12

50 7 0
                                    


12
Bayan wasu kwanaki ko nace satuka,da zuwa lokacin sai nace har na fara sabawa da halin mutanan cikin gidan Yaya Samir kam mutumin kirki ne shi ne abokin fira na idan yana falon idan bayanan zaman idan na ji zan takura sai na shige kitchen wajen Mai yi musu girki Baba Indo da tun farkon zuwa na take min wasa da dariya tana tsokanata da babbar jikarta kamata take take shaidamin,da matsalolin rayuwa yasa take aikin a gidan amma ba wai zaman na mata da da'di ba takan fa'da min su mutane ne kusan da baka ta'ba iya musu basu tausayin ta,su dai ta musu dai dai sukeso,abune kuma da bazai yiyu ba,kai kanka baka cika goma ba bare kace za'ayi ma dai dai 'dari bisa 'dari takan bani baki da lallashina idan suka 'bata min rai

Ina zaune falon dukda na takura hanyar ficewa na kesonyi amma kallo kallo ya riqeni,falon yayi shiru sai qarar Tv da hira qasa qasa na wasu daga cikin mutanan falon,wanda ni dai da ido nake bin Tv ina Kuma jin da'din kallon da muke na film d'in waris

"Yaya Abdulmalik kasan mene?"
Naji Fatima na fa'din hakan

"Yaya Abdulmalik ya bata amsa da
" sai kin fa'da"
Ta cigaba da cewa
"Kasan me Yaya da zaiyi wai makarantarmu sai saka,wannan Sumayyah ,ka jifa"

Tsaki yayi jin maganarta ya Kuma kalli gefena da na nuna masa kamar bansan suna yi ba
"Maine to shafuwarki da hakan Fatima ki raba kanki dai kinsan halin Yaya Samir baya san irin gulmar nan,tunda ki kaga har Abba bai isa da shi ba sai da ya kawota ke to Ina ruwanki"
Yaya Abdulmalik ne yake ta sababi dukda muryar ba da qarfi yake ba amma zaka gane sababi yake
Fatima ta ce
"Wallahi kawai dan yana nuna yafi qarfin Abba ne shiyasa ya kyalesa,yarinyar da suke talakawa ina suka cancanta da zama damu,kaima kanka shaida ne Abba yace duk wanda ya zauna da su tsiya cewa zaiyi,kuma duk mamarsu ce gashi nan Abba Abdallah ko almajiri dake garari ya fisa kyan gani akanme zama da muguwar mace mai qashin tsiya..
Dukda Ummi na zaune bai hana Fatima yin shiru daga cin zarafina ba,ko Kuma ace ta kwa'beta hawaye naji sun soma biyo kuncina da duminsu ya tabbatarmin da sune,gaskiya na yarda talaka yana ganin garari 'yar uwata da nake tunanin zata fi kowa sanin ciwona ita ce take fa'din hakan a kaina,bama akaina ba a gaban ido nama,lallai tabbas akwai wata qaddara a zamana zuciyata tuqiqi take amma banaji zan iya hassala komai,ban iya fa'da ba ko cacar baki hasalima rayuwata ni guda nake sai ko su Halima da rayuwarmu tazo data idan nasan ka fini bana shiga rayuwarka gudun irin hakan
Muryar abid naji kamar daga sama yana cewa
"Haba Yaya Fatima ki bari mana kinga kuka take,Allah sarki ita bata da laifi dama mu duka zamu zama kamarta"
Fatima ce ta ce
" Allah ya kyauta yaro qashin tsiya tayi gado fa"
Abid yayi tsaki ya ce
"Kece kika sanshi amma ni dai nasan Yaya Sumayyah ta cancanta da zama da kowa kuma ta fiki kirki,ita bata neman rigima"
Fatima ta miqe ta hayyako tayi kan Abid zata bigesa
Shigowar Abba ya dakatar da ita ya daka mata tsawa hakan yasa ta koma ta zauna tana turo baki sannu da zuwan da ake masa bai amsa ba ya dubi Ummi
"Yanzu kina zaune zasu yi mana fa'da ba zaki hanasu ba ko Sa'adatu?"
Ummi ta kallesa ta re da cewa
"Ai kasan halin Fatima baki yasa mata tana magana ka kosan ba zata kyalesa ba,laifinsa ne"
Abba ya kalli Abid
"Kai maiyasa kasa mata baki bana hanaku haka ba idan babba yana magana ba'asa baki"
Shiru yayi Abid 'din can ya ce
"Abba Yaya Sumayyah Yaya Fatima ke ta nema da rigima Kuma kowa yayi shiru ya kyaleta,shine nayi magana,ni dai nasan ba mu da banbanci da Yaya Sumayyah ko Abba"

Abban tsaki yayi ba tare da yace komai ba yayi gaba kila ko maganata baya so ayi masa ko?,bare yaji ba'asi maiya ha'da abun,jikina ba kwari na bar musu falon ba tare da na kallesu ba da alkawarin ban qara zama a falon gaba 'daya har na bar gidan,ina tafiya na fara jiyo maganar Ummi
"Fatima abinda kikai gaskiya bai dace ba,karki cigaba da biyewa Abbanku zai kaiku ya baro ku,ni dai na fa'damiki cin zarafi bai da wani alfanu"
Daga nan ban sake jiyo maganarsu ba na kuma fasa shiga daki nayi hanyar kitchen

Baba Indo na samu da sallama baki na na qarasa inda take
Kallona tayi bayan amsa sallamarta tare Kuma da ajiye abinda take ta matso kusa da ni
"Sumayyah nasan kina cikin damuwa ko?"
Hawayen da suka ciko idona suka fara zubowa na goge na kalli Baba Indo ba tare da tace min nabar zubar da hawaye ba na soma magana domin dai iya shaquwa na shaqu da Baba mukan tattauna al'amura da dama na dangane da gidan harma ta bani shawarwari matar bata da surutu da yawan magana dattijuwa ce mai sanin yakamata hakan yasa tare muke hira a gidan Kamar muna da alaqa da ita

"Baba babu mai sona anan nazo gurin da ban cancanta da zama ba gurin da arziqi shine qimarka Yaya Samir ka'dai ke sona a bayan shi sai Kuma ke dukda duk kulawata bata cancanta da ku ba amma wanda yafi kusa dani bai riqeni matsayin 'diya ba Baba banason cigaba da zama anan,na fiso naje inda na cancanta da zama na zauna da su cikin so da qauna"daganan na rushe da kuka

Baba ta dafani"Sumayyah ba zan hanaki kuka ba danni ma na fara jiyo hayaniyar fatima,banyi tsammanin Kuma hakanba na 'dauka komai wani abu da kake ji da shi ba zaka yiwa 'dan uwanka ba,Amma abin takaicin kowa yana jinta aka goyamata baya kuma,Amma ki sani baki cancanta da hakan ba kuma Allah zai miki sakayya ke 'din yarinyar kirki ce mai qoqarin aikata abu mai kyau,na da'de ina kallo da nazarin 'yam mata kamarki kamarki amma ban sami 'diya mai hankali nutsatsiya ba a bayan ke,kinga ko kece kika cancanta da kowa ya soki ma"

Shiru nayi na kalli Baba tare da murmushi Mai ciwo jin ta kawo qarshen zancenta na ce.
"Baba kenan haka mutane da dama suka sha fa'di a gareni amma har yau ban fahimci komai akai ba na kasa fahimtar ta ina Na cancanta,Baba rayuwa ta abar tausayi ce tunda ga yarinya har zuwa girma na sai kin zubda hawaye a lokacin da kikaga Abbana ki kaga Abban Katsina kowa yaqi Abbana yaqi tallafa masa saboda Ummanmu sunce ko sun basa wani abun to a haka zai qare ba zai arziqi ba sai dai idan sun rabu da Ummanmu,hakan yasa kowa ya barsa cikin qunci,bayan soma girmanmu mun 'dauka qiyayyar da sukewa Umma a iya ita ka'dai zata qare ashe ta shafemu muma kanmu,mun zama kamar abin qyama a cikin danginmu,kowa hantararmu yake,na rasa yaushe komai zai wuce"

Baba ta girgiza kanta ta ce
"Karki sare karki gaggawa komai zai wuce ya zama tarihi kuma zaku zamo abin alfahari fiye da duk wanda zai tunani zaku zama wasu abun insha Allah sai danginku sun fahimci ummanku mai qashin arziqi ce bana tsiya ba,kuma ma ki cire wa kanki tunanin akwai wani Mai qashin tsiya kowa dai akwai iya arziqinsa a rayuwa Kuma kowa zai tadda abunsa,komai daran da 'dewa"

Kai nake jinjinawa ina jin da'din kalaman da Baba ke anfani dasu gurin lallashina.

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now