💫🌼fourtyOne🌼💫

2.8K 149 0
                                    

Written by khaair

Ranar lahadi suka isa katsina. Basu tsaya ko ina ba sai gida. Saida suka sauke kayansu duk sannan fa suka shiryasu. Dan babu wata gajiya jikinsu sun huta a Abuja.
Saida suka kimtsa ko ina sannan fatima tadan share ko ina, Aliyu na tayata goge abubuwan da zai iya. Saboda tausayin yanda jikinta yayi kumburi ga cikinta ma ya girma.

Basu gama gyaran kaya ba saida akayi magrib. Bayan su Aliyu sun wuce masallaci fatima ta duba abinda keda akwai gidan.
A fridge din babu komai,  dan kafin su tafi ta cire komai daga ciki takai ma umma gudun karsu lalace.
Dan haka, saita shiga wanka.

Bayan su Aliyu sun dawo daga isha'i tace ana bukatar cefane. Shafa kai yayi yace

"Babe bari dai mu fita mu siyo wani abin. Bansan inda zani sami cefane ba yanzu da daren nan"

"Toh"

Tace dan itama ta gaji din. Batason ta zauna ne, dan bazata iya tashi ba.

Junior jin babanshi zaya fita yakuwa hau tsalle

"Appah nima sai inaje wallai"

Aliyu dariya yayi. Dan junior dariya yake bashi idan yana hausa. Yanda kasan wani gwari. Indai kanaso hausanshi ya fito narai narai, toh saiya hada da english.
Har godewa Allah yake da suka dawo gida. Zaya hadu da yara nan harshensa ya karye sosai.
Dan fatima kullum fadanta ace yaro dan hausawa gaba da baya baya iya yaren hausa na minti uku ma. Amma turanci daga nan har london zaiyi shi.
Dan ji yana ji, amma yayi hausar da bakinsa shine aikin.

"To ka iskeni a mota"

Bai jira Aliyu ya gama ba ya zari takalmansa da fatima ta fiddo mishi yabi babanshi.

Restaurant yayi musu order, amma a sa musu a take-away.
Babu jimawa suka fito. Junior yahau rigiman

"Appah insha ice cream"

"Junior kaganka kaida ice cream dinnan ko?"

Murmura ido yahau yi alamun tausayin nan ya kuma hada hannunsa biyu yace

"Please Appah, please, please"

Dariya Aliyu yayi yace

"Toh naji, yanzu sanya seat belt dinka"

Seat belt yaja ya saka. Sannan ya kura ma titin ido suna tafia. Shidai ganin garin yakeyi kawai.

A oasis&bakery suka tsaya. A tare suka shiga. Junior ya zabi flavour dinda yakeso, Aliyu ya dibar wa kanshi da fatima suka diba wasu abubuwan daban sannan suka tafi gida.

Har fatima ta fara gyangyadi suka kwakwasa mata. Tashi tayi ta bude tace

"Shine kukaje kuka dade ko"

Bare hug ya mata yace

"Sorry babe, wallahi kinga wanda ya tsayar damu wai ice cream"

Kallon junior tayi da harya shige cikin gidan tace

"Aikin daniel ne, kullum saiya kaishi sunsha ice cream. Gashi abu ya zamar mishi kamar gado"

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now