35....
Har bayan magriba babu abinci bare magani,bare zuwan Juraid da nasan ko zaizo sai bayan isha'i Malika kuma ta aikomin Na'im cewa ba a gama tuwon ba mu kuwa dama ba mu samu yin abincin ba,Tunanin nawa yayi saurin tsayawa cik jin ƙarar wayata banyi tsammanin Juraid bane mai kiran bazan kuma iya ɗaga wayar ba sai sa'ar Khadijah dake gefena itace ta ɗaga wayar
"Assalamu alaikum bata da lafiya"Banji mai akace ba a ɗaya ɓangaren kasancewar ba a speaker aka danna wayar ba saida ta aje wayar ta faɗa min
"Yaya ,saurayinki ne yazo dubaki zai shigo"Tana faɗin hakan nagane Juraid take nufi duk da ban tsammaci zuwanshi ba amma nasan zaizo dakyar na iya ɗaga kai na kalleta da muryar rashin lafiya na iya haɗa kalmomi
"Ki..faɗa wa..Mama..shi kuma ki fita kice masa ya shigo"da "Toh"ta amsa min ta miƙe ta fice niSake jan hijabin da Malika ta rufamin nayi sosai na cigaba da rawar sanyi,mintina kaɗan na fara jiyo sallamar Juraid sama sama da inajin sallamar nasan bashi kaɗai bane ba, basu shigo ɗakin da nake kwance ba hakan ya ƙara bani tabbacin sun fara shiga ɗakin Mama gaisheta, Banji fitowar su ɗakin Mama ba sai sallamarsu da naji a ɗakinmu ban iya amsawa ba na dai ɗago kaina na gansu Khadijah itace ƴar jagorar shigowar tasu itace a gaba sai shi Juraid da Alhassan da Yaya Nasir
"Sannu da jiki Sumayyah"Dukansu suka furta hakan suna ƙoƙarin zama can gefen da nake kwancen
Kaina na sake ɗagowa na kallesu a hankali na iya furta "Yawwa"wadda ba nida yaƙinin sun jita
"Sannu amma ya kamata kisha magani ko ayimiki allura ma"cewar Alhassan da shine ya riga su zama
Ban iya ba shi amsar komai ba saboda azabar da nake sake ji
Muryar Juraid naji yana cewa da Alhassan"Ai na zoma ta da magunguna ɗazu nazo wajen Malika na tanbayeta yanayin jikinta shine na biya wajen Idris na siyo magunguna"ya ƙara sa maganar da sanyin muryarshi da yanzu ta sake yin sanyi
"To masha Allah Allah ya ƙara lafiya Sumayyah"faɗin Alhassan ɗin
Sun ɗan jima a ɗakin kafin su fita da kallo na bisu ina sake kallon yanayin Juraid da duk ya canza tashi ɗaya duk kuma nasan ciwona ya sanyashi komawa hakan babu ƙoƙonto akan soyayyar da Juraid yake gwadamin ita,gefen da suka tashi na kalla ƙatuwar leda viva ce cike da bansan mene ciki ba, Khadijah dake zaune na kallah a hankali na furta
"Khadijah ki kiramin Mama"Da saurinta ta miƙe tana furta min "Toh Yaya"
Bata jima da fita ba sai gata sun dawo da Mama ɗin Mama ce ta kalleni"Sannu Sumayyah ya jikin?,jiran Abbanku nakeyi a sama miki magani"
Kai na ɗaga na daure na furta"Yawwah Mama amma magani ma Juraid ya kawomin suna cikin kayan nan"na ƙara sa maganar ina nuna mata ledar da suka ajiye
Mama wajen ledar ta nufa tana cicciro kayan ciki Yoghurt freshyo da lemuka peach a ciki sai Maltina da madara,leda guda magunguna Mama ta ɗago ta kalleni tana riƙe baki
"Sumayyah hidimar nan ta Juraid tana yawa fa,ki duba fa ki gani?"Na ɗan yi murmushi a hankali na iya furta"Ai na gani Mama"
Mama ta jinjina kai"Allah ya tabbatar da alkhairi"
Daganan Mama ta zauna ta buɗe Yoghurt ɗin"Tashi ki karɓa kisha kafin na ɓallo maganin"
Daƙyar na iya tashi na zauna ina miƙawa Mama hannu ta bani magani miƙomin tayi na fara sha a hankaliMama da ta fara duba maganin naga ta dubi Khadijah tana cewa"Ke! Khadijah tashi ki ɗaukomin yarinyata na barta ita kaɗai a ɗaki"Mama bata gama rufe baki ba Khadijah ta fice yau ance ta ɗauko A'isha shine ganɗokin nata da Mama bata bari su ɗauketa
Mama ta ɗaura da cewa"Yaran nan daga cewa Rumaisah ta fidda awarar nan duk suka ɓuya suka bita"Nidai shiru nayi Maman ta ɓalle maganin ta bani sannan ta fice
YOU ARE READING
NA CANCANTA!
Non-Fictionlabari akan zumuntarmu a yau,bisa ga talauci an wulaqanta ta zumunci saboda abunda baka da hurumin za'bar yadda zaka rayu,amma hasashen yana bada gazawa da kasawa ya jawo hakan,bakuma hurumin taimakawa a saboda wancen tunananin.