💫🌼twenty five🌼💫

3K 148 2
                                    

Written by khaair

Lokaci ya ja, awanni sun koma kwanaki, kwanaki sun koma sati, sati sun koma watanni.
Babu abinda ya cenza ga zaman fatima da kabir. Dan yanzu fatima ta aje komai gefe. Ta yakice kunya ta rungumi mijinta. Umma kullum tana zage damtse wajen ganin ta dora fatima a hanya.

Kabir najin dadin zama da fatima wacce take komai danta faranta mashi. Shima bai kasa da guiwa ba ganin ya mata abinda zataji dadi.

Lokacinda admission dinsu ya fito. Sosai fatima taji dadi. Ta samu microbiology. Tareda kabir sukayi registration da komai. Mota sabuwa ya siya mata na zuwa school. Har driving school ya biya mata danta koya mota. Saboda gudun latti wata rana. Fatima bata da bakin gode masa. Su abba ma sai godiya sukeyi.

Yauma ranar lahadi, kabir baije ko ina ba. Yana kwance bisa cinyar fatima dake wasa da gashin kansa

"Ya kamata a aske gashin nan fa. Yayi yawa"

Yamitsa fuska yayi yace

"Ki bari kawai, gashin nan duk sati nake aski, amma kullum fitowa yakeyi."

"Ayi hakuri a aske dan Allah".

"Duk yanda kikace haka za'ayi baby"

Batace komai ba, shima baice komai ba, suna kallon film. Hankalinsu duk yana wurin. Cen kuma kabir ya maido hankalinsa ga fatima dake gyangyadi yace

"Sarkin bacci. Ko 3hours bakiyi da tashi bafa."

Turo baki tayi tace

"Ni baccin nan har ya fara isata wallahi"

"Ba dole ba. Kuma wai nan kina zuwa school. Haka kike je musu school din kina bacci ko?"

Dariya tayi tace

"A'a wallahi..ni ina naga ta bacci a lecture hall."

"Fatima"
  
Kallonshi tayi tace

"Na'am"

"Wai meysa baki iya kiran sunana ne"

Murmushi tayi tace

"Yamun girma ne sunan"

"Toni inaso ki dinga kiran sunana. Kuma banaso ki saya."

Zaro ido tayi tace

"Kanaso ummana ta zaneni. Tace inayin rashin kunya ko?"

"Nooo ba a gabanta zakina fada ba. Ni inaso kawai kina fadan sunana."

"Tohm zani kwatanta nagani"

Hira suka cigaba dayi har aka kira azahar.

Kabir ya wuce masallaci. Kasancewar hutun sallar takeyi. Ta shiga kitchen hada abincin rana. Koda ya dawo ya shiga tayata suka gama tare.

Saida sukayi wanka kowa a dakinshi. Cikin sabuwar kwalliya da kananan kaya fatima ta fito parlour. Kwance ta
Iske kabir yana latsa waya. Koda ta iso ya ajiye wayar ya dubanta.

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now