💫🌼twenty seven🌼💫

3.2K 170 9
                                    

Written by khaair

Wasa-wasa fatima bata farka ba. Tunsu Abba nasa ran ta tashi har akayi azahar shiru.

Har lokacin Dr. Azeema ta shigo duba jikin fatima.

'Yen gwaje gwajenta tayi sannan ta nemi Abba zuwa office dinta. Ba wanda zai iya tsayawa baya, dan haka tare suka dunguma zuwa office dinta.

Bayan wasu sun zauna, wanda basu samu wurin zama ba sun dan raba.

Dr. Azeema tayi gyaran murya tareda saka gilashin ido ta kalli su Abba da sukayi tsuru tsuru kowa na saka abu cikin ranshi, amma duk hankalinsu yana kanta ta fara magana

"As i told you before, fatima na suffering from neumonia, chronic asthma and a hole in the heart. Her neumonia as i was told, tun tana yarinya ne. That can be prevented, her asthma also, indai tana shan magani akai akai, kuma ana mata monthly injections dinda ya kamata, zatana living freely without any fear din zata samu attack. Saidai in Allah yaso.
Amma wannan ciwon danake fada muku. Hole in the heart wanda ake kira da congential heart disease in general. Is very dangerous if chronic, in bai zama chronic bane ko magani sai yayi maganinshi.
Ciwon kala biyu ne.
Akwai wanda atrium dinta ne ya huje, ana kiransa da Atrial septal defects (ASDs) wanda yake hade oxygenated blood dinta da taceccen jinin jikinta. To extra blood will flow to the right side and can cause big damage.

Akwai shima na ventricle. Shima kusan abu daya yake causing amma shi yana hadawa harda huhu."

Shiru tayi, wanda yasa su Abba kara tsura mata ido. Taci gaba da cewa.

"Toh, irin wannan ciwon yara da yawa ansha haihuwarsu da irinshi. Baka ganewa, saboda baida wani sign ko symptom. Amma duk da haka, in sun fara girma, zakaga jikinsu yayi karami, amma sunada shekaru.
Yawanci in signs ko symptoms suka fito fili, zakaji heart murmur, shine most common. Zuciyar mutum.zata dinga wasu sounds. Wani extra unusual sound ne during heartbeat. Amma gaskia yawanci heart murmur din shine kusan symptom dinda ake ganewa.
Iyaye sai kaji sunce ai sanyi ne ya kamashi, a samar masa sassake, a jika mar yasha zayaji sauki. Daga karshe yaro ya mutu sunfi kowa kuka..bacin basa iya daukar yaro su kaishi  asibiti a dubashi.
Amma duk da hakan, bawai ko wanne heart murmur bane mutum nada congential heart disease. Yara masu lafia da yawa sunada irin wannan. Amma duk da hakan anaso a kawo yaro wajen doctor ya dubashi, in doctor yasan abinda yakeyi, daya saurara zaya gane in murmur din is harmless or sign of heart problem.
Toh inhar babban ASDs ba'a gyarashi ba aka toshe hole din, na fada muku, extra blood will flow to the right side of the heart, kuma it will damage the heart and lungs and this may lead to heart failure. And kunsan in mutum ya samu heart failure, possibility din mutuwarshi yafi yawa.
Kuma irin wannan baya faruwa gaba daya sai mutum ya girma, ma'ana ya balaga."

Shiru dr. tayi wanda ya nuna ta gama bayaninta. Sosai wannan magana ta shiga jikin wanda duk yake cikin dakin. Dan kuwa kowa cikinsa ya duri ruwa.
Mama ce kawai ta samu bude bakin magana tace

"Toh doctor, ya ake gane mutum nada wannan ciwon. Abin nufi, physical signs din"

"Eh toh ya danganta gaskia, nace muku heart murmur shine most common. Saidai signs din heart failure akwai :- fatigue (tiredness), tiring easily during physical activitiy, mafi yawanci in mutum nadan hidima, zakiga ko minti goma bayayi, sai gajia. shortness of breath, mutum yawanci sai numfashinsa yana daukewa. Buildup of blood and fluid in the lungs, kinga shi huhu matatar iska ne, wato carbondioxide, toh inhar jini da ruwa ya shiga, ai da matsala. Toh akwai kuma swelling in the ankles, feet, legs, abdomen and veins in the neck. Duk wadannan symptoms din heart failure ne"

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now