💫🌼ThirtyTwo🌼💫

3.9K 173 2
                                    

Written by khaair

Da asuba fatima ta riga Aliyu tashi. A kunyace ta tashi yanda taganta matse jikin Aliyu. A hankali ta zare ĵikinta dan karta tasheshi.

Dakinta ta wuce.
Saida tayi wanka ta tsarkake jikinta sannan tayi nafila tayi sallarta da addua.
Tanajin lokacin fitar Aliyu masallaci. Karatu ta farayi. Saida taga haske ya bullo sannan ta tashi ta shiga kitchen.
Abinci marar nauyi ta hada ta jera a dinning table.

Ta koma dakinta tayi wanka ta shirya. Tara saura Aliyu ya fito. Dakinta ya shiga ya iske tana gyaran gadonta.
Amsa sallamarshi tayi tana gaisheshi amma kanta a sunkuye. Murmushi yayi ya amsa yace

"Kin tashi lafia"

Gyada kai kawai tayi. Fita yayi tabi bayanshi.
Ta hada mashi kalaci. Shikam ci yakeyi, amma kallonta kawai yakeyi. Ita kuwa kasa cin komai tayi dan shanyayyun idanunsa sun tsareta.
Harya gama juya cokali kawai takeyi. Mikewa yayi ya wanke bakinsa yace

"Ni zani wuce, kinada wani sako?"

Girgiza masa kai tayi ta mika masa kayan aikinshi da labcoat dinda ta goge masa sai zabga kamshi take. Karba yayi yace ya gode. Kallonta yayi yace

"Babu rakiya ko?"

Da sauri ta bi bayanshi tace

"Muje"

Yana gaba tana binsa a baya suka fita, saida ya shiga ya duba Asiya sannan ya fito ya iske ta bakin mota. Murmushi ya sakar mata itama ta mayar mashi.
Bude mota yayi ya ajiye kayanshi sannan ya juyo gareta. Harde hannunwansa yayi a kirjinshi yana kallonta.

"Yanzu ma rakiyar hakanan zakizo kimun tsaye ko? "

Girgiza kai tayi tace

"Toh Allah ya bada sa'a"

Shi daria ma ta bashi  yanda takeyin magana ko kallonshi bata iyawa. Ya sani sarai kunyarshi takeyi. 

Tattaki yayi yazo inda take ya riko kugunta.  Kafin ta farga, ya hade bakinsu waje guda yana tsotsa kamar wani alewa.

Sai dan kanshi ya kyaleta sannan ya shige mota ya tafiyarsa.
Kamar wacce ruwa yaci, tayi tsaye a wajen, itama dan kanta ta shigewarta.

Duk abinda ya wakana a idon Asiya da kishi ya turnuke, ta cika tayi bam,  gashi babu damar ta taba fatima, wayasan ko yanzun kuma mutuwa zatayi.
Tunda ta lura fatima qwai ce, saida luliya, inka mata rikon banza ta fashe kuma ya zama masifa. Share kwallar idonta tayi ta koma kujera ta zauna tana tunanin ta hanyar da zatabi ta kawar da fatima daga gidan.

Jarkasa_jnr yace "kainuwa dashen Allah"
Ni kuma nace

"Tun kan daran,  akai kwandi, kuma dole dai acewa mijin inna baba"

Fatima kam har azahar babu abinda takeyi sai aikin tunani. Har yanzu tanajin taste din bakin Aliyu cikin nata. Inta tuna wani abun sai tayi murmushi.

Aliyu kam,  saida ya fara zuwa ya gaida umma sannan ya wuce wajen aiki, tare da mata alkawarin juma'a zaya kawo fatima, dan kuwa umma tayi korafin ya boye mata yarinya.
Bayan asali kuwa Aliyu namiji ne mai matsanacin kishi,  shine dalilin dayasa yake hana fatima fita tun karamarta, balle yanzu da take matar aure,  matarsa kuma.
Gani yakeyi inta fita,  mazan duniya ita kawai zasu dinga kallo.

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now