Written by khaair
Hidindimu akeyi bana wasa ba. An hada shagulgula har uku. Muktar shiya hada brothers night, sannan tareda jagorar Asiya suka hada sisters eve.
Yayye manya kuma su suka hada dinner.Sosai hidindimu sun kankama. Wanda yanzu har fatima ta kashe wayarta ta ajiye a bisa umarnin Umma.
Duk wannan shagulgula da akeyi bada sanin Aliyu ba.
Dan kuwa daman da fatima yake waya. In sun gaisa idan Abba nanan ta bashi su gaisa. Toh yanzun din itama ta kashe waya. Ganin hakan ne ya fara neman hutu, dan sosai yana kewar gida, koda sati uku yazo yayi ya koma.Kabir ma ba'a barsa baya ba, dan kuwa ya kawo gudunmuwarsa sosai. Kuma Abba yayi murna, dan kabir din ya fawwalawa Allah komai. Cikin iv din da aka bashi. Hada kawunninsa akace ya kaiwa, in sun samu dama suma halitta daurin auren.
Da kuma IV din yinin biki da mommy ta bada a bawa maman kabir din. Dan kuwa cewarsu duk an zama guda yanzu.
Biki ana saura kwana uku a fara, muktar ya yanke shawarar zuwa gidan umma ganin amaryarsa.
Dan ya jima baisata a ido ba, saidai hoto.A waya ya kira umma ya sanar da ita da zuwanshi.
Ta shiga dakin Inna inda fatima take kwance tace"Bintu ki tashi ki shirya ga muktar nan zuwa, kuma ki girka masa wani abun."
"Umma ni saina wani shirya yanzu. Kuma abincin basai yaci wanda kika girka ba"
"Ke banason shirme kinaji. Yaushe na fara magana kina mun musu. Tashi maza nace"
Tashi tayi da sauri tace
"Kiyi hakuri umma"
Kitchen ta shiga ta rasa me zata dafa mishi. Sai lokacin ta tuno yanda muktar yakeson indomie mai attarugu da albasa. Murmushi tayi ta dora ruwan. Ta jajjaga attaruhu ta yanka albasa. Ta zuba. Yana tafasa ta zuba indomie din. Saida ya dahu ya kusan idarwa ta bude sardines ta juye tana dode hanci dan kuwa batason karnin kifi sam.
Minti uku ta bashi ta sauku tukunyar.
Kwai hudu ta fasa ta zuba albasa da tarugu kadan ciki da barbada gishiri kadan.
Bata kada ba ta juye a frying pan ta soya.
Karamin cooler ta samu ta juye indomie a ciki ta kanga kwai daga gefe.
Sannan ta dauko kankana ta fere shi tas tareda cire 'ya'yan. Ta dauko ayaba da abarba suma ta fere su. Sannan gwanda shima ta fere tareda yankawa.
Dubawa tayi koda akwai kwa-kwa dan kuwa baka raba gidan umma da kwakwa. Cikin sa'a ta samu kuwa a fridge an fasheta ma. Daukowa tayi ta gurje shi da grater.
Sannan ta dauki kankanar da ayaba da gwanda ta yankasu kanana ta zuba a blender. Da ruwa kadan ta markade su. Saida suka markadu sannan ta kashe.
Ta samu mataci ta tace ruwan cikin jug. Ta dauki abarbar ta yanka kanana kanana sosai ta zuba a sama. Sannan ta dauko kwa-kwar ta zuba shima. Bata saka sugar ba, danshi ko tea zaisha sugar tea spoon rabi yake sawa kuma baya motsawa.
A fridge ta girka. Sannan ta gyara wurin ta abubuwan data bata. Ta koma daki.
Wanka tayi.
Bayan ta fito tayi tsaye jikin wardrobe ta rasa kayan da zata saka. Hakanan ta tsinci kanta da dauko wasu riga da skirt da umma ta dinka mata. Bata taba sakasu ba. Saida ta fara gyara fuskarta da gashinta ta kullum cikin gyara da kamshi yake.
Yaune rana ta farko da ta fara sha'awar yin kwalliya har ta taba shafa jan baki.
Kuma ba karamin kyau ya mata ba. Ta gyara fuskarta sosai.
Ta dauko kayan ta sanya. Tsam suka mata, dan ba karamin gyara takesha a wajen hajia maigado ba. Ita kanta saida tasan tayi kyau. Taje gaban mirror ta daura dan kwalin kayan. Bata bukatar turare, dan daman ba shafawa takeyi ba. Kuma gashi ruwan da take wanka dashi yanzu ko wanne kamshi sukeyi.
Tana cikin daura kallabin ne muktar yayi sallama. Duk tabi ta dabarbarce. A sauri sauri ta daura ta mike.
Duk gabanta faduwa yakeyi. Ta fara tunanin to yaya ma za'ayi ta fita wajen ya muktar a haka. Anya. Gaskia bata iyawa.
Cenza kayan zatayi ma ita. Haka tayi ta sake-sake harta ji sallamar umma. Da sauri ta mike tace"Umma ni kunya nake ji, bana iya fita haka, jifa yanda kayan suka matseni"
"A'a basu matseki ba, sun miki dai-dai. Kuma kinyi kyau sosai, muktar mijinda zaki aura ne, kuma dan uwanki. Dole kija ra'ayinsa.
Bawai ta wata mummunar hanya ba a'a, ta hanyar shigarki, kwalliyarki, iya maganarki da kuma uwa uba girki. Kinga karkiyi shigar banza, kamar yanzu kin fito a dai-dai, ki saka mayafi kije, sannan gashi kinyi kwalliya wacce inada imanin zata ja ra'ayinsa dan baki taba irinta ba, nasan ki kuma da fahmin kalami, ba zani samu matsala dake a wannan fannin da.
Girki ma nasan kin iya, saidai ki kara kaimi, sai kuma iya tafia.
Akwai tafiya iri da dama wacce sai a gaban miji ake yinsu. Shine zasu kara janyo ra'ayinsa a kanki yaji ba wata mace dake birgesa saike. Yanzu kije wajenshi. Yana parlour, idan kin dawo, zamu cigaba daga inda muka dora. Allah miki albarka."A kunyance tace.
"Amin umma, kema Allah biyaki da gidan Aljanna, dan a kullum kina kara ilimantar dani akan abubuwan da ban sani ba.
Nagode kwarai, nagode wa Allah da samun uwa ta gari. Allah sa kowacce uwa mace ta zama haka"Murmushi umma tayi. Itama ta mayar mata da murmushi.
Tareda daukar mayafi karami ta yana a jikinta ta fita.
Tafi minti biyar a wajen ta rasa yanda zatayi ta shiga dakin. Ita ba komai takeji ba, sai dan kar muktar yaga kamar sonshi take, tunda har ta tsaya tayi kwalliya.
Ga girki ta dafa mishi abinda yafi so. Anya ita ba komawa zatayi ba ta cenza kayan. Nan kuma sai maganar umma ta dawo mata.
Duk ta rasa yanda zatayi. Ga kunya, gashi tana jin nauyin muktar. Shi kuwa tunda tazo bakin kofar ya ganta. Tuni ya manta kansa, sai kallonta yake. Dan kuwa bata taba irin kyaun ta tayi yauba.
Karamin bakinta ya kalla, wanda yasha jan janbaki. Daga sama har kasa yake kallon halittar ubangiji. Sai godiya yakewa Allah daya bashi fatima. Adduarsa kawai Allah ya ida nufi a shafa fatiha ta zama tasa baki daya.
A hankali ya furta"Masha Allah"...
Khaair❤
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
Roman d'amourFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...