💫🌼Twenty six🌼💫

2.8K 143 0
                                    

Written by khaair

Tun bayan da kabir yabar office din mustapha. Bai tsaya ko ina ba sai gida. Dan kuwa kanshi a cunkushe yake. Mamaki da tsoro ne fal a ranshi. Kenan mutane ma ba kowanne zaka gani ba kace ga halinshi.

Mustapha class mate dinshi ne tun nursery, har suka gama secondary. Abokinshi ne sosai. Kawai halin rayuwa ne da yau da gobe yasa suka rage neman juna, amma suna gaisawa akai akai. Shidai tun suna yara baisan mustapha da wani hali marar kyau ba saina shaye shaye da kuma son mata, duk macen da zata wuce sai mustapha ya bita yace yanaso, to kasancewarshi mai kyau sosai, kuma sunada kudi duk wacce ya tsaida saita bada kai.
Shima shaye shayen suna gama ss3 iyayenshi suka kaishi NDLEA. Anata tsegumin ai kara lalacewa zaiyi. Saidai koda ya dawo, ko sigari mustapha yabar sha.

Shiru kabir yayi, cen kuma ya nisa cikin ranshi yace
"Toh kodai tun a rehab dinnan mustapha ya koyi halayen banzan nan? Tunda wuri ne da za'a hada maza sama da arba'in a cikin daki karami. Ba shakka ma acen ne. La haula walakuwwata illa billah, mustapha ka sanya kanka ga hakala"

Haka yayita tunane tunane har ya dawo gida, fatima batayi mamakin ganin yanda yanayinshi yake ba.
Toh wanda masifu daya bayan daya suke bibiyar su, dole ya shiga halin ha'ula'i.
Babu abinda takeyi sai aikin kwantar masa da hankali. Ko yanaso ya saki jikinshi, daya tuno yana cikin tsaka mai wuya ne, sai a koma gidan jiya.

***

Sati guda bayan wannan al'amarin. Kabir ba inda baije ba inda yasan za'a taimaka masa, amma kowa saiya nuna yanda halin da kasar take ciki. Wanda har mamaki mutane suke bashi. Tun daga dubu dari, abinda yayi miliyan hamsin yana iya bayarwa rance. Wani lokacin in yana kunyar mutum, saidai ya bashi kyauta. Amma mutane sun mance da haka. A ganinsu tunda wannan masifa ta fada mishi, baida kudin biya, saidai ya dulmiyar dasu.

Kabir har wajen kawunninsa yaje, cewa sukayi yanzu ciniki yayi karanci. Babu kudin nan a kasa.

Kabir ba kadan ba ya shiga hali. Fatima wani lokacin saita saka mishi kuka yakecin abinci. Wani sa'in ma rufe kanshi daki zaiyi yayita kuka. Toh kukan ne yake rage mishi wani zafin. Lallai mutane abin tsoro ne, kullum kalmar da zakaji ta fito bakinshi kenan. Daga nan ya yanke shawarar nemar wa kansa mafita. Kota wanne hanya.

Kwana hudu bayan wannan. Fatima ta rasa gane kan kabir. Inhar yayi sallah to bazai tashi ba zaiyi ta kuka yana rokon Allah ya yafe masa.

Akwai randa taje school, tayi lectures din 2-4, ta shigo gidan. Kabir ta gani durkushe bisa sallayar yana fadan

"Ya ubangijina, na saba maka, nabi hanyar daba ita ba, na cuci kaina na cuci duk wanda suke mun fatan alkhairi, ya rabbi ka dubeni da idon rahmarka marar karshe ka yafemin"

Sosai fatima ta tsorata. Amma tayi tayi da kabir ya fada mata abinda ke damunsa, yace mata babu komai. Hakanan ta hakura ta barshi. Saidai har cikin zuciyar tana tausaya mishi da halin daya shiga.

Washe gari ta masa karyar tanada lectures din safe. Bayan ta kammala kalaci ta shirya ta fita. Amma bata zame ko ina ba sai gidan mama, mahaifiyar kabir.
Mama tayi murna da ganin fatima, tana nan nan da ita. Amma murnar ce ta koma lokacinda fatima ta fadan mata dalilin zuwan.
Mama itama ta girgiza, amma tayi alkawarin zuwa da maraice taji. Sai karfe sha biyu fatima ta koma gida.

Da maraice wajen biyar, saiga mama driver ya kawota.

Ta zaunar da kabir. Tambayar duniya ta masa, amma sam ya kasa ce mata uffan saidai hawayen da yakeyi. Nan ta bashi baki, ta hada da fada da nasiha. Sannan ta kuma ja kunnensu dasu rike juna amana, su rike Allah, kar dan sun shiga wani hali su butulcewa ubangijinsu. Ita kaddara mutum baya tsallaketa. Kuma indai mutum yayi hakuri, komai mai wucewa ne. Koba komai, wannan iftila'in daya fadawa kabir, ya gane masu sonshi na gaskia da masu son abun hannunsa.

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now