42

35 5 0
                                    


42.....

Ina ɗago idona ya sauka kan Malika da take ta aikamin saƙon harara har ta ƙaraso inda muke zaune da sallama sannan ta gaishe dasu Gwaggo Aunty da batasan Malika ba naji tana cewa Gwaggo

"Gwaggo wacece Malika ko ɗiyar Yaya Maryam ce?"

Gwaggo ta girgiza kai"A'a wannan ƙawar Sumayya ce makwabtansu ne kuma,Amma ɗiyar Maryama ko Nasiba tafi su Sumayyah girman jiki bare Abida kamar Maryama jikinta yake da girmanta, kuma Abidah ta girmi Sumayyah da a ƙallah shekara uku ma ƙanwarta kuma Nasiba ma ta girmi Sumayyah,duk suna makaranta da tuni kin gansu sunzo"

Aunty tayi murmushi "Alhamdulillah ai karatun na da anfani indai da halin yi ɗin tunda zaman ma ba auran bane sai Allah ya kawo,Allah ya taimaka ya basu sa'a ya kawo miji nagari"

Gwaggo tace"Uhmm ke dai  Rumaisah to Amin dai amma ƙoƙartawa kawai akeyi dai haka nan,gashi a haka har Abida ta  kusa gamawa,sai bautar ƙasa ita kuma ƙanwarta Nusiba tana Shekara ta biyu ne da shiga itace ta ba Sumayya kusan shekara"

Aunty ta ce "To ya za'ayi Gwaggo haka za'a cigaba da ƙoƙartawa , Allah ya ƙara horewa ai ilmi makarine indai dashi ko ya yake zakiga banbanci da wanda baiyi ba a dai wannan zamanin da muke ciki bare su kuma ai zaki ƙara ganin rayuwarsu ta ƙara canzawa da abubuwa masu kyau insha Allah addu'ar ku dai itace makaminsu a ko ina"

Ni ko da hankalina naga hirarsu Aunty da Gwaggo da har nama manta da zuwan wata Malika ma dukan da naji a cinyata ya sani maido da hankali na zuwa ga inda aka dokeni Malika ce da take zaune kusa dani da bansan ma ta kai ga zama ba

Cikin haɗe fuska na juyo gaba ɗaya ina kallan Malika itama haɗe fuskar tayi ta kuma ƙimin magana nice na katse shirunmu

"Haba Malika me nayi miki?"Dukda nasan laifin nawa amma inason sake jin ba'asi

Hararata Malika tayi "Bansa ni ba Sumayyah,tsabar wulaqanci nazo gaishe da mamarku ki juyamin baya ma nice ma nazo ai tunda baki iya faɗa min ba"

Ganin nayi laifi inji Hausawa sunce gaishe da mai gaisheka ko ba zai amsaba hakan yasa na sassauta da murya na ce"Haba mana ƙawata shine to na dukan hankalina yana wajen maganar su Aunty ne fa,kuma wallahi da wuri muka taho asibitin ne,waye ya miki bayanin asibitin"

"Uhmm kin gama daɗin bakinki ba buƙata kisan waye ya faɗa min ai bari na tashi saiki fi sauraron labarin da kyau"Malika tayi maganar tana miƙewa,Nima miƙewar nayi ganin ta fara tafiya yasa nima nabi bayanta

"Toh sai kizo ki gaishe da Mama tunda kinƙi yarda ki haƙura"

Kallona tayi "Rakani to wajen Mama ɗin"

Murmushi nayi"dan Allah kiya haƙuri Malika ita Mama ba a fara ganinta bama kinsan private Hospital sunce batasan hayaniya ne"

Daƙyar na lallashi Malika ta dawo ta zauna,Aunty ta dubeni
"Ya naga ɗazu ta tashi?"

Nayi murmushi na kalli Malika sannan na ce"Ai da tayi fushi ne Aunty"Murmushi Aunty tayi ba tare da tace komai ba suka cigaba da fira da Aunty Maryam

Har Yamma sosai Malika takai a asibitin sannan tace zata tafi zata yi suyar dankali,dama ta jira ko za'a bari a ga Mama amma har lokacin basu ba riba,sallama ta yiwa su Gwaggo sannan na biyota na ɗan rakata hanya muna tafe muna ɗan fira

"Juraid kuwa ya san Mama bata da lafiya?"Malika ta jefomin tanbayar a lokacin muna ƙoƙarin rabuwa

Kaina girgiza mata Sannan na ce"A'a gaskiya  ban faɗa masa ba"

"To wai maiyasa ne?,kinsan bazaiji daɗi ba idan baki faɗa masa da wuri ba"

Cikin sassauta murya na ce "zan fa faɗamasa amma kinsan me Malika banasan wannan hidimar tashi tanayin yawa gashi Abbah ma bayaso duk ya kawo saiya yimin faɗa

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now