Written by khaair
"A'ah mallam Abu lafia?"
Fadar baban Aunty Bilkisu da suke zaune kalkashin bishiya shida sauran dattijan unguwa.
Ganin an fido da Aunty Bilkisu daga mota ga yanda Aunty take kyalkyalar daria gata kuma daure da igiya.
Abba da shima ba cikin hankalinsa yake ba sosai yace"Babu lafia mallam"
Aida sauri dukansu suka iso wurin suna sallallami dan kuwa abin ana gani anga hauka.
Mallam ya kama aka shige da Aunty bilkisu gida dan kuwa har yaran unguwa sun fara taruwa wajen.Itama mahaifiyar Aunty bilkisu inna larai tana bakace shinkafa taji shigiwarsu.
Ba shiri ta saki farantin shinkafar ta taso tana lafia.
Kanwar Aunty bilkisu ma data zo ganin gida ta fito daga daki tana tambaya"Inna lafia... "
Bakinta bai rufe ba tayi tozali dasu Aunty bilkisu data tokare taki shigowa tana faman fadan aini na rabasu.
Dakyar aka shigo da ita. Inna ta shimfida tabarma suka zauna. Kowa yayi zuru.
Abba tsananin bacin rai ya kasa ko gaishe da surukan nasa, kuma ya kasa amsa nasu gaisuwar.Ya Aliyu ne kawai yayi ta mazan iya gaishesu.
Mallam ya tambayesa ko lafia, ga kuma yanayin daya ga Aunty bilkisu."Baba gaskia ba lafia ba... Kaji, kaji"
Tun abinda ya faru shekera da shekaru duk ya kwashe ya fada musu. Har zuwansu zaria da komai daya faru yau.
Inna larai saita saki kuka. Mallam kuwa salati kawai yakeyi. Itama kanwar Aunty bilkisun kuka ta saki.
"Yanzu balki da tsufanki bakiyi wayau ba, ashe halinki nanan, kinyi asara. Nayi nadamar haihuwarki, ina nadama da kirana baba da kikeyi. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu gashi kinja mana kinja wa kanki kinja wa dukan danginmu abin magana"
Shima saiya fara kukan.
Abba shima nashi hawayen ya goge ya mike tsaye yace"Mallam kayi hakuri dan Allah, amma ba zani iya cigaba da zama da maigado ba, na saketa saki uku."
Yana kaiwa nan ya fice daga gidan. Ya Aliyu ma ya mara masa baya.
Yana shiga motar Abba yajata.
Bai tsaya ko ina ba sai gidan inna.Yana tsayawa ya bude ko key bai cire ba ya fito.
Harda sassarfa ya shiga gidan. Inna na zaune bisan carpet dinda umma ta shimfida mata kafin ta fita, tana gyaran goro.Bayan sallamar da Abba yayi kasa komai yayi saidai faduwa da yayi zaune jigib a gaban inna.
Inna da bata lura dashi ba, ba karamin tsoro taji ba ta dago da sauri.
"Amma dai habu bakada hankali ko? Ya zaka shigo gida babu sallama babu gaisuwa saidai mutum zani gani a gabana kamar wanda aka jefo"
Wani kuka mai karfi ya kwacewa Abba, baisan lokacinda ya dora kansa a cinyar inna ba yana rusar kuka.
Hankalin Inna ba karamin tashi yayi ba. Mutum a wannan shekarun nasa inhar zaiyi kuka ba karamin abu bane ya faru ba.
Bata fara kawo komai ba a ranta sai Bintu ta rasu, dan bayan kanshi, Abba babu wanda yake kauna makamancin yanda yake kaunar fatima.
Itace rabin ransa.
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...