💫🌼Fourty🌼💫

3.3K 178 4
                                    

Written by khaair



Bayan satika

Babu wuya wajen ubangiji. Dan kuwa yanzu bikin sadiya ya kankama. Hidindimu akeyi bana wasa ba. Yara sun nuna gwaninta, dan sun hana iyeyensu duk wata dawainiya sun dauke komai.

Tun daga kayan daki, abinda yayi gara, gudunmawa, da kudin kayan abinci na fitar biki, kayan sakawar amarya kowa da wanda ya dauka. Wanda Aliyu aka dorama dawainiyar kayan gara.
Fatima tayi tsaye kuwa wajen a siya masu yawa. Wanda komai buhu biyar biyar Aliyu ya siya. Kwalaye ma nasu taliya, macaroni, cous-cous dadai sauransu sune shida shida. Man gyada abinda yayi manja suma ko wanne jerry can biyu biyu.
An yaba sosai da kayan. Aka ajiye su tsab aka shiga hidimar biki.

Fatima an zama Amara kirjin biki,  ba'a nan ba'a nan. Ta shiga ta fita dai. Junior yama koma dan gidan mummy dan fatima batada lokaci sosai.
Aliyu ma sai dare yake sata ido.
Yanzu ma yau kunshi akeyi. Amma suna salon wajen gyaran gashin sadiya.
Da yake bama wani gashi ne da ita ba. Shiyasa bai dauki lokaci ba aka gyara tas. Itama fatima aka gyara nata.
Daganan fa suka wuce wajen siyen wasu kaya. Sai karfe bakwai na magriba suka shigo gida.
Lokacin an gamawa kowa kunshi. Aunty hauwa ma an gama mata. Nan fatima ta tsaya sukayi sallah. Ta zauna aka fara zizara mata nata. Ana fara kunshin kenan sai Aliyu ya kira, wai tazo shi kadai gida. Tace nanda 30minutes zata zo.
Kona kafar bata bari akayi mata ba tace zatayi a gida.
Saida ta bari ya dan sha iska sannan fa ta wuce. Ta biya gidan mummy ta dauki junior sannan ta wuce gida.

Washe gari kuma aka sha wa'azi. Wanda suka gayyaci sheik kabir gombe.
Amma kasancewar aiyuka da kuma hidima bai samu zuwa ba. Saiya saka abokinsa ya wakilce sa wato sheik yakubu musa.
Inda yayi waazi sosai, na zamantakewar aure, zamantakewar rayuwa da kuma mutuwa ita kanta.
Maganganunsa sun girgiza mutane sosai. Dan haka har aka tashi kowa jikinsa yayi sanyi.
Dan kowa da irin sakar da yake a cikin ranshi.
(Allah yasa mu dace)

Anci fa ansha an batse. An bada. Akayiwa mallam godiya sosai ya tafi.

Washe gari akayi wankin amarya. Wanda yanzu zamani wai mutane suke kira da bridal shower. A zamanin da, iyaye ne zasu zo, ayiwa amarya wanka da ruwan lalle. Sannan a yayyabeta da lallen kanshi. Lokacinda za'a gama, amarya zata fito jawur da ita Zar kyau.
Amma wai zamani ya kawomu da wai za'ace bridal shower amma kida ne kawai za'a saka, amarya da kawayenta su chashe, sai aci cake a yanka aci abubuwa a tafi.

Shima ango a nashi bangaren gidansu anyi wankan ango. Duk dadai shi a gefen fuska kawai aka shasshafa masa,  sai hannu da kafa shikenan.

Washe gari akayi kamu.
Mutane dason bidi'a yaukam mutane danqam cikin wajen da akayi.
Yaukam amarya tasha ado sai kace bebin roba.
Fatima ma ba'a barta baya ba. Tasha adonta itada mijinta da yaronta. Sai kamshi suke zabgawa. Dasun gitta sai an kallesu. Anci shima ansha anyi hotuna.
Karfe goma aka watse. Kowa ya koma muhallinsa dan huce gajia.

Washe gari ne akayi mothers night.  fatima bata samu zuwa ba, dan junior ya tashi da zazzabi. Dukda Aliyu yace taje zaya kula dashi amma sai ta kasa tafiya. Dan yanda taji jikin junior ya matukar tada hankalinta.
Har kuka saida tayi dan yaro mai kazar kazar da kwaramniya shine yau ya kasa koda daga ido sosai.

Sai bayan cen tsakar dare jikin ya fada. Fatima harta fara bacci taji yana bubbugata.

"Ammah ansha  wuwa"

Da sauri ta tashi ta zuba mishi daga cikin jug din dake bisa bedside drawer.
Karba yayi ya shanye. Ta ajiye cup din ta dawo kusa dashi ta zauna. Tace

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now