💫🌼eleven🌼💫

2.7K 159 1
                                    

Wriiten by khaair

Babu abinda ya rage shakuwa tsakanin Aliyu da fatima, saboda a yanzu ma, dashi kawai take chatting, kullum a jone suke online. Ita dai kullum rigimar yaushe zaya dawo tana missing dinshi. Yace break din one week kawai suke bashi. Amma duk lokacinda ya samu lokaci, koda 3weeks ne, in sha Allahu zayazo.

Muktar ma kusan kullum sai yazo. Suyita hira. Shi koda wasa bai fada mata wani abu ba, yana jiran Abba ya fashe kwai ne.

Kabir ma bai fasa zuwa ba. Yau dinma tun wajen 3:30 ya zo wajen da suke haduwa, da yaje hanyar ba mutane suke bi ba, sai jefi jefi, shiyasa baya damuwa da komai. Ita fatima din cikin hanzari tayi shirin islamiyya, danta san yana can yana jira, gashi karta makara islamiyya, cikin sauri ta leqa dakin aunty bilkisu tace ta wuce. A hankali take tafiya cikin nutsuwa, harta karasa a wurin. Yana ganinta ya fito yana mata murmushin daya ke sata wani irin  tunani. Gaida shi tayi hadida risinawa kadan, ya amsa tareda fadada fara'arsa.

"Shine kika shanyani ko"
Abinda ya fada kenan tareda karkace kai ya bata fuska yanda yara sukeyi. Dariya tayi, wacce kusan ba cikin kayanta bace, saidai murmushi. Kallonta yakeyi cikeda so da kauna. Itama shiru tayi tareda kallon kasa.
Murmushi yayi yace

"Dariyarki tana mun kyau binafa na, kinada kyau, komai naki yanada kyau, kinada hankali fatima. Inason ki, ina sonki so mai tarin yawa, a kullum addua tawa, bata wuce Allah ya bani ke a matsayin matata, nidai fatana kibani izini naje wajen Abba, in har na mallakeki, na cika wani babban buri a rayuwana faty na, inda zaki saurari bugun zuciyana, wallahi duk lokacinda nake tare dake, bugun zuciyana yana linkawa daga uku uku zuwa tara tara. Fatima i love you so much."

Fatima dake tsaye, sai taji kafafunta suna neman kasa daukarta, saboda kabir ya daureta da jijiyoyin jikinta. Kasa magana tayi. Saima ta fara wasa da yatsun hannunta.

"Nasan ba zaki iya magana ba, saboda zuciyarki da tunaninki suna yaki da juna, kowanne na baki wata shawara. Fatima rokonki nake, karki hanani gwada damata, wallahi kinji na rantse miki fatima, ban taba son wata 'ya mace ba sai a kanki, mata basa birgeni, akwai kyawawa a gari, kuma suna sona, fatima amma ke din zuciyana take so, from very first time i see you, i knew you are the one for me."

Salati kawai fatima takeyi a cikin ranta, dan a yanzu ji takeyi kamar ta nutse kasa.
Kabir kamar ya lura da hakan, yace

"Binafa, nasan kunyarki, yanzu kunya kikeji ko? To tafi islamiyya kinji, karki makara, nidai ya kamata gida a baki waya hakanan, kince mun fa you're going to 17 next month, july kenan."

"Ya Aliyu ya aiko mun da waya a bani tun last week. Bansan number na bane ba dai."
Cikeda zumudi kabir yace
"Ina wayan yake? Kina tareda da shi?"

Gyada kai tayi tareda saka hannu a Aljihun rigarta ta zaro wayar kirar samsung s6 ta mika masa. Karba yayi yace

"Akwai kudi a ciki ko?"
Gyada kai tayi. Number shi yayi dialing ciki, ya danna call. Wayarshi dake cikin aljihu ta soma suwa, maida nata wayar yayi yace
"Gashi, zaniyi saving number. Wallahi fatima naji dadi sosai, Allah ya biya yaya Aliyun mu,"

Murnushi tayi tace
"Amin, bara na wuce, kaga 4 har yayi."

"Ai kin biyani binafa, yau naji dadi, tunda koda kin koma gida zamu cigaba da magana. Ki maida hankali kinji. I love you."

Har yayi gaba sai kuma ya dawo, ta gefenta ya raba ya hura mata iska a ido.
Murmushi tayi tareda barin wajen da sauri sauri. Shi dariya kabir yayi sosai.
Ya shiga motarshi zuciyarsa fal da farin ciki.
Daren ranar wuni sukayi suna waya da kabir. Wanda har gajia fatima ta soma dan bacci ya fara figarta, muryar kabir yana sauke mata kasala, uwa uba maganganunshi, saisu saka ta jin kamar bata kyautawa.

A bangaren Aliyu ganin Zarah shi bata online yau, kuma gashi bata kira shi ba. Ya sashi tunanin anya lafia. Har wajen 11 yaji shiru, waya dauka, "heartbeat" yayi dialing, mamaki ya cikashi jin number busy. Ya kira yafi sau 20 amma number busy, tambayar kanshi yake to dawa take waya ne, da sauri ya kawar da tunanin dan yana neman sa mishi hawan jini. Wajen 11:30 ya kuma kira, har ya lokacin number busy. Tsoro ya fara ji.
Yadai ajiye wayar.

A bangaren fatima kuwa, cewa kabir tayi
"Bari na kwanta, ni ban taba kai 11 bafa banyi bacci ba, idona har nauyi yakemun."
Murmushi yayi wanda ta jiyo sautinshi yace."toh binafa, take care of yourself kinji? Saida safe in Allah ya tashemu lafia. Allah miki albarka. I love you so much."
"Um"
kawai ta iya cewa. Inda sabo, kabir ya saba da rashin maganar fatima, sai ya zauna yayita surutu, yana gamawa amsarta bai wuce eh, um ko a'a, lokaci da yawa ma shiru takeyi.
Cen kuma tace
"Allah ya bamu alkhairi" tareda datse wayar.

Ajiyar zuciya tayi. Ta tashi ta shiga toilet, alwala ta daura, ta hau sallaya, ta saba kafin ta kwanta ko kuma inta tashi ciki  dare tayi nafilfili, koyawar ummanta ne wannan, dan kuwa a da, komin baccin da fatima zatayi, indai umma ta tashi sallah a cikin dare, zata tashi fatima ne. Tun fatima tana kallon abin kamar takura, har yazo ya zauna mata jiki ta gane ashe gata ne umma take mata, yanzu koda batanan, tasan in ta tashi tayi sallah, akwai kason umma a cikin ladarta. Murmushi tayi tace.

"Allah  sarki ummana, Allah ya biyaki da gidan Aljannah, Allah ubangiji ya gyara tsakaninku da Abba ummana, mu koma rayuwarmu irin ta da. Ko mene ya shiga tsakaninku, d yardar ubangiji Allah zaya warwareshi"

Kabbara sallah tayi. Tana a raka'a na biyu wayarta ya hau ruri, batayi yunkurun kara sauri wajen sallarta ba. Hankali kwance takeyi. Saida tayi raka'a goma sallama biyar. Tayi addua  ta shafa. Kayan bacci ta saka ta hau gado tareda janyo bargo ta rufa kanta, dan kuwa yau an zuga  ruwan sama tun wajen magrib har kusan goma na dare, gari ya dauki sanyi.
Ta mance shaf da an kirata. Ta shafa adduar bacci kenan taji wayar ta kuma ruri, a hankali ta janyo tana mamakin wazai kirata wannan lokacin.
"Yayana" ta gani a rubuce.
Dan zaro ido tayi. Sai yanzu ta tuna, yau basuyi magana ba, dole ya nemeta yaji ko lafia. Sai a yanzu taji haushin kabir daya riketa sunata waya. Kafin tayi yunkurin dauka harta katse.
Da saurinta ta kira shi. Bugu guda ya dauka. Kafin ya fara magana har tace

"I'm so sorry yayana na kaina, i'm very sorry yaya, wallahi ina sallah ne kayita kirana, kayi hakuri my lovely brother".
Shiru yayi yana sauraren yanda take magana cikin sanyi. Baima san lokacinda duk haushin daya keji ya bace ba.  Murmushi yayi kadan. Amma sai yace
"To dawa kiketa waya, ina kiranki tun dazun inajin busy"
Gabanta ne ya fadi. Yaune rana ta farko a tarihin rayuwarta da tayi yunkurin yi masa karya, wata zuciyar tana cewa kar tayi, wata zuciyar kuma tana cewa ai inta fadi mashi gaskia fada zaiyi mata, kuma zaiyi fushi da ita...

Khaair❤

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now