30

37 6 0
                                    

Bayan wasu kwanaki a yanzu al'amuran sun soma sauƙi zan iya cewa dan mun fara sana'ar awara da safe da har gida ake zuwa siya ana gama soyawa a siyo wake a jiƙa na yin yamma kenan,bawai dan riba mukeyi ba dan muke cinye ribar dan cinikin Abbah na attaruhun ba wani azo a gani bane ba bare ayi maganar riba a tsakanin Abbah da Mama bansan waye yafi rama ba ga Mama na shayarwa al'amuran dai suna tafiya da godiyar Allah kawai,Yaya Samir a yanzu ko wayarshi bana ɗagawa kwana biyu dan wayarma bana wani yawan kunnata saboda caji,babu yadda na iya da takurar Malika takemin na amince da soyayyar Juraid tun a washe garin ranar ba laifi yana zuwa wajena kuma duk yazo zai bani ɗan wani abu wannan ya ƙara sa Jurayd matsayi a zuciya ta saboda inada buƙatar tallafin ko da da Naira Ashirin ce duba da ni a matsayina na budurwa,sai dai wasu sunfi ganin rashin cancanta ta da hakan,baya ga wannan Juraid mutumin kirki ne matuƙa fiye da yadda nayi tsammani,bara kuwa duk ranar da babu ita ƙannena ke zuwa nice dai ban taɓa zuwa ba,aikin da Ahmad ke yi wa Hajiyar da yasamu yana samo abinci har ya rage mana,wanke wanke da shara da ƴan aikace aikace yake mata shima sai da yamma saboda makaranta sai weekend yana zuwa da safe ba kuma a wata tana ɗan bashi wani abu ina yabawa halayyar matar dan jinake ina ma nice nake aikinnan ganinake zanfi Ahmad samu

A tsaye nake ƙofar gidanmu da yammaci nida Juraid dawowarmu islamiyya kenan ya tsaida ni kallona yakeyi kamar ba zai bari ba hakan yasa na yi ƙasa da kaina dariya kaɗan yayi kafin ya ce"Sumy ƴammatana kinyi kyau"murmushi nayi masa na ce"kyau kuma fa Jurayd daga fa islamiyya na dawo fa ba komai fuskata,bari dai na shiga ma kar Mama tayi min faɗa"kallona ya sake  yi"ok namanta zaki fito da awara ko,zan jira ki ni yau zan tayaki suyar awarar ma"murmushi kawai nayi masa na ce"toh Allah ya kaimu lfy" daganan na shige gida da sallama Mama dake zaune saman tabarmah a tsakar gidan tana yanka awara ta amsa sallamar tawa ta ɗaura da cewa"ai nayi tunanin bazai kyaleki haka kiƙarasa kawo lada gida ba"murmushi na saki dan batun Jurayd takemin da nake jin daɗin ayimin zancensa yadda yakamata ɗakinmu nake ƙoƙarin wucewa ina tafiya ina cewa "Haba Mama bahaka bane,yanzu dai bari na ajiye jakata na sauya hijabi nazo na fita suyar awarar kar Malika ta rigani tayimin gori"mama ta ce"badai kin tsaya soyayya ba ke" murmushi nayi kawai na ƙara sa shiga ɗakinmu abinda nayi niyyar yi na aiwatar na fito dana tarar ƙannena sun fidda komai sai ni ya rage na fita awarar ma Rumaisa naji Mama ta kira tazo ta ɗauka yadda mu kayi da Jurayd ina fita na sameshi akan Lifan ɗinsa yana zaune,kusa da inda nake zama,murmushi na saki ganinshi dan ko inasan Jurayd abin ba acewa komai yana da abinda za'asoshi danshi ɗin kirki ga natsuwa da wayewar rayuwa ina zama Malika itama ta ƙara so da itama yau anyi sa'ar ta,ta fito da wuri dan ko fitowata har na tarar an haɗa wuta,kallonta nayi nace"yau basa ban ba"hararata tayi"zan dungureki Allah saboda munfi to tare kike maganar ke banda ma taimakon ƙannan naki basai kinkai magrib ba ki fito ba,kin yi saurayi mai naci ai Abbah inajin saiya fara rakashi da bulala"sai da ta kai ayarta Jurayd yayi gyaran murya daganan yace "bama za'a kai ga haka ba ai aurenmu zamuyi"Malika kai ta ɗago "Au wai dama kana nan dama gaba ɗaya hankalina baikai gare ka ba"murmushi yayi yace"ai dama naga alamar hakan"Ni ko dariya na yi ma Malika hararata tayi tace"Malama ni kikewa dariya ko?"na murmusa na ce"yi hakuri ƙawata"dukkanmu kasko muka ɗaura a tare dan nima wutar da Rumaisa ta haɗo na fifita ta kama sosai muna cigaba da firarmu da yau harda Juraid dan yace sai fa mungama zai tafi kiran sallahr magriba ya tayar dashi yace mana bari yaje ya dawo sannan muma ƴan siyan awara da dankali sun fara zuwa an aje firar

Sallamar Jurayd tasa na ɗago kaina na dubeshi muka amsa masa,saman machine ɗinsa ya sake hayewa da har lokacin idona na kansa na ce"ai banyi tunanin zaka dawo yanzu ba?,ɗauka ta zaka koma ta gida ku dawo da Alhassan?"ya ce "A'a zai nemeni ma bare ma yasan inanan ɗin,yawwa ina hanya na tuno da maganar makarantar da kika cemin zaki koma naji shiru?"shiru na ɗan yi kafin cikin raunin murya na ce"ai ba muyi maganar da Abbah ba sai gaba kaɗan"Malika ta kalleni ta ce"gaba kuma wacce gaban kuma gashinan mu muna shirin fara Wa'ec ma kina maganar gaba Allah ya taimaki mashiririciya"harararta nayi nace"to dake ake magana ne wai?"ta ce"Allah ya baki haƙuri" maganar da nayi niyyar sake faɗa mata Jurayd ya riga ni yin magana"Please ki daure ki masa maganar ni in abun zai zama shiririta zan kaiki da kaina bakisan yadda na ƙosa ki koma ba,ina son bada jimawa ba na turo iyayena gidanku nasan zaki ce kuma saikin gama karatu zaki yi aure?"tunda ya fara maganar gaba na yake faɗuwa har ya gama tunani na shiga yi ta ina abun zai fara ne,me zai faru a Mu'amalarmu da Jurayd nan gaba,girgiza min kafaɗa da naji anyi ya sani firgigit na dawo hayyacina a firgice nakai kallona ga Malika da itan ta girgiza ni a hankali naji ta furtamin"lafiyarki kuwa Sumayyah?,tunanin me haka kike ƙoƙarin shiga?,Jurayd yana ta magana" a hankali na ɗago na kalleshi nima ya kalleni banyi tunanin har ya sake wata maganar ba bayan wadda yayi na tsinci kaina a tunanin"kodai auren ne bakyaso?,ko nine bakya so ne Sumayyah?,ko kinada wani muradin ne daban daban sanshi ba?"Jurayd da yanayin damuwa yake jeromin wannan tanbayoyin,ƙasa na sake yi da kaina ina juya awara da nayi sa'ar bata soye ba"tanbayar ki fa nakeyi?"na sake jiyo amon muryarshi har kaina naji maganar saboda yadda yanayin nawa ya juye a wannan lokacin saboda gudun kar ya fahimta wani abun bayan wanda yake kokarin fahimta na furta"babu komai karatuna nake tunowa gashi ƙawayena har zasu yi graduation"ina yanka zancen da dagaji ba alamun gaskiya ni dai a zuciya ta banji maganar ta yi daidai ba,kallonsa na ɗago nayi har da murmushinsa na alamun ya yarda naji sa yana cewa"Ai babu komai Sumayya haka ubangiji ya tsara,zan baki kuɗi ki yanko uniform ma,idan kunyi maganar da Abbah saboda nasan ba shida kuɗi a wannan yanayin dai,nasan ƙila abun ya sake shiriricewa ma idan ban shiga maganar ba"ɗaya daga cikin abunda ke ƙaramin son Jurayd kenan mutum ne mai fahimta yasan halin da muke ciki a gidanmu dukda ba zancen na taɓa masa ba, mu'amalarmu da ƴan uwan Abbah bana ji ya sani ko ya fahimci wani abun yana ƙoƙarin yimin abunda baifi ƙarfinsa ba a duka abunda bai yi wata ɗaya da fara soyayyarmu ba idan nace bazan amsa ba sai yace ai a matsayin ƙanwarshi ya ɗaukeni shiyasa ya bani ɗin,Abbah badan ranshi naso yake yarda da kyautar ba sai dan bashi da shi ne yana yawan faɗa mana ni da Mama shi tsoron kyautar namiji wajen ɗiya mace yakeyi wasu ba dan Allah sukeyi ba duba da yadda zamani ya canza haka firarmu ta kasance da Jurayd da jefe jefi Malika kan saka baki ko Jurayd ya ambaceta a firar tamu,har lokacin sallar isha'i tayi ya miƙe ya je ya dawo ya na dawowa bai jima da zama ba Alhassan da Yaya Nasir yayan Malika suka zo wajen da muma lokacin gaf muke da ƙara sa suyar dan anayin isha'i muke tashi dan ko muna samun ciniki sosai muka ɗai ne a layinmu muke awarar saɓanin wasu unguwannin ko wasu layukan Yaya Nasir ne ya siya musu sauran awarar da dankalin Jurayd da ya kasa tafiya ah lallai sai na haɗa kaya na tafi gida ina miƙawa yaya Nasir awarar Jurayd yace "Malam Nasir kufa ragemin tawa" tsaki yaya Nasir yaja"toh yayanmu ko ɓalli bata raguwa soyayyah ta ƙosar da kai" Alhassan ya ce"dan Allah Nasir kyaleshi kai ka kula ɗan rainin wayau shi lallai Romeo ai, baka ga neman da na masa ba a yau ɗin nan ashe yananan lafe"ganin zasu tafi su cinye awararsu yasa Juraid miƙewa da ga kan machine ɗin sa ya buga shi ya tayar yana furta "zakuga iskanci ni a machine ma zan buga na tafi inda zaku je cin awarar"tsaki Alhassan yayi ya na cewa"saifa munyi niyya zamuje inda kake tunanin,da dai ka zauna kasha soyayyahr kasha ruwa ka tashi kwanciya dan yau tuwo akeyi a gidan"da haka suka tutse su uku a lifan ɗin suka bar wajen Malika ta waigo ta kalleni tana dariya tace"saurayin wata yarone sai gaɓunta ya iya"harararta nayi nace"naji ai nafi mai ƙarar samarin da tsoho zata aura ma ƙila a ƙarshe"ina dariya na tashi na fara haɗa kayana dan ko nasan na ƙular da Malika aiko nan ta fara masifa ni Ko dariya nake ƙunshewa har na gama haɗa kayan na ɗiba wasu na kai gida ban da Ahmad na sake fitowa ya ƙara sa kwashemin ina dariya na kalli Malika da har yanzu bata ƙara sa kwashe kayan ba"sai da safe Madam Malika,Ahmad ka tayata kwashe kayan"nayi maganar inajin wata dariyar tazo min,"zaki san dani kikeyi zan zo har gida na bawa Mama labari kina neman gogemin harda"cewar Malika da ta kwashi kaya fuu tana gama maganarta Ahmad yace"tofa Yaya mai kika ma sahibar taki" tsaki nayi nace"bari kawai Ahmad Juraid ta cewa yaro shine daga namata batun tsoho ƙila zata aura shine fa taji haushi na take ta masifa kasan dai Malika"dariya Ahmad yayi yace"kunfi kusa bari naje nakai mata kayan kar tayimin masifar nima"banjira dawowar Ahmad daga kai kayan ba na shige gida.

Shigowar Abbah da naji sallamarsa yasani miƙewa na bi bayanshi dan kar na sake mantawa da maganar makarantar da muka gama da Jurayd dan nasan Mama tausayin Abbah zataji shiyasa ta kasa maganar ƙofar ɗakin Mama da na hango hasken fitila da nasan Abbah na ciki anan na tsaya na gabatar da Sallamata Abbahne naji ya amsa min hakan yasa na shiga sannu da zuwa nayi masa ya amsa min shiru nayi ba tare dana furta komai ba
"Kin shigo kinyi shiru ?ko Mamanku kike nema?, ai tana kitchen"Abbah yayi maganar yana sake kallona kai na girgiza na ce"A'a Abbah dama maganar makarantar zanyima naji ance ana komawa SS2"nayi maganar da ina ƙasa da kaina saboda kunyar da naji ta zomin dan ganin kamar ina ƙoƙarin matsanta masa duba da yanayin da muke ciki bansan da ya zai ƙarɓi zancen ba, muryar Abba naji yana cewa"kiramin mamarku"miƙewa nayi daga tsugunnen danake kusa da Abbahn na fito daga ɗakin na shige kitchen Mama na kira har zan fito ta kalleni "kiran me kikaji Abbahn naku na yimin" na furta "wallahi  bansani ba,nadai yimasa maganar makaranta ɗazu Jurayd ya sakemin maganar yace ma zai yimin uniform ɗin ma"kallon tuhuma Mama tayi min kafin ta ce"roƙonsa kikayi kenan?,kinsan Abbanku bayasan wannan ɗawainiyar da yaronnan ya fara yimiki ,so kike ya riƙa ganin laifina ko Sumayya?"kai na girgiza  nace wallahi Mama ba haka bane ba ban taɓa roƙon Jurayd ba yace gani yayi lokaci naja"miƙewa mama tayi ba tare da ta kulani ba saida zata fice naji tana cewa"ki zauna ki ƙara sa girkin inma tambayar kikayi dai keta shafa nidai baruwana"bata jira cewa ta ba ta fice abinda ake dafawar na buɗe taliya nagani da bazata wuce guda ɗaya ba a tukunya,hawaye na goge dan itace zamu ci a daren mu tarfata a hannu a hannu saima angama za'a tashi sauran ƙannena da har sungaji da jiran abinci sun haƙura sunyi barci.

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now