Written by khaair
Tun daga wannan lokacin Aunty Bilkisu ta rage shiga harkar Binafa. Itama ta samu saukin takurar. Kuma tana dan sakewa cikin gidan. Yanzu Abbanta ya rage zama kasuwa saboda gudun kar a cutar da binafa.
Bayan shekara uku
A kwana a tashi asarar numfashi, fatima bintu yanzu shekararta goma sha biyar, ana ss2. Girmanta da kyaunta ya fito sosai, daman gata kyakkyawar gaske. Dirinta da kyaun surarta ya bayyana. Shiyasa har dar in fita takeyi, yanzu maza zasu fara bibiyarta.
Daga manya har yara sunsha zuwa wajen Abbanta suna sonta, sai yace yarinya ce sosai. Girman jiki ne kawai. Shiyasa daga boko sai islamiyya,sai gidansu Asiya kawarta, sai kuma in Aliyu yazo friday, suje gaida dangi, sannan ya kaita wajen ummanta tayi weekends dinta acen. Har gobe akwai shakuwa mai tsanani a tsakanin Aliyu da fatima, wanda a bangaren Aliyu, shakuwar ta shiga jininshi har bargon kashinsa, ta zama soyayya mai karfi. Shiyasa dukda yanzu yaci ace ya tsaida matar aure, shekara 26, amma ranshi Fatima yake bege. Bai taba nuna mata alamu ba koya fada mata. Jira yake ta gama secondary ya fadawa Abba dukda cewar yasha fadawa umman binafa in tana masa maganar aure sai yace saidai in zata bashi Zarah, zaiyi aure cikin shekararma. Saidai tayi dariya dukda tasan cewar da gaske Aliyu yake.Yau asabar, dayake babu abinda fatima takeyi gida, tayi shirin islamiyya tsaf, ta shiga ta gaida Abba da Aunty bilkisu, tace ta tafi islamiyya.
"Bintu tun yanzu? Bakiyi sammako ba kuwa? Naga 7:30 fa."
Murmushi tayi tace
"a'a Abba, yawanci innaje 8 din sai kaga an barni cen seat din baya banajin me akeyi sosai. Gwara naje na samu gaba na zauna kafin malaman su karaso."
"Allah sarki bintu na 'yar albarka, to shikenan kije, Allah tsaremun ke. Ya dawo dake lafiya"
Dariya tayi sosai tace "Abbana mai sona, Amin Abba, nagode. Saina dawo."
"Kin biya kin gaida babarki ko?"
"Na shiga Abba"
Gyada kai yayi yace "Toh Allah yayi albarka. Sai kin dawo"
"Amin Abba."Waje tayi, dayake akwai dan tafiya tsakanin gidansu da islamiyyar yasa take danyin sauri. Saida tazo kusa da islamiyyar ta rage saurinta.
A guje ya shigo kwanar, domin sauri yake ya isa inda ake nemansa. Adan tsorace yaja birki ganin ya kusa bange mutum. A fusace ya leko da niyyar fara masifa, amma cin karo da kyakkyawar fuskar da binafa data rumtse idonta dan tsananin tsoron dataji. Sai yaji jikinshi yayi sanyi ya kasa yin masifar da yayi niyyar yi. Fitowa yayi daga motar ya matsa kusa da ita yace
"Baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah, wallahi sauri nakeyi ne, ban lura dake ba. Kiyi hakuri dan Allah"
Fatima bude ido tayi tadan zare su ganin wanda ke mata magana. Kasa cewa komai tayi saidai kallonsa da take daga sama har kasa. Dogo ne sosai, wankan tarwada, fuskarsa kyakkyawa da dan karamin gemun daya tara, idanunsa farara sol, ga dogon hancin daya dace da fuskarsa, karamin bakinsa baki ne, madaidaici. Jikinsa kuma budadde ne, daga gani basai ka fada ba, yana gyming, manyan kaya ne jikinsa Ash colour da hula wacce ta dace da kayan a kansa. Bata ankara ba taji ya kara magana yace "na tsorata ki ko? Kiyi hakuri dan Allah."
Kunya ce ta kama ta tayi saurin saddar da kai, a hankali tace
"Babu komai, amma ka dinga kiyayewa saboda gaba."
Murmushi yayi yace
"Nagode kanwata"
Itama murmushin tayi. Motarsa ya koma ya tada ya wuce, itama ta raba gefe ta wuce.
Haka ta isa islamiyya. Tana zuwa ma har 8 din tayi. Ta samu waje ta zauna. Umdatul Ahkam ne suka fara, suna babul siwak, sosai taji dadin karatun yau. Saboda a layin gaba take. Ta fahimce komai. Karfe goma suka fito break din 10minutes. Itada kawarta Asiya, wacce tun yaransu suke tare, suka fito break, nan take bawa Asiya labarin abinda ya faru dazu, ta hada da cewa "wallahi Asiya, yanada kyau, kinga wai kunyar danaji daya sake mun magana, ni kuwa kallonshi nake ko blinking banayi."
Asiya tayi daria sosai "shegiyar mata, yanzu ke bintu har kinada bakin cewa wani nada kyau, ga Ya Aliyu nan, duk unguwar nan wallahi bamai kyaunshi. Kuma keda kike cemun kin tsani maza, ni banda ma Ya Aliyu, banji kin tabamun hirar wani ba, sai new catch inki" ta ida maganar tare da kashe ido tana daria. Fatima ta kai mata duka "kedai wallahi haka kike bakida kirki, ya Aliyu yayana ne fa. Kuma nasan kyakkyawa ne amma ai bance komai ba bayan danace shi mutumen yanada kyau. danna baki labari shikenan, ai ba cewa nayi sonsa nake ba"
Asiya ta kara daria tace
"To dan kince sonsa kike ma minene, kinfa girma"
Zaro ido bintu tayi tace "keeeeh, so kike yi Ya Aliyu da Abba su kasheni? Ni inje in fara maganar soyayya ko secondary school ban gama ba. Ya Aliyu kullum sai yamun fada yaja mun kunne akan maza, ni kuma gaskia bazan iya bijirewa maganarsa ba"
Asiya tadan murguda baki tace
"Ki tsaya nan ki bari har lokacin aurenki yazo ki rasa mai aurenki, tunda ke baza kiyiwa kanki fada ba. Miye dan kina son wani? Ai gani nake ba wani abu bane, kuma tun yanzu zaka ajiye tsayayye, lokacin aure na zuwa an riga an saba ki fiddo shi. Ke, wannan zamanin fa ya wuce wanda za'a hana mutum saurayi, lokacin aure na zuwa a aura mishi wani a dangi"
Fatima mamaki ne sosai ya cikata, ko da yake ba abin mamaki bane ba. Asiya daman batajin magana, gashi kullum jerin marasa kunya ake sata, har mamakin kanta take wata rana da take kawance da Asiya. Halinsu kwata-kwata ya banbanta, Fatima ga hakuri ga sanyin rai, gata kyakkawar gaske, batada shawa'ar yin saurayi koda wasa. Saboda gargadin da Aliyu ya mata akan maza. Ga uwa uba ladabi da biyayya, batada girman kai sam, kowa nata ne. Ita kuma Asiya tanason yin samari, gashi ita ba wata kyakkyawa bace, baka ce doguwa, tanada dan jiki kadan, idanunta madaidaitu, sai kuma guntun hanci da baki madaidaici. Sai son gayu da kwalliya. Amma ikon Allah har yau bata samu wanda yace yana sonta ba. Shiyasa in bintu na bata labari wani ya tareta, ko yace yana sonta, saita dinga mata fada meysa take korar masu sonta.
Asiya ce tayi magana tace "kikayi shiru kina kallona"
Murmushi kawai fatima tayi.
"Ha'an kiyi magana mana bintu""Ni wallahi zabin Abbana shine ma zabin da nakeso, nasan bazai cutar dani ba."
"Lallai ma, to Allah yasa mu dace tohm"
"Amin kawata, mu koma class, ga mallam musbahu nan yazo, nasan ko hadda baki iya ba...muje na biya miki""Wallahi kamar kin sani, ban iya ba mu zauna back seat ki biyamun, kafin azo kanmu nasan na rike"
"Allah shiryeki asiya"
Daria Asiya tayi tace "Amin"_khaair❤
Your votes give me courage.
Share and comment please❤
![](https://img.wattpad.com/cover/126442930-288-k893284.jpg)
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomantizmFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...