18.Jin qarar tsaida motar ya sa ni dawowa daga duniya tunanin rayuwata da na fa'da Yaya Samir na 'dago na kallah nima ni yake kallo a daidai lokacin,kafin na maida kallona bakin titi dan duk tunanin da na fa'da na tabbatar rabin Kano ma ba muyi ba,a daji Yaya Samir ya tsaida motar,na sake kallonshi da yanayin tsoro,saboda rashin tsaron da ke qasar a 'bangaren Katsina abun yafi tsanani,na fara magana ga Yaya Samir da tsoro qarara fuskata
"Yaya Samir naga ka tsaya daga nan,ko babu mai ne?"Kai ya girgiza min,"Ko 'daya Sumayyah natsuwarki nake so ne,Dan Allah ki daina tunani ko baki fa'da min ba nasan ki nayi bazan iya ciro zuciyarki ba da nacirota na cire miki tunanin,dan Allah Sumayyah kiya haquri da abunda ya faru Samir na tare da ke ki yafema Abbah mu masa addu'a Allah yasa ya gano gaskiya,abun nashi ba yamin da'di banda Ummi ma sai yafi haka Sumayyah inaji ne ina ma Abbah Abdullahi da Ummi Hauwa'u iyayena duk rayuwarku zan jureta hakama ina tayaku rayuwar,Sumayyah ina sanki ko badan halinki ba da Abbah Abdullahi,umminku ma kin cancanta a so ki aso zama dake a qarar da komai dan samun ki,inaji dan ko baki dauko halin iyayenki duka ba kin dauki wani bare ma nasan Sumayyah kin zarta su ma,dan Allah Sumayyah ki yarda dani,karki manta da rayuwata ki kar'bi wani komai da'dewa Sumayyah,ni ne ke,ke ce ni"
Kallonshi nayi ina hawaye,tare da rasa me zance nayi qarfin hali na ce"Dan Allah Yaya Samir ka ja motar mu tafi haka ina tsoron wani abu ya samemu anan,bansan amsar da Zan baka ba ba abinda ke min da'di ,bare har nayi tunanin gano cancanta da kake gani kai da Halima kuna ta cemin NA CANCANTA,har yau banganeta ba,Dan Allah karku qarama zuciyata ra'da'di ku barni haka,nafi yarda da maganar Abbah Hashim ne,ban da wata cancanta,inama rantsuwa da Allah mu talakawane abincin yau da gobe kullum muke nema,na yarda da Kai ne na biyoka nan na tsallake mutane mafi daraja a bayan iyayena amma ga makomata anan haba Dan Allah me zance wai....."kuka kawai na fashe da shi to me Zan ce ne wai wata jin wani zafi nake daga zuciyata zuwa kirjina
Lallashina ya fara"Haba Sumayyah dan Allah ki bar kukan ka da kisa nayi nasan komai Sumayya nasan nayi laifi dan Allah kada kisa zuciyata ta qara qunci banajin da'din abinda ya faru ina sanki Sumayyah, duk duniyar da Kika shiga zan tayaki shiga ne Sumayyah,ni ma fa Katsinan ba tamin da'di bana jin zan sake komawa katsina Sumayya Nima na barota saboda ban cika alqawarin da na daukarma Abbah Abdullahi akanki ba"
Da kallon mamaki da goge hawaye nake kallonshi"Yaya Samir ni din fa na yafema,Nima Mai laifi ce,amma karka tafi ka bar Ummi dan Allah ina zakaje Yaya Samir"
Murmushi na ga Yaya Samir yayi kawai"Ai Sumayyah zamana ba shida anfani zanje nima na samu rayuwar da zan tsaya da qafafuna saina dawo na aureki dan Allah,banajin da'di nima dama ina Shirin barin katsinan abokina ya kirani zan samu aikin da yafi nanan,Allah Sumayya banaji zan iya zama anan babu ke din,dan Allah ki bawa wancan haquri Sumayyah"
Daganan yaja motar muka cigaba da tafiya,shirun kurame ya cigaba da ratsa tsakaninmu,na rasa gane duniyar tunanin da zan fa'da duniyar batamin da'di abubuwan sun cunkushewa zuciyata, qarar taka burki ya sa na farka daga barcin da nayi a motar a lokacin na kallo agogon dake jikin motar 4:00pm dai dai ta window nake kallon mutanan da ke alwala suna shirye shiryen tafiya masallaci sai sannan na gano inda nake mun qaraso layin gidanmu muna gefen gidanmu daidai qofar gidan Alhaji Yassar Makama masallacin jikin gidansa ake ta shiga sainaga unguwar tana sauyawa a idona maganar Yaya Samir ta katseni
"Sumayyah mun qaraso fa muje na sauke miki kayan,ina sauri ne"
Kallonshi nayi ido cikin ido abinda banwai ta'ba yi ba"Yaya Samir ba zaka shiga ka gaida su Umma ba"
Kai ya girgiza"Haba Sumayyah idan na shiga me kike tunanin zan ce musu,bazan ta'ba iya ha'da ido da Ummi Hauwa'u ba,bare Abbah Abdullahi"
Wani hawayen naji yana qoqarin fitomin nayi qoqarin gogesu na bu'de murfin motar na fito da ciwan jikin dukan da Abbah Hashim yayimin sai yanzu jikina kemin tsami dana tashi,Yaya Samir kayana ya fiddomin ina gefe tsaye sai lokacin na lura da qaton jakarshi a gefen da ya ciro tawa,yaja boot din ya rufe,aljihu yasa ya fito da ku'di ya mikomin nayi kamar ba Zan amsa ba ya ha'demin rai na amsa nayi godiya ya kalleni
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.