Written by khaair
Da maraice fatima na kwance parlour ta shafa zuma a fuskarta bayan tasha paracetamol. Dan sam batajin dadin jikinta. Kamar ma fever na neman kamata.
Tananan kwance taji dirar mota, tasan ba Aliyu bane ba, dan yau lahadi, yana gida, ya fita waje zagayawa amma bada mota ba. Baya fita saidai idan wani emergency ne ya taso asibiti.
Lekawa tayi ta window. Aunty jamila da sadiya ta gani sun fito. Har tsallen murna saida tayi. Koba komai zata rage kewa. Sashen Asiya suka fara shiga. Basu wuce minti biyar ba suka shigo wajen fatima.
Da gudu ta rungumesu tana oyoyo oyoyo. Aunty jamila tace"Ohni bintu ba'a girma ba dai har yau"
Dariya tayi tareda dan turo baki tace
"Aunty wallahi naji dadin ganinku ne"
Zama sukayi. Aiko ta shiga jero musu kayan motsa baki, da abun sha. Sadiya ta sauko kasa, ita dambun naman ma ta dinga hambala tace
"Kaaai, gaskia bintu dole ki zubamun wannan dambun naje dashi gida. Kai gaskia yayi dadi. Kamar da zuma naji ciki. "
"Sarkin santi kenan, Abba ya aikomun dashi ni tun last month, banma taba zaunawa naci shi ba. Bari zani zuba muku kuje dashi."
"Dakin kyauta mana, dan yayi dadi sosai"
Hira suke tayi. Aunty jamila ta saki jiki dasu kamar ba wacce ta isa haihuwarsu ba, dan itace babbar jikar Inna, kuma babbar diya a dangi. Yaranta yanzu har akwai wacce tayi waec. Asali kuwa nan so takeyi ta gano damuwar fatima.
"Wai shin ni wannan ramar da kikeyi bintu, ta lafia ce koko dai kanina yayi ajiya?
"Laaaaa, Aunty wannan zolaya haka, ni banada komai, ina zani samoshi ma, kilan dai Asiya ta samu"
Ta fada tareda rufe ido
"Ah toh, naga kin rame da yawa, kuma in Asiya zata samu, mai zai hana kema ki samu . Koda matsala ne dai"
Fadar aunty jamila tareda kafe fatima da ido
Murmushin karfin hali fatima tayi tareda wasa da zobenta na hannu da muktar ya bada tace
"Ai Aunty komai lokaci ne. In lokaci yayi ai sai a samu"
Zama Aunty jamila tayi kasa gefen bintu ta kalli sadiya tace
"Ke acici, shiga wajen Asiya ki bamu wuri zamuyi magana"
Bubbuga kafa sadiya tayi tana tura baki
"Ni kullum in za'ayi magana sai ace na tashi, bintu dinma ai karama ce"
"Kiyi zuciya ki fiddo miji, kin tsaya shiririta, bansan mi kike jira ba"
Tura baki tayi ta fice tana kunkuni. Aunty jamila ta juyo ga fatima tace
"Yauwa, daman zuwa nayi muyi magana kina jina bintu? Karki daukeni a matsayin yayar mijinki, kinga dai nan ni yayarki ce, Zan zame miki tamkar uwa, tunda wani abin dole bazaki iya fadawa umma ba, keda Aliyu din duk nata ne, kuma ni bazani zauna ana cin zalin ki ba, ki fadamun yanayin zamanku anan gidan sai muga yanda zamu taro bakin zaren"
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
Roman d'amourFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...