Written by khaair
Saida akayi magrib sannan suka dawo gida. Aliyu ya kara mata nasiha akan ta kula, banda kawayen banza, sannan bayason jin maganar samari koda wasa. Tace in sha Allahu... zaya tafi kuma Abba ya dawo, saida suka gaisa, har ya jira akayi isha'i sannan ya wuce straight asibiti, baije ba duk ranar.
Tun bayan komawarsa gida ya kasa daina tunanin fatima, daya juya fuskarta yake gani. Ya rasa zaune balle tsaye. Ya dauki alwashin gobe kuwa saiya koma inda suka hadu jiya din dan kuwa ko sunanta bai sani ba.
Nace "Hmm"***
Washe gari kamar jiyan ta shirya da wuri zuwa islamiyya.
Tanata sauri danta samu wajen zama daga gaba. Saida ta kusan islamiyya, kamar a mafarki taji ana fadin
"Sister, sister, kiji mana"
Tsayawa tayi tareda juyowa. Turus tayi ganin mutumen jiya wanda ya kusan banke ta. Da dan saurinsa ya karaso yace
"Kiyi hakuri na tsaidaki, inaso na miki tambaya ne."
Batace komai ba, saidai dan karamin murmushin da tayi.
"Mey sunanki please"
"Fatima"
"Nice name fatima. Ni sunana kabir. Nasan dai kin ganeni, na jiya dinnan."
"Eh" tace a takaice.
"Fatima naga sauri kikeyi, ko zaki bani phone number naki."
'"Kayi hakuri, gida ba'a bani waya ba, banada waya."
Dafe kai yayi
"Oh God, toh shikenan. Anan unguwar kike ko?"
"Eh anan muke, daga gefen babban masallaci na jumua, mai farin gate."
"Allah sarki, islamiyya za'aje?"
"Eh, karna makara ma, bari naje"
"Toh fatima, nagode kwarai."
Murmushi ta sake yi masa ta wuce.
A islamiyyar kuwa duk wasu sun zauna a gaba, ta samu wuri daga tsakiya ta zauna, ta dudduba bata hango asiya ba. A ranta tace
"Mashiririciya, ta tsaya bacci ta tashi makare"
Ko mintu biyu batayi da zama ba mallam ya shigo. Tajwid sukayi. Ana cikin yi su Asiya suka shigo. Mallam saida ya musu fadan makara yace idan suka kara zaya hanasu shigowa darasin shi, sannan suka zazzauna.
Bayan fitar mallam, asiya ta dwo wajen binafa, yau basi fita ba, sunanan zaune suna hira, cikin hirar ne Fatima ke bawa Asiya labarin sun kara haduwa da wannan mutumen na jiya.
"Kinga me nake fada miki ko, ki tsaya nan kallon ruwa kwado ya miki tsirfa""Amma fa Asiya kinsan bazan bijirewa maganar yayana ba ko? Dukda nasan ban taba tsayawa da wani namiji ba bayan shi wannan kabir din, harna fada masa sunana ba, da kwatancen gidanmu. Amma bawai hakan na nufin ina sonshi ba. Mutumen yanada kwarjini sosai, baxan iya mashi wulakanci bane"
"Ki tsaya nan to. Ni inkin san babin shawarata zakiyi ba, kibar bani ko labarinshi"
Fatima bata sake magana ba, ita ta tsani tsiwa. Saima ta dauko arba'una hadith dinta tana kara biyawa, anjima za'ayi shi da an dawo daga shan iska. Ganin ta shareta, itama Asiya ta tashi daga wurin ta koma wajen wasu kawayenta.Bayan an tashi islamiyya kowa yayi hanyar gidansu, fatima ko takan Asiya bata yiba, danta lura da Asiya nason jefata hanyar banza ne idan tayi wasa. Data isa gidan ma babu kowa, saboda haka ta dauki kayan makarantar bokonta ta goge.
Ta dauki Qur'an tana biya karatunta. Saida ta tabbatar da ta haddace sannan ta ajiye.
Kiran sallah aka kwallara. Tayi sallarta tsaf, tana bisa sallaya bacci ya fara fisgarta, ta gyara kwanciyarta sai bacci.***
Wasa-wasa kullum indai fatima zataje islamiyya, saita hadu da kabir sun gaisa, kuma bata taba jin haushin abin ba, kamar yanda takejin haushin sauran samari in sun mata haka. Amma tasan ita ba sonshi take ba, shima din bai bude baki yace yana sonta ba.Akwai ranarda ta wuce bata ganshi ba, duk saita ji babu dadi, har dan tsayawa tayi taga kodai bai ida isowa ne ba, amma shiru. Haka ta tafi islamiyya duk ranta babu dadi, ta rasa dalilin jin haushin, harta kasa maida hankali. Haka ta koma gida, a hanyar gidan ma tanata waige-waige taga ko yazo. Amma bata ganshi ba. Rai babu dadi ta isa gida.
Shiko kabir yazo, kawai cikin shago ya shiga yayi zamanshi, ta yanda idan ta wuce zaya hangeta, data tsaya tana jiranshi, sai yaji wani iri, harda aka tashi yananan. Saita bashi dariya yanda take waige-waige, yasan shi take waigaya taga ko yazo.
Lokacinda ta wuce ta gaban shagon, nan ne yake tambayar mai shagon manniru
"Chairman, wai wannan yarinyar 'yar ina ce?"
Manniru da hankalinshi yana kan cinikinshi saida ya leka yaga fatima sannan ya murguda baki yace
" yarinyar gidan Alhaji Abu sanda ce, akwai kyau da ladabi, amma sai ji da kai."
"Ah haba mai gida, yanzu ni idan naje nace ina sonta sai ta koreni ta yarfani kenan?"
Zaunawa manniru yayi sosai yace
"Kaga wannan yarinyar, bari in maka na mahaukaci, danginsu kyawawa ne, kamar anan unguwar, itada yayanta Aliyu sune ma zanice maka sunfi kowa kyau, danshi har yaso ya wuceta. Kuma sunada tarbiyya mai ingantacciya. Gashi ita kadai ce wajen mahaifin, shi Aliyun yaron kaninshi ne. Shiyasa Alhajin ke sonta sosai.Amma ita ni gani nake kamar ta cika hangen nesa, tun daga manya har kanana, babu wanda baizo neman aurenta ba wajen mahaifinta, shi dai saiya ce tayi yarinya, girman jiki ne da ita, amma indai ta amince, zai mata aurenta. To koni da kake ganina nan, saida naje gidansu, da ledoji na manya, gani nake ko kilan masu kudi takeso, aiko ta watsa mun kasa a ido wai karna sake mata irin wannan. Wallahi har kuka saida nayi, dan ina bala'in son yarinyar da kuma nutsuwarta amma tunda ban sameta ba na barwa Allah"
Me kabir zaiyi inba dariya ba hada rike ciki, kara kallon manniru mai shago yayi, guntu ne na kwarai, gashi baqi wuluk, dan dakyar inya shiga duhu ka ganshi dan bakinshi, gashi hakoransa na gaba sun cire guda uku, sunyi jawur alamar cin goro, hancinsa kamar yaje dambe saboda ya karkace, a haka wai zaije wajen Fatima. Wata muguwar dariya kabir ya kara harda hawayensa, manniru kuwa ya hasala. Kabir yace
"Chairman, ba dole tace karka kara zuwa ba, ai hakoran roba ya kamata aje a saka maka a gaban nan saboda ka fito a yaronka, amma kaje baki wawulau, sai tayi tunanin kai sa'an kakanta ne. Kuma kaje wankin hakora duk goron nan a wankeshi hakoran suyi tas, hancinka kuwa kaje asibiti a saita maka shi, tsayi ne dai ban san inda ake samu ba"
Shiru manniru yayi yana nazarin maganar kabir, cen ya gane latsa shi kabir yake. Aiko fuska a murtuke ya kalli kabir dake kunsar dariya yace
"Mallam, fitar mun daga shago"
Shiru kabir yayi kamar baiji ba
Manniru ya kara cewa
"Bakaji ba"
Tareda dauko wani dogon icce wanda yake amfani dashi yana dauko abubuwan da sukafi tsayinsa. Kabir na ganin haka ya fice daga shagon a guje yana dariya. Cen karshen layin ya isa ya shiga motarsa ya wuce gida.Khaair❤
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomanceFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...