Written by khaair
Tun jiya ya shigo kasar, amma yana garin kano. Bai tsaya bata lokaci ba dukda dare ya tsala. Baya iya hakura sai ya zo gida. Babban burinshi yazo gida yaga fatima. Hankalinshi ba karamin tashi yayi ba jin kullum baya samun wayar gida. Fatima din da yake samu a waya itama shiru.
Motar haya ya biyo ya shigo gari. Gidansu ibrahim ne kusa da tasha, saboda haka ya wuce dutsin safe. Ibrahim sosai yayi murnar ganin abokinsa, dan kuwa sun jima basu hadu ba. Sosai ya tarbe shi. Anan gidan ya samu ya kwana. Dukda rabin ranshi yana kan gida. Dan hankalinsa a rabe yake.
***
Tun bayan asuba da Abba yayi sallah yake zaune yana sakar abinda ya kamata ayi yau.
Yau dai gashi daurin auren muktar bayan an tashi sallar jumu'a. Komai zaya faru. Zaya yarda a daura auren, yanda ko bayan muktar ya farka ya samu karfin guiwar kara jin yana son samun sauki.
Da wannan shawarar a ransa su mummy suka shigo wajen bakwai na safe. Tareda abinci da abubuwan da za'a bukata. Muktar nanan yanda yake bai motsa ba.
Labari tuni ya karade dangi muktar yana asibiti. Tunda safe mutane suke sintirin zuwa dubashi. 'Yen uwa da abokan arziki.Umma ma da safe bayan ta hadawa fatima ruwan wanka ne. Dan na yau ya bambanta da ko yaushe. Aunty jamila ta kirata. Tsoratar da tayi ne yasa har wayar ta fadi ta fashe bata sani ba. Jiki na rawa ta shiga dakin inna ta sanar da ita. Baiwar Allah inna tabi ta rude tana a kaita wajen muntari itadai.
Fatima dake bkin kofar dakin zata shigo. Jigib ta fadi zaune. Tsoro, fargaba da rudewa sune suka ziyarci zuciyrta. Tuni jikinta ya fara karkarwa... daki ta shiga da gudu, doguwar riga ta zumbula. Tasa hijab. Bata tsaya ko saka dankwali ba ta dauki kudi ta duba time karfe goma da rabi na safe.
Ko dakin umma bata shiga ba ta bude gidan ta fice da gudu. Hanyar da zatabi ta rasa. Kamar a mafarki taji ance
"Zarahna"
A razane ta juyo jin muryar da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. To me zatayi ma.
Da gudu ta ruga ta rungumeshi ta fasa kuka mai karfi. Shima rudewa duk yabi yayi dan tun safe jikinsa babu kwari. Hannu yasa ya matseta ya bubbuga bayanta. Jin ta tsagaita kukan ne yake tambayarta me ya faru.
Cikin kuka ta fadi mishi abinda yake faruwa ta gama tareda kara rungumeshi."Shh, dont cry okay. Muje asibitin"
Batayi musu ba. Kasancewar motarsa tana gidan Abba, suka samu adaidaita. Minti shaa biyar ya kaisu. Fatima babu abinda takeyi sai kuka.
A tare suka shiga asibitin. Amma da mamakinsu suka ga kowa daga waje. Wasu na sharbar majina, wasu na goge hawaye.
Mummy kukanta takeyi tsakani da Allah. Dan kuwa kaf a yaranta. Muktar ne tafi so. Kodan shi baida isassar lafia ne.
Mutane sunsha mamakin ganin Aliyu. Dan kuwa bai fadama kowa zaizo ba. Ga murnar ganinshi ga fargabar halinda muktar ya shiga."Ina Muktar dinne naga duk kunyi cirko cirko anan kuna kuka" abinda ya tambaya kenan jiki qa sanyaye..
Farida ce tace
"Yaya gashi cikin dakin nan. "
Ta nuna dakinda muktar yake ciki
"Muna zaune fa,bayan fitar Abba yaje gida yayi wanka. Kawai ya muktar ya fara tari. A hankali jini ya fara biyo hancinsa. Bakinsa ma jini"
Gashi doctor dinda ya dubashi jiya yau da safe yabar duty. Wanda ya kamata yazo yauda safe is not here yet. Duka doctors dinda suke wajenshi. Likitocin mata ne, sundai je su bashi iya kokarin da zasu iya"
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...