💫🌼twenty🌼💫

2.6K 128 3
                                    

Written by khaair

"Wayyo ni, na shiga uku ni kaltume, me nake gani haka, muktar meya sameka"

Abinda mummy take fada kenan yayinda ta tsuguna ta tallabo kan muktar da jini keta zuba. Bata san lokacinda hawaye ya fara biyo idanunta ba.

Adaidai nan duk yan gidan suka fito, dayake duk anan suka dawo kafin a gama biki. Da yen uwa duk ananan. Ba karamin razana sukayi ba ganin mummy tallabe da muktar wanda yake kwance sharkaf kamar gawa.

Agurguje suka iso ana tambayarta lafia.

"Ku kiramun sada kuji, ku kirashi azo akai muktar asibiti. Kar yarona ya mutu." Abinda mummy take fada kenan tana shafar fuskar muktar.

Tashin hankali ba wanda basu gani ba jin sun kira wayar daddy a kashe. Aunty jamia ce tayi ta maza ta wawuri key din mota tace

"Mu tallaba mu kaishi mota, mu fara zuwa asibitin, a kira daddy daga baya. Kar ayi saki na dafe"

Babu musu suka tallabr shi. Mummy taki sakinshi kona second guda. Aunty jamila ta kwankwasa wa mai gadi yazo ya bude gida. Shima a kidime ya bude jin ance muktar baya lafia. Ya dauka ciwon zuciyarsa ne ya motsa. Hangoshi da jini a jiki, duk sai ya rude, jiki na karkarwa ya bude gate din. Akai akai mummy ta koma taki, haka ta zauna da muktar baya sai su fadila itada farida suka shiga gaba.

Ba bata lokaci suka yi asibiti. Alheri clinic yafi kusa da gidan. Saboda haka shi aka wuce dashi. Sunyi sa'a dr johnson yananan. Shine ya tarbesu. Nurses suka kawo gado aka wuce dashi emergency. Mummy kuka kawai take. Jikinta duk ya baci da jini.

Aunty jamila tayi sa'a tazo da waya saboda haka ta kira wayar Abba. Abba da bacci ya fara fisga, a hankali ya bude ido ya jawo wayarshi. Ganin sunan jamila yasa dauka da wuri.

"Abba dan  Allah kazo asibiti. Ya muktar babu lafia. Ya fadi kasa, kansa ya bugu. Ni gani nake jininsa ma ya kare"

Shine kawai abinda yaji. Tsananin rudewa ne yasa daddy ko takalmi baida shi ya fito gidan. Kofar gidan ya bude. Harya fita, kome ya tuna kuma ya sake dawowa gidan. Gani yake inya tsaya fiddo mota wahala ce, hakan yasashi sauri sauri gudu gudu. Asibitin daga gaban gidanshi ne. Layi biyu ne a gaba. Shiyasa ya kasa daukar motar. Baima san baida takalmi ba. Haka ya dinga gudu cikin dare. Harya zo wajen wasu yen banga dake kwanar asibitin.

Tareshi sukayi suna tambayar waye. Suna haskawa sukaga Abba, sunsha mamaki dan kuwa ganin irin lokacin dayake waje.

Baibi ta kansu ba yaci gaba da gudu. A harabar asibitin ya iske su jamila. Sannu suka mashi. Guri ya samu ya zauna yana tambayar ba'asi. Sai lokacin mummy tayi magana.

"Wallahi yaya, wai na gama sallah ina lazimi, nasan dai naji sallamar muktar. Tunanina sai yaci abinci zaya shigo. Toh kuma can sai naji faduwar abu. Ina fitowa na duba. Naga yaro kwance shane shane cikin jini kanshi ya bugu da jinin tile."
 
Ta karashe maganar cikin kuka.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Abinda daddy ya samu ya furta kenan.

Kasa magana yayi. Su jamila suka mashi bayani.  Ta kara da cewa

"Yanzu an shiga dashi emergency. Allah ubangiji yasa ba wani babban ciwo bane. Bawan Allah gobe daurin aurensa"

Shiru kowa yayi yana saka a cikin ransa.

Bayan minti 20


Doctor dinne ya fito. Nurses na bin bayansa. Bismillah yawa daddy a office dinshi.
Bayani sosai yawa su daddy kan cewar Zuciyar muktar inba heart transplant aka masa ba, dakyar yasha. Dan kuwa bata bugawa yanda ya kamata. Ta cunkushe jini baya pumping sosai.
Sannan as a result of heart failure dinnan ne ya fadi. Mistakenly ya buga kanshi. Jini ya shiga kwalwarsa. Yana bukatar aiki. Yanzu sun bashi all necessary ailments. Zuwa safe zasu magana da asibiti a Abuja. Zasuyi referring dinsu acan, saboda su basayin major surgeries anan.

Kowa saida jikinshi yayi sanyi jin irin bayanin dr. Johnson.
Abba ne yayi karfin hali yace

"How is he now doctor?"

"He is doing no better honestly. But we will try our best. We've mixed sleeping pills in his drip. You shouldn't worry aloy, he will not wake up till morning."

"Thank you doctor, please do your very utmost, he is getting married tomorrow, i dont want anything to go wrong"

"Nothing will go wrong by God's grace"

"Can we see him?"

"Yes sure you can"

A tare suka dunguma dakin da nurse ta musu kwatance.
Kwance yake bisa gado. An canza mishi kayanshi zuwa na asibiti. Kanshi daure da bandage wanda shima jini ya jika shi.
Hannushi drip ne manne. Duk mai imani inya ganshi saiya bashi tausayi. Jiki a sanyaye suka karasa dakin suka zazzauna. Abba kasa zama yayi. Saidai ya tsurawa muktar ido. Haka mummy ma.

Wajen karfe daya da kwata Aunty jamila tace

"Abba kuje gida..ni bari saina zauna anan din. Ga key din mota sai fadila ta  kaiku gidan"

"A'a, kuje din, ni zani zauna, irin wannan sai babba, in case wani abun ya taso. Kikai mummynku gida. Kinji ko, sannan kima kaninki addua. Karku sanar da sada din sai zuwa gobe. Karku tada mishi hankali ciki dare"

"Toh Abba"

Sukace gaba daya yaran.  Dakyar mommy ta yarda suka tafi. Kuka jina jina. Kukanta ne yasa su farida kuka suma. Jiki ba kwari abba ya samu wuri ya zauna. Sai a lokacin ya lura da kafafunsa babu takalmi. Tsuka yaja kadan. Ya maida kallonshi ga muktar da yake kwance lifelessly.

"Allah tashi kafadarka muktar."

Nima kaina muktar din ya bani tausayi dan har kuka saida nayi nace

"Amin Abba"

***

Fatima kuwa kasa bacci tayi. Hakanan duk taji kasa ta rufeta. Jikinta har nauyi yake mata. Sallar daren data saba yauta kasayi.
  Duk batajin dadin komai.  Addua ta shiga yi tana karanata innalillahi wa inna ilaiji rajiun har taji dan sauki. Alwala ta dauro ta kabbara sallah. Kamar kullum tayi nafilfilunta. Ta shafa addua. Saidai adduar yau ta bambamta. Yau ta roki Allah bata zaman lafia a sabon gidanta inda zata fara sabuwar rayuwa. Ta shafa ta koma gado ta dukunkune a blanket. Amma ta nemi bacci ta rasa. Muktar ne kawai take tunani.
Mikewa tayi zaune tace a fili

"Ya muktar, you keep coming to.my thoughts, i hope u are doing good over there"...


Khaair❤

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now