Written by khaair
Cikin bacci ta wani zabura ta saki salati tana yarfa hannu.
Aliyu dake gefenta bai kwanta ba yana aiki a laptop yayi saurin sakin aikin da yakeyi ya juyo gareta. Baisan lokacin daya kirata da ainihin sunanta ba
"Fatima lafia?"
Shine abinda ya iya tambayarta.
Girgiza masa kai tayi tareda dafe gefen cikinta tana yarfa hannu.
"Yaya muje asibiti, muje asibiti dan ALLAH"
"Zarah gani kusa dake kina kiran muje asibiti. Kuma gashi ba lokacin haihuwanki bane, you still have w months to EDD dinki ma"
Tuni fuskanta yayi sharkaf da hawaye. Rungumeta yayi a jikinsa yana bubbuga bayanta.
"Ba zaki girma bane zarah, kin cika kuka ko"
A hankali ya samu tayi shiru. Daga lallashi sai bacci barawo ya saceta.
A hankali ya kwantar da ita tareda kara mata pillow a kirjinta.
Duba lokaci yayi yaga daya saura.
Ya cigaba da aikinsa.Baiyi minti talatin ba ta kara zabura tareda dafe gefen cikin tana salati. Ajiye aikin yayi gaba daya ya hayi gadon sosai, ya tallafota a jikinsa yana tofa mata addua.
A takaice daren basu runtsa ba.
Saboda haka da asuba ko azkar bai tsaya yiba ya kwasheta zuwa asibiti.
Bayan ya sauke su junior gidan umma.Abu wasa wasa ya zama babba. Dan kuwa haihuwa ce akace ta zowa fatima.
Hankalin Aliyu ba karamin tashi yayi ba, dan haihuwar bakwaini yasan probability na rayuwar yaro is zero.Dole yasa hannu a takarda, sannan fa aka shiga da fatima wajen operation.
Shima ya shiga kiran wanda ya dace ya sanar musu fatima na asibiti za'a mata CS wai haihuwa. Daman umma da hankalinta bai kwanta ba tun kawo su junior.
7am aka shiga da fatima dakin CS din.
Sune basu fito ba sai sha biyu.
Aliyu shi ya tsufa masallacin asibiti ma dan hankalinsa ya mummunan tashi.Dangi ma duk wanda yazo sai yayi turus.
Yana shigowa cikin asibitin sukayi karo da doctor dake fitowa daga dakin.
Da sauri ya tarbeta da tambayarta
"Dr Asiya how is she?"
Murmushi ta masa tareda da cewa
"Alhamdulillah, an samu beautiful baby girl, and the mother is very okay and healthy, she will wake up anytime from 4hours now. Saidai baby din dole za'a sakata a kwalba har nan da wasu weeks"
Daga tsaye ya Aliyu ya duka har kasa yayi ma Allah godiya ta hanyar sujudu shukur.
Hawaye ke zuba ratata daga idonsa. Allah ya karba adduansa, yau ALLAH ne ya bashi 'ya mace. Saida sadiya ta tabashi sannan ya tashi tsaye.Dakin da fatima ke ciki na hutu wanda dr Aisha ta nuna masa ya shiga. Tana kwance bisa gado tana sharar bacci. Gefen gadon ya zauna, ya riko hannunta ya dora bisa bakinsa. Hawayensa kamar pampo haka suke zuba.
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomantikFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...