💫🌼ThirtyThree🌼💫

3.8K 161 1
                                    

Written by khaair

Bayan sun gama cin abinci ya tabbatar data koshi sannan ya kyaleta. Ko mosti kadan fatima tayi sai yace

"Are you okay?"

Ita kuwa sai kara narkewa takeyi tana ta shagwaba. Shima zaune yayi ya biye mata.
Shaf ya mance da zuwa aiki. Har saida akayi masa waya.
Ya shaida asibitin gida babu lafia a masa afuwa. Sun karba korafinsa dan kuwa Aliyu akwai punctuality and regularity.

Fatima na kwance cinyarsa,  shi kuwa yana wasa da gashin kanta wanda yau din bai samu gyara ba amma yananan da shekinsa da kamshi.

"Zarah"
Ya ambaci sunanta a hankali

"Uhm"
Tace

Dagota yayi daga cinyarsa yana fuskantarta sosai yace

"Zarah, nasan kona ce kiyi hakuri dole kiji a ranki ina baki haushi. Amma don Allah zarah,  dan darajar manzon Allah ki yafewa yayanki laifukansa. Duk abubuwan dana miki wallahi bakin kishi ne ya rufemun ido.
Zarah kinsan ranar da aka kaiki gidan kabir, daren ban runtsa ba, har saida ibrahim yamun wayau yamun allura ashe ta bacci ce.
  Wallahi idan na rufe idona, ke nake gani da kabir kuna abinda mukayi jiya. Zarah,  wani sa'in kuwa kaina nake jiwa haushi, dan nine nayi nauyin baki, dana fada da wuri da Abba ni zayaba ke. Ko auren Asiya,  saidai naji anyi. Lokacinne na kara tabbatar da kinmun nisa.
Shiyasa itama Asiyar nayi watsi da ita. Sai daga baya ta fara bani tausayi, na kuma yi tunani sosai,  naga babu laifinta a ciki, in kuma na mutu da hakkinta fa, wallahi sannan ne na shiga dakinta.
Zarah, ranar da aka raba aurenki da kabir, kwana nayi yiwa Allah godiya,  abin bakin ciki ni abin murna ne  a wajena.
Zarah,  babu rana ko dare da zasu zo su wuce banyi tunaninki ba,  banyi begenki ba. Dan Allah kiyi hakuri ki yafemun kinji zarah"

Saiya sauko daga kujera ya tsuguna a kasa. Da sauri ita ta sauko kasan tareda cewa

"Dan Allah ka tashi daga tsugunen nan,  bai dace ba. Na yafe maka wallahi, daman ni ban rike ka da komai da. Nice zani ce ka yafemin laifukan dana maka da maganganun dana fada maka mararsa dadi wanda basu dace ba"

Rungumeta yayi yace

"Thank you zarah, you dont know how much i love you,  wallahi you mean the world to me. Jiya zuwa yau, Allah kadai yasan adadin farin cikin danake ciki. Allah ya miki albarka for keeping yourself for only me. Nasan yanzu ke zarah na ce ni kadai, kuma banaso wani namiji bayan ni ya dandani wannan zumar dana sha. Kabir ma yaje yasha bonus, ban yafe masa ba, amma kuma nine na bambare kayana daga leda"

Zare jikinta tayi daga jikinshi tareda rufe ido. Dariya yayi yace

"Ashe dai kunyar nan tananan. To Allah miki albarka"

"Amin"
Tace. Amma taki bude idonta. Pillow ya sauko kasa ya kwanta ya janyota jikinsa sukayi kwanciyarsu. Cen dai yace

"Zarah"

"Na'am"

"Kin tuno ranar da kika cemun mahaukaci, kika ce na sakeki,  bakya sona?"

Gyada kai tayi cikeda kunya da jin nauyinsa yanzu ne take dana sanin furta wadannan kalaman a gareshi.

"Wallahi ranar, naji haushin da ban taba jiba, amma dana zauna nayi tunani, wallahi sai naga sosai na fita daga sahun masu hankali. Mai hankali bazai taba irin abinda nayi ba,  waini harna daga hannu na mareki, zarah dan Allah kin yafemun marin dana miki?

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now