💫🌼chapter six🌼💫

3.5K 184 1
                                    

Written by khaair

Ana tashi islamiyya wajen sha biyu, basu tsaya wata doguwar hira ba kowa ya wuce gidan iyayensa. Koda itama fatima ta koma gida. Abba lokacin yake shirin fita. Da sallamarta ta shiga parlour Abba inda yake cin abinci. Risinawa tayi kadan tace
"Abba ina wuni, na dawo"
Murmushi yayi yace
"Sannu da dawowa 'yar albarka, ya karatun?"
"Alhamdulillah Abba"
"Babu wata matsala daiko? Ko bokon ma?"
"Babu komai Abbana"
Dubanta yayi yace
"Anya kinci abinci ma kuwa kafin ki fita? Kinyi wuri-wuri"
Dariya tayi"Abba banci ba, yanzun zanici amma"
"Ai babar taki ta fita tun wajen 11, bana tunanin da aninci a kitchen din, zauna kici wannan, fita zaniyi yanzu na makara, kuma zani biya ta wajen Bala mechanic in karbi motana, jiya ta tsayamun a hanya"
"Toh shikenan Abba, saika dawo, Allah ya tsare"
"Amin Amin, ki kula da kanki, bance a fita ba"
"Toh Abba"
Har waje ta raka shi tareda saya gidan, tasa sakata. Saida taci abincinta tsaf sannan takai kayan kitchen. Dakinta ta koma tana gyaggyara kayan data bata da safe, saida ta kimtsa ko ina ta dauko assignments dinta, physics ta farayi. Sannan ta shiga maths, tayi solving duk questions din amma banda guda daya, ta rasa yanda zatayi dashi, adduar Allah kawo mata Ya Aliyu takeyi, shi kadai ne zaya huce mata takaici. Kamar kuwa mafarki, saiji tayi ana kwankwasa gidan. Tashi tayi tareda yana mayafinta da key a hannu tayi wajen kofar, saida tayi tambayar ko waye taji shiru, taga ba'a shirin magana, ta bude kofar kadan ta leka, ganin Aliyu da wannan kyakkyawan murmushin nashi shimfide a fuskarshi yasata wage kofar ba shiri, har tayi kanshi zata rungume da murnarta, kome ta tuna kuma ta tsaya tareda ja da baya tana tunzurar karamin bakinta, ala dole tayi fushi dashi. Shi kanshi yasan laifinshi, shiyasa yazo ban hakuri. Dariya yayi wacce inba fatima ba ko umma, dakyar kaga yana ma wani dariya, sai kuma dangi da dai wasu mutane kalilan. Sai kuma uwa uba hussaininshi, mukhtar. Ko yau dinma tare sukazo. Shi kuma muktar rikakken lawyer ne a garin katsina mai zaman kansa.
"Haba zarah, yi hakuri kinji kanwata, nasan nayi laifi, kiyi hakuri, kinga tare nake da mukhtar kar ya mana dariya."
Jin  an ambaci mukhtar ya sata saurin fitowa gidan tana leqe leqe, aiko ta hangoshi cikin mota yana latsa waya. Shima kamar ance ya daga ido, yana dagowa ya hangeta, da murmushinsa ya ajiye wayar ya fito yana cewa
"Lale lale maraba da yar kanwata, wallahi nayi missing dinki, gashi kin bar lekomu yanzu"
Turo baki tayi tace
"Kaima wallahi ya mukhtar mun kusan batawa dakai, daman shi Ya Aliyu mun rigada mun bata"
Ta juya ta kalli Aliyu dake kallonsu yana daria, murguda masa baki tayi  ta juya. Aliyu yace
"Lalala, zarah waya koya miki wannan murgude murguden, lallai ashe zamu hada kafar wando dake"
Rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka tace
"Ka gani ko ya mukhtar, waima zamusa kafar wando guda"
Dariya sosai mukhtar yayi, saboda shi daman ko asali akwai dariya, balle ma ya samu dalili.
"Yi hakuri my sister, muje daga ciki kar a jimu daga waje."
Gidan suka shiga, parlour umma suka yada zango dukda bata gidan amma kullum sai an gyara shi, kuryar dakin ne dai aka rufe.
Nan Aliyu ya shiga bada hakuri ya hada da cewa
"Mukthar ka tayani bata hakuri mana, shiyasa fa nazo dakai"
Dariya muktar ya kara yace
"Toni ai ko laifin ma dakayi ban sani ba, ya za'ayi ma na bada hakuri"
"Waifa dan jiya banzo ba mukaje yawo, kuma bamujr wajen umma ba."
Zaro ido yayi yayi yace
"Ashe laifin naka babba ne Aliyu, dole kake zuwa ka bada hakuri, to yanzu bintu, yanda za'ayi shine, ki tashi ki shirya kiyi kwalliya sai muje yawon, mu kaiki wajen umma, sannan muje gida ki gaishe da su mommy, sunata cigiyarki"
"To ai Abba yace karna fita ko, saidai idan ka kirashi ka tambayesa, inya bari sai muje."
Ba musu mukhtar ya dauki waya ya kira Abba, bugu biyu ya dauka. Bayan sun gaisa, ya tambayi izini
Dariya abba yayi ta waya yace
"Bintu rigima, ashe bata mance ba, jiya fa ni nayi lallashi, ita wai yayanta baizo ba yabar sonta."
Shima mukhtar dariyar yayi yace
"Shine fa nan ma taketa rigimar, ita tayi fushi."
"Toh Allah huci zuciyar gimbiya. Kuje sai kun dawo"
"Toh Abban mu mun gode."
Saida ta matsa ya koya mata assignment dinta, sannan ta shirya, bakar after dress da veil dinshi tasa, ba kadan ba kayan sun mata kyau abinka da farar fata.
Tunda suka fito gida  babu wanda yace komai, fatima ta gaji da shirun tace
"Ya Aliyu ina zaka kaimu?"
Yana tukunsa yace
"Gidan yankan kai"
Turo baki tayi, ta mirror ya kalleta ya mata gwalo.
Rau rau tayi da ido tana kallon waje. Sajuma suka tsaya, a mota suka barta, Aliyu kayan kwalam yayita kwasa yayi leda uku. A bayan motar, gefen fatima ya ajiye. Ya koma inda yake ya tada motar. Gidan mahaifinshi sukaje, aikuwa sunyi murna sosai da ganinta. Sunsha hira, saida karfe uku Aliyu ya shigo gidan. Dakin mahaifiyarsa ya shiga yace
"Hajia bari na kaita gidan Aunty Asiya. Ta kira tanata korafi wai ba'a kawo mata Zarah, kinsan ta ita fada."
"Kaga ni babu ruwana, ka kaita din, sannan ka tabbata ka kaita wajen ummanta."
"Toh hajia." Ya kalli binafa yace
"Ki daura veil dinki Zarah muje."
Har kofa hajia ta musu rakiya, tareda bawa bintu 'yar leda. Risinawa tayi ta karba tareda godiya.
A gidan Aunty Asiya sukayi sallar la'asar. Karfe 4:30 suka isa wajen umma. Tana saman sallaya da gani tunda tayi sallah bata tashi ba.
Da murnarta ta karbesu tana cewa
"Yanzun nan nake tunaninku a raina, nace jiya baku zoba ko lafiya. Gashi na kira wayar taka Aliyu bata shiga ba, yau kuma babu chaji wayar, rabonmu da wuta tun jiya da safe. Injin dinma kamar ya samu matsala. Hajia ta kira mansur mai gyara acan bakin titi, amma dai yaki tashi."
Ta kare maganar tareda shimfida musu tabarma da ruwa.
"Wallahi umma jiya a asibiti na kwana, harfa na taso aiki wajen 5 aka kirani ina bisa hanya wai an kawo wasu emergency, accident ne akayi. Dole tasa na koma.
"Allah sarki, wallahi rayuwarnan saidai Allah sa mu dace, amma yanzu yawan mutuwa da hatsari yayi yawa."
"Umma saima kina asibiti, wallahi cases din sunyi yawa. Allah dai ya kawo mana sauki. Munata surutu bamu gaisa ba. Ina wuni umma.?"
"Lafia kalau Aliyu"
Itama binafa nan suka gaisa. Tana tambayarta boko.
"Umma Alhamdulillah, saura fa duka how many weeks ma muyi exams, finally mu shiga ss3."
"Toh Masha Allah, kiyita maida hankali kinji ko? Allah miki albarka."
"In sha Allahu umma, Amin ya rabb"
Aliyu ya mike tsaye yayi hanyar dakin Hajia, yana fadin
"Tsohuwa mai ran karfe, ina kikaje ne?"
Umma ce take shaida masa ai bada dadewa ba kawu ishaq yazo ya kaita asibiti, tanata korafin ciwon kafa tun kwanakin baya
"Yama isa ace sun dawo hakanan, kilan kuma sun biya wani wurin"
Fatima tace "Allah sarki hajiyarmu, Allah bata lafia."
Suka amsa da Amin.
Fatima ta kwanta a cinyar umma tana  cewa "umma na gaji, bara na huta kadan kafin mu tafi."


To nima nace bara naja bugatti kafafu naje na huta. See you in the next chapter❤

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now