💫🌼eighteen🌼💫

2.6K 219 4
                                    

Written by khaair

Biki ya kankama. Umma hidima takeyi sosai. Fatima yanzu ko fita batayi. Su asiya ne keyin hidindimun. Muktar ma tun zuwanshi bai sake zuwa ba dan kuwa aiki ya masa yawa, amma kusan ko wanne lokaci zaya kira wayar umma yaji muryar fatima. Suyita waya basu gajia.

***

Yau ya kasance ranar talata. Ranar kunshi. Tun safe muktar ya aiko driver yazo danya kai fatima salon gyaran gashi.
Asiya ta mata rakiya sukaje. Sai wajen 3 na rana suka dawo. An gyara mata dogon gashinta baki kirin yayi kyau yana salki.

Koda ta dawo gida cike yake da yen uwa da abokan arziki. Ana gamawa farida kanwar muktar din, dan suma sunzo daga gidan mijinsu itada fadila. Fadilan ma ake cikin yiwa.

Sadiya ce diyar Aunty hauwa ta fito daga dakin umma, wanda yayi daidai da shigowar su fatima. Aida gudu tazo ta rungumeta tana cewa

"Amarsu ta ango"

Duka fatima takai wa sadiya tace

"Kaji marar kunyar yarinya, saikin karyani"

Dariya sadiya tayi tace

"Yi hakuri Aunty Amarya. Kar ya muktar ya yankani"

Itama dariyan tayi tace

"Wai yaushe kika dawo, ko kunyi hutu ne?"

"Wallahi shekaran jiya muka gama exams, ulul albab sun karo wulakanci, seniors muke fara gama exams, sannan juniors."

"Allah sarki. Yanzu ai ss1 kike ko?"

"Eh wallahi. Na kagara na gama secondary school dinnan nima ko auren nayi"

Ta gama maganar tana tuntsirewa da dariya.
Aunty jamila dake cikin kitchen tana jinsu tace

"Laaah, sady yanzu ke har kinsan aure"

Ai da gudu sadiya ta ruga dakin umma tana dariya. Mutanen waje suka saka dariya suma.
Nan fatima ta shiga cikinsu suna gaisawa. Tace

"Naga ma akwai sauran wadanda ba'awa kunshin ba da yawa. Bari na aika a kawo wata mai kunshin, kar ayi dare"

Wata kawarta munawwara tace

"Yauwa dan Allah, akwai layi sosai"

Fatima ta ari wayar umma ta kira wata salame mai kunshi anan unguwarsu. Ta amsa da gatanan zuwa.

Tana cikin alwalar la'asar saiga salame.
Tace duk wanda ba'awa ba yaje yayi sallah sai azo a cigaba.

Bayan sunyi sallah akazo aka cigaba da kunshi.
Sai wajen shida na maraice aka gamawa mutane. Dan har inna an mawa. Saida salame tayi sallar magrib sannan tayiwa umma. Tace zataje gida, wajen tara na dare zatazo tayi mata nata kunshin dan sai an turara nata.
Ta amsa da toh.
Ta gama sallar isha'i, bayan tayi shafa'i da wutr ne aka aiko yaro wai tazo inji muktar.

"Toh"

Kawai tace
Hijab ta zira kawai ta fita wajen.
Cikin mota yake zaune. Gefen mai zaman banza ta shiga tareda sallama. Amsawa yayi tareda cewa

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now