banwai cika surutu ba
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.