Written by khaair
Sake maimaita mata tambayar yayi. A hankali tace
"Yaya ba waya nake ba, ban sanma tana cewa number busy ba"
Shiru yayi cen kuma yace
"Toh shikenan, hope kina lafia dai."
Murya cen kasa tace
"Lafia kalau yaya, ya aiki ya karatu?"
"Alhamdulillah, yasu Abba da mutan gida"
"Duk suna lafia"
"Ki gaishe mun dasu duk. Yau kuwa muktar yazo?"
"A'a baizo ba gaskia. Amma ya kira yace aiki ne ya masa yawa, suna wani shari'a ne, ba zaune yake ba."
"Okay, to kice masa dai yana kirana, kinsan bana iya samunsu, bansan dalili ba."
"Toh yaya in sha Allah"
"To maza jeki kwanta, banason ana kai war haka ba ayi bacci ba kinji ko? In sallah zakiyi, ki dinga sanya alarm saiya tasheki wajen 2 ko 3 kiyi abinda zakiyi ki jira ayi subh saiki kwanta. Kinji ko?"
"Toh yaya, kayi hakuri bana sakewa"
"Good girl, now go to bed, saida safe"
"Allah tashemu lafia yaya"
"Amin" yace tareda katsewa.
***
Da sassafe ta kasance ranar Alhamis, babu abinda fatima takeyi. Ganin haka yasa ta fincike dakinta ta mishi sama da kasa.
A hankali ta shiga gyarashi, ko ina yayi tsaf dashi. Ta goge ko ina.Hakama ta shiga dakin Abbanta. Wanda baiyi minti talatin da fita ba. Shima haka ta gyara mishi shi tsaf.
A zuciyarta tana tir da halin Aunty bilkisu. Bata taba ganin ta dauki koda tsintsiya bane da sunan zata gyarawa Abba daki. Saidai tasa masu aiki.
Abba shi kuwa yace bayason masu aiki su mishi aikinda matarshi ta aure ba zata mishi ba.
Abinda umma batayi kenan. Hatta inner wears din Abba ita take wanke masa, bata yarda wata mai aiki tawa mijinta wani hidima ba. Sudai tsaya ga wanki, dan har wanke wanke ita take masa.
Abinda yayi ga dakinshi, bayinshi da duk wani abu daya dangance shi itace.
Abinci kuwa zata zauna ta masa iri iri, yaci saiya ture. Amma tun sabanin da suka samu da umma ta tafi, abubuwanshi suka tabarbare, komai nashi kara zube.
Abinci ma wata ran baya samu, in yayi magana tace ai ita daman zaman hakuri takeyi, kuma ita batajin dadi, saidai yaje yaci na waje, in kuwa yaga ya gaji sosai, zaya zauna da yunwa ne har saiya samu ta dafa din idan taga dama.Inka shiga dakin kwanansa kamar na samari yen makaranta dan yanda yayi kacha-kacha. fatima ce daman weekend in batada hidima take sharowa ta goge ko ina. Yanzu ma da bata zuwa ko ina. Da safe zata sharo tayi mopping. Abinci ma tana dafa mishi iri iri. Shiyasa yake kara godiya ga ubangijinsa daya bashi fatima.
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...