Written by khaair
Jarkasa_jnr surprise!😍 this chappie is specially for you for all the support.
Sai wajen karfe uku da kwata aka gamawa fatima kwalliyarta. Masha Allah
"Epitome of beauty"
Ba mutanen ba, ita kanta fatima saida ta yaba. Dan ba karamin kyau tayi ba. Kamanninta sun cenza. Kamar wani baby doll.
Saida miemie ta dauketa hotuna iri iri. Sannan tayiwa duk wanda ya biya kudinsa kwalliya.Saida fatima tayi sallar la'asar sannan miemie ta taimaka mata ta saka gown dinta, wanda suke royal blue decorated with gold. Fatima har tsorata tayi ganin wani kyau da tayi. Bata san lokacinda tace
"MashaaAllah, this is so masha Allah"
Murmushi miemie tayi tace
"Amarya kinyi kyau sosai. Ango yau dole ya biya kudin kwalliya"
Dakin gaba daya akayi dariya. Su Asiya ne suka shigo daga dakin umma kowannensu ya shirya cikin kayan alfarma. Sunyi kyau ba kadan ba. Dukan yen matan amarya zasu saka fararen kaya. Maza kuma farin shadda. Amarya da ango ne kawai suka sanya royal blue.
Kawayenta sunata santin kwalliyarta wasu kuwa hotuna suke mata. Umma ta aiko wata mai aiki da waya wai a bawa fatima ana kira. Karba fatima tayi tasa a kunne tareda sallama.
"Wa alaiki salam nurul ayn... da fatan kin tashi lafia?"
Sautin murmushinta yaji daga bisani tace
"Lafia kalau, kaifa?"
"Lafia kalau, da fatan dai kin shirya, dan a yanzu haka ma muna wajen kofar kwaya, mun kusa mu iso. Ku shirya kinji ko?"
"Duk a shirye muke. Munyi sallah mun kimtsa, zuwanku kawai muke jira"
"Toh masha Allah, gamunan zuwa"
"Saikun iso, Allah ya tsare"
"Amin faty na"
Nan da nan kowa ya kimtsa. Miemie ta hada kayanta ta tafi. Umma sai yaba kwalliyarta takeyi.
Hudu da minti goma kiran muktar ya shigo, ya shaida musu cewar gashi sunzo.Saida yen matan amarya suka gama fita, motoci suna jerawa. Asiya ce takewa fatima korafin bata fiddo gashinta ba.
"Aa wallahi. Ni inda badan ma wannan rigar dogon hannu bane,da bbu yanda za'ayi na fita babu gyale. Gashina kuma al'aurace, bazani budewa duniya ta gani ba. Ya muktar ma bazai ji dadi ba"
Tsuka Asiya taja tace
"Kedai anyi bakauyiya wallahi"
Murmushi fatima tayi tace
"Alhamdulillah, da dai nayi wayewar da zani samu zunubi. Gwara kauyancin da banida zunubin, besides i'm not looking that bad"
"Kedai kika sani, bagidajiya"
"Naji din. Wayayyiya"
![](https://img.wattpad.com/cover/126442930-288-k893284.jpg)
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomansaFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...