Bismillahir rahmanir rahim❤Written by khaair
Ruwan sanyi ta shiga kwarara wa kanta tana ihu tana kiran sunan Allah, dan ita a ganinta duk abinda ta gani mafarki ne takeyi, mafarkin ma mummuna. Da taga ruwan sanyin ba amfani zaiyi ba, ta shiga watsa wa kanta mari kyawawa amma ta gaza yarda da idanuwanta. Kabir ne ya fito daga dakinshi a guje yana sanya singlet. Kiran sunanta ya fara kira
"Binafa, Binafa, meye haka ne? Kashe kanki kike so kiyi? Wani irin kuka ta fashe dashi ganin fuskar kabir.
"Wayyo ni Bintu, ya kabir ka cuceni, ya zaniyi da rayuwa? Ina zani saka kaina naji dadi? Innalillahi wa inna ilaihi raji..."
bata ida fadar abinda tayi niyya ba ta kife a sume. A gigice kabir ya saurin tarbarta ta fado jikinshi, baiko tsaya sanya kaya ba, jikinshi gajeren wando ne sai singlet, ya rarumi key din motarshi sai asibiti. Ko ina bai tsaya ba sai hanyar emergency yayi da ita a hannunshi kamar gawa. Babu bata lokaci nurses suka taho da gado aka wuce da ita wani daki. A guje wata mata akalla shekaru 40 da ita, shiga dakin da binafa take tana gyara stethescope dinda ke wuyanta. Sunfi minti talatin kafin su daidaita mata numfashinta sannan aka bata duk wata kulawa data dace.
Kabir da yake waje, ya kasa zaune ya kasa tsaye, tsoro, fargaba, suka cunkushe a zuciyarshi ya rasa takamaimai abinda yake damunshi, guri ya samu zaune ya shiga rusa kuka. A hankali aka bude kofar. Daga kanshi yayi da sauri, ganin doctor ya sashi saurin mikewa ya tarbeta.
"Dr azeema ya binafa?
"Follow me to my office" kawai ta iya cewa a takaice. Haka ya bita jalau jalau har cikin office dinta da sanyin AC kawai yake tashi. Zama tayi, shima ta mishi alamar daya zauna shima. Binta yayi da ido bayan ya zauna a takure kamar wanda yake bisa allura.
"Kabir, dama fatima batada lafia ne?"
Gabanshi ya mugun fadi
"Doctor lafiar fatima kalau batada wani ciwo, wani abun ne?"
Gyaran murya tayi tana daidaita gilashin idonta tace
"Gaskia dazun nayi cross examining dinta sosai, ciwuka kusan kala uku ne a tare da ita. Ko su baka san dasu ba?"
A wannan lokacin har kabir ya fara zufa dukda sanyin dake cikin office din. Goge zufar goshinsa yayi yace "doctor wanne ciwo ne haka, ni gaskia bansan binafa da wani ciwo ba, saidai tun tana karama take fama da neumonia wadda saida kyar aka samu ta samu lafia. To sai athma wacce har yau akwaita, kuma shi binafa ne batason magani, tafi son taita zuqar inhaler kullum, babu yanda banayi da ita wallahi, shiyasa kusan kullum tana samun attack, koda yaushe muna hanyar wajen doctor dinta. Amma banda wadan nan, bansanta da wani ciwo ba."
Ajiyar zuciya dr.azeema tayi tace
" to banda athma, neumonia dinta ya zama very chronic, she will need an x-ray a chest muga respirational system dinta yanda yake working. Athma dinta ma zamu samu magani mai karfi, dole tana shansu gaskia saboda shima yana affecting lungs dinta. To bayan wannan, fatima is suffering from heart problem.
In ba'ayi taking immediate action ba, i'm sorry to say, she might lose her life saboda its a simple heart problem, many people can survive it, amma if it turns to be big, its very dangerous." Tunda doctor ta fara magana, babu abinda kabiru yakeyi banda salati. "Ya salaam, yanzu doctor ya za'ayi kenan, wanne za'a fara treating?"" yanzu zani maka prescribing magani ka siyo su, zatana shansu har sai munga yanda hali zaiyi. Amma zamu fara x-ray din mugani mu fara treating neumonia din"
"Toh doctor, nagode sosai"
Mika masa takardar data rubuta maganin tayi, ya karba tareda mikewa, sai lokacin ya lura da kayan dake jikinshi, a kunyace ya fito. Hanyar dakin binafa yayi, amma akace bazai iya shiga ba. Lekawa yayi yana kallonta. Drip ne a jikinta, tausayinta ne ya kamashi, da sauri ya juya hawaye nabin idonshi. Hanyar motarshi yayi straight, yana ma binafa fatan samun lafia dukda yasan samun lafiyarta wani babban tashin hankali ne a rayuwarshi dama rayuwar aurensu.
Gida ya isa, yanda ya barshi haka ya iske shi, dakinshi ya leka, ganin babu mustafa, alamu ya tafi kenan. Wanka ya shiga, ya dinga dirzar jikinshi kamar kayan wanki, yanayi yana hawaye. Saida yayi sabi biyar, sannan yayi wankan tsarki. Alwala ya dauro, saida ya jero nafilfilin dashi kansa baisan yawansu ba. Sannan yayi sallarshi. Addua ya shiga yi, saida yayi mai isarsa ya tashi ya shirya cikin kananan kaya, ya fice daga gidan. Pharmacy ya fara tsayawa. ya fiddo takardar ya basu, suka bashi magani, ya biya kudin ya wuce restaurant, abinci ya siya, ya tsaya wajen mai fruits ya siya mai gudan yawa. Wuri ya samu yayi parking, number mahaifiyarsa ya latsa, bugu guda aka dauka da sallama. Suka gaisa, ya shaida mata halin da ake ciki, tareda fada mata asibitin. Tana salati da sallallami ta kashe wayar. Number baban binafa ya latso, dukda gabanshi na matsanacin faduwa, saboda yasan irin shakuwa da soyayyar dake tsakanin binafa da babanta. Daurewa yayi ya danna call, aiko bugu hudu ya dauka da murnarshi, murnar komawa ciki tayi ta koma fargaba jin abinda kabir yake shaida mishi. A gigice yake tambayar asibitin, kabir yace "federal medical centre ne Abba, maternity room 6." Bai jira wani bayani ba y katse wayar. Daman ya tashi wajen aikinsa, sallah ce zayayi ya tafi. Aikuwa sallar ya kabbara. Wata ajiyar zuciya kabir ya ajiye dukda shi kansa baisan dalilinta ba. Haka ya isa asibitin yana sake sake zuciyarsa cunkushe da tunane tunane. Office din dr azeema ya fara shiga. Ta fada mishi yanda za'asha maganin tareda fatan Allah ya bada lafia. Tambaya yayi ko zaya iya shiga wajen binafa, tace masa "eh" dakin ya nufa gabansa na matsanacin faduwa, domin ya sani sarai in har fatima ta farka to ciwonta ma karawa zaiyi inhar ta ganshi, dan yasan yanzu ya shiga layin makiyanta.
A hankali ya bude kofar dakin da yer siririyar sallama...So guys💃, how's the first chapter? What did you think? Please,
comment,
share, and
vote.
Thank you. #OneLove❤
![](https://img.wattpad.com/cover/126442930-288-k893284.jpg)
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...