💫🌼thirty🌼💫

3.4K 169 2
                                    

Written by khaair

Asiya duk tabi ta daburce, ta rasa ya zatayi, tasan karyarta ta rigda ta kare.
Kukan kuran da Aliyu yayi ne yasa ta makale maganar da zata fiddo, bata ankara sai ji tayi ya shakare ta, magagi ta fara tana rike hannunshi tare da bude baki tana neman iska. Dukan hannunshi takeyi amma sam bai kyaleta ba, saida yaga ranta na gab da fita ya ingizata kasa. Ya hau dukan ruwan cikinta. Saida ya tabbatar ta jibgu ko motsin kirki batayi sannan ya zare falmaran jikinshi, ya bar doguwa kawai. Kan fatima yazo wacce sam bata motsi, ko numfashi batayi.
Ya rasa to ina ma zaya fara. Sabarta yayi kawai ya dauki key din motarsa ya fice da ita.

A asibiti kuwa, shida abokan aikinshi sukayi attending dinta. Duk wata kulawa sun bata amma fatima sam ko yatsanta bata motsa ba. Saidai numfashinta ya dawo. Amma sam bata haiyacinta.
Aliyu kuka ya zauna yanayi wiwi, kenan daman Asiya azabtar da Zarah take in bayanan, shine abinda yake maimaitawa a ranshi, aiko saita gane kurenta, dan bamai taba masa ita ya kwana lafia. Bari dai ta farfado sannan.
Kafin kace me, duka gida suna asibiti. Kowa yana jimamin irin wannan rashin imani na Asiya, dan kuwa Aliyu bai boye musu komai ba ya fada gaskia danji yake a duniya yanzu yafi tsanar Asiya da kowa. Inta bari suka gamu, saiya lahantata yanda ta nemi lahanta fatima, wama yasan ko kasheta tayi niyyar yi haka yake ta cewa.
Dukda hakan su daddy sukace sam bai yarda Aliyu ya saki Asiya ba. Dan babu wanda yasan miya hadasu harya kaida kwanciyar fatima asibiti.

Fatima ta share 2weeks a asibiti bata ko wani motsi. Dan babu wani likitan zuciya asibitin mai zama din din din. Har saida dr. Azeema ta dawo daga tafia. Tayi bakin cikin jin yanda abin ya faru. Ta duba fatima, aka yi mata X-ray. Tace dole yanzu sai ayi surgery dan kuwa aikin da aka mata watannin baya ya dawo sabo. Inma ba'a ciro abinda aka saka mata ba, zaya causing wani damage ne. Dan haka bama sai sunje Abuja ba, su zasu aika daga abuja din a gaiyato cardiac surgeons suzo nan.
Dan fatima is in a critical condition. A cewar dr. Azeema. Ko kwana uku ba'ayi ba gaiyar doctors suka zo.

Washe gari ba tareda bata lokaci ba Aliyu ya saka hannu, aka shiga da fatima dakin surgery. Saida suka dauki awa yafi uku sannan wani doctor ya leko, ya kira wata nurse, yace a dauko heart-lung bypass machine.
Babu bata lokaci aka kawo. Tun abin karfe sha biyu, sai shida na maraice suka tabbatar da komai daidai, su daddy saidai suje suyi sallah su dawo, Aliyu kuwa, kasa kwakkwaran motsi yayai, dan kuwa ji yake duk dalilinsa ake wahalar da fatima, gashi yanzu anja mata wani bala'in kwanciyar asibiti.

"Saina ci uban yarinyar nan inta bari na iske ta gidana"

Abinda ya furta kenan a tunaninsa cikin zuciya ne, wanda baisan harsu daddy sunji shi ba.

Shida da rabi daidai doctors din suka fito su duka. Kuma suka bawa su daddy goodnews din komai daidai.

Amma dai fatima din sai nanda 8-10hours zata tashi, kafin anesthesia dinda aka mata ta saketa. Aliyu dan murna har sujudu shukur yayi. A tare suka shiga dakin bayan dr williams yace zasu iya shiga, amma a sassauta surutu.
Gaba daya suka shiga daki, har rige rigen dubata suke. Aliyu kasa dauke idonsa yayi daga kanta. Inda za'a bara zuciyarsa gida biyu yanzu, da anga yanda soyayyar fatima take tafarfasa a zuciyarsa.
Da Asiya batayi kuskuren koda ma fatima kallon banza bane. Shi kome ya mata da dalilinsa, amma ita baiga wani dalili ba banda tsohon kishin banza, wanda zaya kasheta ne a banza, dan har abada bata taba samun kwatan gurbin da fatima take dashi a zuciyarsa, jigo ce a rayuwarsa.
Hawaye suka zubo mishi, yayi saurin gogewa. Abba yadan bubbuga bayansa. Juyowa yayi ya rungume Abban yana kuka yana cewa

"Abba wallahi inhar wani abu ya samu Zarah na, wallahi bazan kyale wannan tsohuwar bakar algungumar ba. Wai kaga yanda ta mata duka ne a kirji, wallahi inda banzo ba, ni nasan kasheta tayi niyyar yi. Wallahi saina muzanta mata. Wane irin bakin kishi ne haka. Yarinyarda ko fita batayi daga section dinta saidai ta kama. Amma ta bita har dakinta ta mata wannan cin zarafin"

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now