💫🌼fourtysix🌼💫

2.7K 166 2
                                    

Written by khaair




Tun lokacinda yazid ya barta anan kwance, bata kara motsin kirki ba sai gabacin asuba da sanyi ya fara dukanta.

Bude ido tayi a hankali. Take kanta ya mummunan sarawa. Ta daga hannu dakyar ta dafe kan tare da sakin kuka.

Kiri kiri ta kasa motsa jikinta, dan yanda take jinsa ma uwa ba nata ba. Ganin haka yasa tayi kwance a wurin tanajin yanda sanyi ke ratsa duk wani sashi na jikinta amma sam ta kasa tabuka komai. Tuni baccin wahala yayi awon gaba da ita.

Wajajen karfe goma sai taji alamun mutane ga kuma hayaniya sama-sama.
A hankali ta bude ido tayi tozali da dandazon mutane, wasu na kallo, wasu na magana kasa-kasa, wasu kuma suna daukarta hoto.

(Mutane muji tsoron Allah, zamani yazo mana da wani salo na rashin taimako, komi yanzu sai an dauka hoto anyi video dan ayi posting online, waya ta zama jigo a rayuwarmu da bamu tsayawa mu duba illarta a garemu. Lokacinda mutum yake bukatar taimakonka, lokacin ne zaka fiddo waya kana dauka hoto da video dan kayi posting twitter, snapchat ko instagram da kuma sauransu. Kai yanzu abun har gidan mutuwa, kaga ana daukar gawa hoto, idan anje makabarta rufeta a dauka hoto, idan an rufe a dauka hoto, sai kaga an tashi anyi picmix. Allah yasa mu gane)

Rufe idonta tayi ta kara budewa danta tabbatar ba mafarki take ba. Ganin sunanan yasa ta daga hannu dakyar tace

"Help me please"

Jin haka yasa wasu suka fara baya baya, wasu kuma na tafia. Wasu kuwa video din sukeyi, babu wanda yayi yunkurin taimakonta.

Sunanan, ALLAH ya kawo wani babban mutum wucewa, harya wuce, yace driver ya maido shi yaga dandazon me akayi anan, yanzu haka hatsari akayi kuma babu wanda zaiyi niyyar kai mutanen asibiti.

Ba musu driver yayo reverse. Daidai wajen sukayi parking. Ya bude ya fito. Mutanen suka bude masa ya shigo.

Da sauri yace

"Subhanallahi, meya sameta haka"

Wani christian dake wajen yace

"We just saw her lying here o"

"Then why didnt you take her to the hospital"

"Ahh, alhaji, in this boko haram season, who will help such kind of people"

"Why are you people so heartless, a human being like you is dying and you guys are not doing anything to help her, yet you stand here video taping her"

Ya juyo ga driver dinshi yace

"Lati, dan ALLAH kama kasata mota mu kaita asibiti, gaskia mutane muna neman gyara"

Aifa nan da nan mutanen wajen suka yi masa caaa, wai dan fillan kanu ne zaya fake da taimako ya tafi da ita.

Juyowa yayi garesu yace

"If i wanted hurting her. I would've waited till you all are gone, and i will carry her without any of you seeing. I'm not heartless like you. You call yourselves the children of God, ku kuma kuna kiran kanku hausawa, musulmai, yet you cannot help a common poor girl. Shame on all of you"

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now