Written by khaair
Yau ne Abba ya yanke shawarar sanar da fatima da maganar sa bikinta. Saboda haka bayan ya dawo wajen aiki ya kira fatima dakinshi.
"Abba gani"
Gyara zama yayi sosai sannan ya dubeta yace
"Fatima"
Gabanta ya fadi ras, saboda Abba bai taba kiranta da fatima ba, saidai idan har magana mai nuhimmanci ne.
"Fatima kira nawa nayi miki?"
"Kira biyu kamun Abba".
"Good, kindai san nine mahaifinki ko? Kuma saninki ne bazan miki zabi na banza ba, zabin da zaya cutar dake. Hakane ko?"
Gyada kai tayi tareda cewa.
"Hakane Abba"
"Yauwa, to a matsayina na mahaifinki, wanda ya isa dake, na zaba miki muktar a matsayin mijinki."
A razane ta dago kanta ta dafe kirji
"Abba ya muktar kuma?"
"Kwarai kuwa, muktar shine wanda na zaba miki, naki yayi saura biyayya, nayi magana da sauran iyayenki, sunyi na'am da hakan, dan kuwa har an saka rana, wata biyu masu zuwa za'a daura aure"
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai fatima take karantowa a ranta, hakanan taji kuka ya taho mata. Ta fashe da kuka. A rude Abban yake tambayarta lafia? Kasa magana tayi. Dakyar ya samu tayi shiru sannan yace
"Bintu, a tunanina, koda wuta nace ki shiga zaki shiga, sai danna hadaki da muktar kike kuka kamar an cire miki rai iye? Ko kina da wanda kikeso ne?"
Kasa cewa komai tayi, saidai ajiyar zuciya da takeyi.
"In kinada wanda kikeso ki fadimun tunda wuri kafin abu yayi nisa."
Jin haka yasa ta bude baki tace"Abba ni ba sonshi nake ba"
Nanta kwashe komai ta fadawa Abba tun farkon haduwarsu, har zuwanshi gidan.
Sosai Abba yayi mamaki, amma sam ranshi bai baci ba.
"Shi kabirun a ina yake, su waye iyayensa kuma? Mene sana'arshi?"
"Abba ni ban sani ba, nadai san dan kasuwa ne, kuma watan baya mahaifinshi ya rasu."
"To abinda za'ayi, ki gaya mishi yazo gida gobe war haka ina nemanshi."
"Toh Abba""Jeki Allah miki albarka"
Tashi tayi ta shiga daki, ta hau gado ta kudundune, kuka takeyi son ranta bamai lallashi. Tasan tsakanin kabir da muktar babu wanda takeso. Amma kuma batasan meysa harta gabatar da kabir din wajen Abba ba. Anya tayiwa Abba adalci? Kamata yayi ace duk zabin da zaiyi mata tayi hakuri dashi ta karbeshi da hannu biyu.
"Kayi hakuri Abba, bansan me yake damuna ba, ina cikin tsaka mai wuya"
Shine kawai abinda take furtawa.
![](https://img.wattpad.com/cover/126442930-288-k893284.jpg)
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...