Written by khaair
Karfe biyar doctor ta duba fatima. Ta sallamesu.
Babu bata lokaci Aliyu ya shiryata suka fido daga asibitin.
Tana rike da babyn, shi kuma yana rike da kayan.
Mutane sai congrats ake mashi. shikam bakinshi yaki rufewa.Koda suka isa gidan umma, cike yake kam da mutane. Har rububin daukar yaron akeyi. Aliyu yana cewa su bishi a hankali.
Itadai fatima shigewa daki tayi tana tube kayan jikinta, dan umma tace taje a mata wanka. Da towel ta fito ta iske umma a kewaye.
Umma da kanta ta nuna mata yanda ake wankan.
Dukda fatima tana jin zafin ruwan, haka tayita daurewa tana yinshi.
Ga kuma ruwan bagaruwa da take tsuguno dashi.
Saida tayi sabi uku ta tabbatar data gasu sannan umma ta kyaleta. Ita kuma tasa soap da sponge tayi wanka ta fito.
A daki kuwa har Aliyu ya fiddo mata kayan sawarta.
Murmushi ta mishi. Da kanshi ya tayata shiryawa bayan ya rufe kofar kar wani ya shigo. Saida ta gama tsaf sannan ta kwanta. Kafin Aliyu ya farga harta fara sharar bacci. Baccin gajiya da wahala. Dariya yayi ya fito.
Ya iske anawa boy dinshi wanka yanata tsanyara kuka. Yayi zaune yana kallon yanda akeyi. Bayan da aka gama akazo ana gasa cibinshi.
Yanda yake lumshe ido alamun abin na mishi dadi saiya bawa Aliyu dariyaUmma tace
"Kai wallahi ka tashi kabar gidan nan, ko kunya bakaji kayi zaune cikin mata?"Dariya yayi yace
"Umma jira fa nake ki gama masa wankan na fita dashi"
Aiba shiri umma ta dauki wani bulala zata tsala mishi, da sauri ya tashi ya fice gidan yana sharar dariya.
***
Haka akayi ta wankan jego.
Tun umma na hana Aliyu harta gaji ta kyaleshi. Fatima kam ba irin kulawar da bata samu. Sosai takejin dadin zamanta. Gashi yanda Aliyu yake kara ji da ita. Umma ma. Abba kam kullum saiya zo ganin jikanshi. Mummy ma tana zuwa. Sadiya kam gidan ta tare yanzu. Da yaran kawu ishaq suma suna zuwa Aunty bintu ta haifar masu baby.Ana kwana na biyu, Asiya tazo ganin baby.
Yau kam saida tayi kuka da idonta ganin babyn.
Ga yanda fatima ta kara murJewa. Ba zaka taba cewa ita bace.Sai dare Aliyu yazo daukarta, duk ta gaji da zaman gidan.
***
Ranar daren suna Aliyu ya kawo kaya akwati set guda biyu da kit na baby ne. Akwati biyu kuma manya na maman baby ne. Sai kuma wani jaka daban, dinkakkun kaya ne na fitar suna kala goma sha biyar, duk na maman baby, sai kuma kayan shafa na baby da mamanshi. Sannan kuma ya kawo katon Sa guda daya da rago manya guda biyu.Lokacinda aka bude kayan. Saida kowa ya sarawa Aliyu. Dan kayane uban ubansu. Dakakku, kuma na gani a fada.
Fatima tayi godiya sosai ta kuma jinjina.Washe gari. Tunda asuba Aliyu yayi wa yaronshi huduba ya sanar a masallaci yaci suna muktar. In memory of his late twin brother.
Aka ce Allah raya muktar Allah yasa hafizi ne, ya rayu cikin tafarki da koyawar addinin musulunci.
Akace amiiiin. Suka rarraba goro da alewa aka tashi.A cen gida kuwa aka fara shirye shirye. Tunda Asuba fatima bata samu damar komawa bacci ba. Dan hidindimun da akeyi gidan. Ita har mamaki takeyi kamar yau aka fara haihuwa cikin jikoki. Kodan an dade ba'a haihu ba, kuma Aliyu ne namijin farko daya fara haihuwa.
Tun karfe bakwai masu yankan rago sukazo. Babu bata lokaci suka yanke su duka. Aka shiga fida.
Umma kuwa da mutanenta sunata hidimarsu. Karfe takwas masu saka rumfa sukazo suka shiga daurawa.
Umma ta shiga amsar baby daga fatima, ta iske sai kuka take.
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...