💫🌼FourtyTwo🌼💫

2.9K 180 0
                                    

Written by khaair

Bayan sati uku



Wannan karon fatima cewa tayi ba zatayi taron suna ba. Su umma sukace tayi hakuri tayi. Ai abun kwana guda ne. Bada son ranta ba ta amince.

Jikinta kuma alhamdulillah, da sauki sosai. Baby ma yanashan kula ta ko ina. Junior kuwa da akace baby brother dinshi ne, saifa aka rasa zaune, sai rawar kai. Ya saka shi gaba yayita lagudar hancinsa ko hannunsa da tiny legs dinshi. Sai Aliyu ya koreshi sannan.
Alhamdulillahi itama jikin fatima ya murnure saidai avinda ba za'a rasa ba.

______________________

A bangaren Asiya ma, likafa tayi gaba, sune hot babes in town, sai wane da wance daukarsu. Kuma har gobe yazid dinta nanan suna sha'aninsu babu ragowa. Dan in yazo gari ma wajenshi take komawa gaba daya saiya koma sannan itama ta koma ga harkarta. Yanzu ma ta rage bin mazajen daman dan kudi takeyi, kuma yanzu suma zauna mata, ci da sha saita ture. Har dalleliyar mota ta d
Siyo tana fantamawa itama cikin kawaye.

*___________*___________*

Suna yayi anci ansha an kuma batse.
Yaro yaci suna Muhammad Jawad. To Allah ya raya muhammad a bisa tafarkin addinin musulunci.
Amin.
Itama fatima tuni an sallameta daga asibiti tana gida yanzu.
Baba delu ma nanan tana ingozuma.

***

Kwanaki kenan, sunja sosai. Kuma rayuwa sai handala, abubuwa komai na tafiya dai dai, sai abinda ba za'a rasa ba.
Jawad yanzu watansa biyar, yaro kyakkyawa kamar iyayensa, yayi bulbul dashi abinshi.
Junior ma karatunsa Alhamdulillah. Akwai kwalwa kamar mamarshi. Kullum cikin prizes da yabo yake. Competition ma akwai wacce sukayi ta local yazo number one a katsina. Aka tafi dasu har lagos yazo 3rd. Suka bashi scholarship turkish.
Aliyu yace bayaso yayi nisa. Hakan yasa suka biya mishi full time school fees, tun daga primary 3 har ya gama ss3.

Aliyu ma ya koma bakin aikinsa yanzu. Dukda yanzu babba ne sosai a asibitin. Sai an nemeshi yake zuwa yanzu.
Ganin zaman gida na neman sashi kiba dan fatima kullum cikin tsokanarsa take yayi katon ciki
Shiyasa ya fara neman abinda zaiyi keeping dinsa busy. A takaice ya fara kasuwanci. Babu wuya, a hankali abubuwa suka dinga bunkasa. Kudi suna shigo masa ta ko ina. Rayuwarsu dai sai godiya. Basuda wata matsala

_____________________

Ranar wata juma'a, fatima ta gama shirya jawad cikin kayan baccinsa. Saiga Aliyu ya shigo. Gadon ya haye tareda ware hannuwansa, da sauri da shige jikinshi.

"Zarah na kinji nauyinda kika kara"

Dariya tayi tareda dagashi tana gyara guntuwar rigarta data dage

"Toh i'm a mother of two fa. Dole ai"

"Just a mother of two kina wannan rakin, keda yanzu kinada sauran takwas a gabanki"

Ware ido tayi tace

"Kam. Lallai ma ya Aliyu. Ba saidai na hakura da auren ba. Ina zani iya. Koda boys dina aka barni ai sun isheni"

Dariya yayi sosai

"Allah shirye ki wallahi, saima ki hakura da auren. Baby nikam boys dinnan basu isheni ba, i need a baby girl."

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now