💫🌼chapter two🌼💫

6.3K 369 14
                                    

Written by khaair

Tananan yanda ya barta, tana numfashi sama-sama, sautin numfashinta kamar mai munshari, bugun zuciyarta daka saurara zakaji ba daidai yake ba.
Tausayinta ne ya kamashi ganin yanda farat guda ta kara fari kamar fatalwa, tayi wata irin rama sosai. Hawaye yayi nasarar sirarowa a kumatunshi, ya zauna gefenta tareda riko hannunta yana jujjuya zoben hannunta. Yakai minti ashirin haka, babu abinda yakeyi sai kuka kamar wani karamin yaro.

A haka mahaifiyarshi ta shigo  hankali tashe. Hankalinta bai kara tashi ba saida taga danta tilo da Allah ya bata cikin mata biyu yana kuka Allah annabi. Dukda ba abin mamaki bane tasan irin sonda kabir kewa fatima bana wasa bane. Sallamarta sa sashi dawowa hankalinshi, da saurin goge hawayensa yana daidaita natsuwarsa.

Murmushin karfin hali yayi yace "mama harkin iso? Sannu da zuwa."
Tashi yayi ya bata kujerar da yake zaune yana mata sannu.

"Ya jikin nata? Itace tambayar data jefa mishi. Dam! Gabanshi ya fadi yana koron karta tambayi ba'asi. "Da sauki sosai mama, amma dai har yanzu bata farka ba, tun wajen bayan azahar. Gashi yanzu la'asar harta wuce." Maganar yake idonshi dukya cicciko da kwalla.
" Tome akace yana damunta?" Cikin damuwa yace "wallahi mama, wai neumonia dinta dinnan daine…" nan ya mata bayanin komai bai boye duk abinda doctor ta fada masa ba. Ya karashe maganar yana goge hawayen da suka zubo. Salati  tana cewa
"Yanzu duk wadannan ciwukan daka lissafa mun sune suke damunta? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah tashi kafadunki bintu ya baki lafia..."

karar bude kofa ne yasa su duka juyowa. Baban binafa ne ya shigo. Har kasa kabir ya tsuguna ya gaisheshi. Ya amsa amma hankalinsa yana tashe. Gefen binafa ya zauna yana tambayar yaya jikin nata  da sauki suka hada baki su duka. Ya tambayi abinda yake damunta, mama tayi mashi bayanin komai, hankalinsa bai gama tashi ba saida fatima tana fisge drip din hannunta tana ihu. Jini kuwa ya dinga diga daga hannun.

Gaba dayansu sukayi kanta suna lafia. Kabir daya rude da gudunsa yayi waje, baima san wanne office bane ya shiga  dukda doctor din bai gane abinda kabir yake nufi ba, bin bayanshi yayi a rude. Doctor na shiga yace su Abba su fito daga waje, aikinsa doctor yakeyi cikin kwarewa, dakyar ya mata allura sannan ya lallasheta ta nutsu. Su Abba suka shigo.

Babu abinda binafa takeyi sai kuka tana kiran sunan abbanta. Aida sauri ya isa wajenta idonshi duk ya jiqe da hawaye yana fadin "fatima, bintu na gani  nazo, yi shiru kinji yar albarka, zaki samu sauki." Jin abbanta rike da hannunta yasa ta bude ido danta tabbatar daba mafarki takeyi ba. Ganin lallai shine yasa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, mai ratsa kahon zuciyar mai saurare. Kukan takeyi har muryarta na dishewa. "Abba ka tafi dani, karka bari kabir yazo nan inda nake, abba banason ganinsa, wallahi abba raina fita zaiyi, wayyo Allah Abba kabir ya cuceni, umma na kizo ki agajeni."
Shiru tayi tareda mikewa zaune, tana kallon Abbanta da idanunta wanda sukayi jajir dan kukan data sha. Ganin kabir yasa ta fashe da wani irin kuka "Abba ni  shikenan haka rayuwata zata kasance? Matsala daya bayan daya? Abba dan Allah kace mafarki nakeyi, Abba ka tadani daga wannan mummunan mafarkin, nasan kabir nasan halinsa, bazai mun haka ba. Wayyo ni bint..." luuu ta sulale a jikin mahaifinta sumammiya.
Tashin hankali babu wanda Abba bai gani ba a wannan lokacin, mutuwar zaune yayi, 'yarsa guda tak duniya da lahira itace take fada tsakanin rayuwa da mutuwa, inya rasata me zaiyi da rayuwar shi kuma? A cikin kanshi yakejin hayaniya, ashe doctors ne kabir ya kira, sune suke cewa a fita a fita  jiki babu kwari suka fice su duka.

Wasu zafafan hawaye ne suke zuba idonshi. Cak kukan ya tsaya yana raba idanu neman kabir, cen ya hangoshi jikin bango yana rusar kuka kamar wanda aka aikowa mutuwa. Mahaifiyarshi gefenshi alamar tana bashi hakuri
. Dubawa yayi yaga mutane sai kai kao suke a asibitin. Bin bango yayi ya sulale kasa.
A hankali ya fara addua yana rokar Allah ya bawa bintu lafia. Bangaren bintu kuwa, sunfi awa biyu sannan suka samu ta farfado, salatin annabi a bakinka, sannan ta fashe da kuka. Sunan Abbanta ta kara kira. A hankali dr. Abdallah wanda duk tausayin bintu ya rufeshi ya bude kofar ya leqo yace "Abba bintu ta tashi, tana bukatar ganinka." Kamar an zunguresu gaba daya suka mike  saidai dr yace kar a cika dakin saboda bata son hayaniya.

Abba ne kawai ya shiga dakin da saurinsa. Jikinsa har rawa yakeyi ya zauna gefen bintu tareda riko hannunta. "Yi shiru bintu, yi hakuri, gani nazo, karki kuma yin magana bintu, lafiyarki itace babban farin cikina a rayuwa. Kiyi shiru, idan kika samu sauki saiki fadamun komai kinji ko 'yar albarka?"

Gyada kai tayi tace "to nayi shiru abba, abba ka dora kaina a cinyarka, inaso naji ni a jikinka, zuciyana kamar zata fito nakeji Abba." Bisa cinyarsa ya dora kanta, yana goge mata hawayenta. Shiru tayi tana ajiyar zuciya. Sallamar kabir da mahaifiyarshi yasa gabanta faduwa, lamo ta karayi kamar mai bacci. Maman kabir ne tace 
"Alhaji, bata ci abinci bafa, ga magungunanta nan tun la'asar  ya kamata tasha su amma gashi har anyi kiran magrib"
   Abban binafa ne ya duba fuskar binafa, a hankali ya shafa kanta yace "bintu, tashi kici abinci kisha magani kinji ko?"
Bata bude ido ba tace "Abba na koshi"
A hankali ya sake cewa "kinaso ran abbanki ya baci ko?" Girgiza kai tayi hawaye na zuba daga idonta.
"To ki tashi kiyi salloli, kici abinci kisha magani, kizo kiyi kwanciyarki, saiki ji sauki, yanzun nan ma zani kira ummanki in sanar da ita, kinga gobe da safe saina biya ta gidan hajia in dauko ta muzo."
Jin an ambaci ummanta yasa ta zabura ta mike zaune "Abba da gaske zakazo da umma?"
"Zanizo da ita, amma saikin yi duk abinda na lissafa miki."
Cikin murna tana goge hawayenta tace "wallahi zanici abincin ma abba, kuma da yawa zanici ma"
Mikewa tayi , ko inda kabir yake bata kalla ba ta shiga toilet dinda ke manne da dakin. Saida ta watsa ruwa sannan ta fara alwala, tsayawa tayi gaban mirror tana kallon kanta, a hankali hawaye wani nabin wani ya dinga diga daga idonta. Take abinda ya faru dazun ya dinga dawo mata kamar lokacin yake aukuwa. Kanta wani irin sarawa yayi, tayi saurin rumtse ido tana salati tareda dafe kanta.

Da sauri ta bude kofar ta fito, ganin babu kowa dakin sai maman kabir, tasan sun tafi sallah, tunda tana wanka aka kiraa. Zaunawa tayi tana jiran mama ta gama sallah, dan ita ko kallabi bata dashi. Tunani mai zurfi ta shiga, har mama ta gama bata farga ba saidai ji tayi an dafa ta, a dan firgice kadan ta kalli mama, murmushinda yafi kama da yake tayi ta karbi hijab dinda ta miko mata, sakawa tayi tareda hawan sallaya ta dubi gabas ta kabbara sallah. saida ta rama sallolinta sannan tayi magrib. Ta shiga adduoi tareda neman mafita daga ubangiji. Saida aka kira isha, tayi sallah, tareda shafa'i da wutr da suka zamar mata kamar dole sannan ta mike. Mikawa mama hijabin tayi. Har zata kwanta, saita tuno da zataci abinci tasha magani. Kuma harga Allah tanajin yunwar daman, ganin kabir ne yasa tace ta koshi. Saukowa tayi kasa ta zauna tana dudduba abinda aka siyo. Bataji tanason komai ba. Ledar fruits ta bude, aiko ta sha fruits din sosai. Saida taji dai-dai sannan ta dauko ledar magani. Saukinta ko wanne da yamda za'a sashi a rubuce. Ta balla tasha. Har lokacin mama bata gama sallah ba. Hawa gadon tayi ta kwanta. Ai kamar karta sha maganin nan, kanta kamar ana daka a ciki haka yake bugawa. Rike kan tayi tana salati a hankali. Nan da nan zazzabi mai zafi ya rufeta.

Wajen tara su abba suka shigo, tareda da doctor a biye dasu, dukunkune yaga binafa, ga mama na jero mata sannu. Zama yayi ta gefen gadon yana tambayar meke faruwa, mama tace zazzabi ne. Doctor ne ya dubata. Cewa yayi maganin data sha ne yake reacting amma nan da 3hours zata dawo dai-dai. Binafa wacce ke bacci bata san me akeyi ba abba yaketa jerowa sannu. Numfashinta nanan yanda yake sama-sama, bugun zuciyarta ma yayi sauti mai karfi. Abba yace wa kabir yaje gida ya dauko musu kaya, sannan ya ajiye mama gida, kafin gobe asan wa zaina zama da ita. Mama tayi fir tace

"Haba alhaji, baka ji jikin wannan bakwar Allah bane, ciwo irin wannan saida babba a kusa, gashi wata lalurar inta tashi sai mace. Kuje dai gaskia ni zani zauna, kabir yaje gida ya dauko mun kaya koda zuwa safe ne, amma yanzu yaje ya kawowa yarinyar nan maya, da hijabi, harda kallabi. Bai halatta matar aure tabar gashi bude ba, kowa na shigowa. Amma Alhaji ka fadawa umman nata, tunda naga dazun har murna takeyi."

"Toh shikenan, bari muje  daren yana karayi, Allah tashemu lafia, ya bata lafiya itama"

Amin kowa ya amsa. Sai wajen sha daya saura kabir ya dawo da kayan binafa. Yayi-yayi da mama shi zaya kwana. Tace ya tashi ya wuce karya bata mata rai. Fita yayi ya dauko karamar katifar dayazo da ita, ya kawo wa mama, sannan ya musu saida safe.
Mama ta shimfada. Ta saya kofar dakin. Sannan ta kwanta. Ga gajia ga dare yayi. Tuni bacci yayi awon gaba da ita.

Asuba ta gari mama❤

Yeey guys💃❤  its second chapter. Enjoy💋

Please dont forget to
Vote
Share
And comment
Thank you❤

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now