Written by khaair
Junior girmanshi har mamaki yake bawa jama'a. Yanzu watanshi hudu amma saika rantse yayi wata bakwai. Fatima har complain din girmanshi takeyi.
Umma tace yanayin nononta ne. In nono nada kyau, sai yaro yayi girma yayi kyau.
In kuma baida kyau, wani yaron sai an hada da madarar gwangwani sannan jikinshi yakeyin kyau.Asiya dukda tana kokarin taga sunyi zaman lafia da fatima, ta jawo fatima jiki ko Aliyu zaya sota itama.
Amma hassada da bakin ciki basu barinta ( Allah mana tsari da mahassada, Amiin).Fatima itadai ta ajiye hankalinta waje guda ta rungumi duk kaddararta. Yanzu kam batada damuwa.
Akwai kishi, halitta ce.
Amma dole take kwantar da kishinta kuma ta jawo Asiya jiki.
Asiya itama wani lokacin tanajin babu dadi. Amma munawwara da kawayenta suke bata shawarar banza. Kullum zugata suke akan wai ta kashe junior, inba haka ba, ko Aliyu ya mutu, batada gadon komi, tunda yaron namiji ne. Ita kuwa gatanan ko batan wata bata tabayi ba.
Hakan yasa hankalin Asiya yayi mugu mugun tashi. Kullum. Neman hanyar kawar da junior take.
To daman zuciyar mugun abu ya kasheta dole ta amsa shawarar iska.
Yanzu bama ta fatima take ba.
Dukda fatima dinma ta tsone mata ido. Amma ta dauki alwashin saita kashe junior, saidai duk abinda zaya faru ma ya faru.Yauma Aliyu ya fita office, girkin fatima ne.
Duk bayan awa daya ko biyu saiya kira fatima yaji muryarta.
Ta zama part of him. Baya iya rayuwa bai jita kusa dashi ba ko baiji muryarta ba.Yanzu haka ma ya kirata sunata hira a waya.
Bangaren Asiya kuwa, tana kitchen ta soya man gyada yayi zafi sosai. Sashen fatima ta leka ta window. Babu kowa parlour din sai junior dake ta wasa da toys dinshi.
Yasa wasu a baki duk ya batasu da yawu.
Fuskarta daukeda murmushi ta koma kitchen din. Tsumma tasa ta dauki frying pan din tareda kashe gas din ta fito.
A hankali ta bude kofar part din fatima wanda fatima ta mance bata rufe ba.A bangaren fatima kuwa Aliyu yace
"Sunshine, wai ina mutumina ne? Ya barmu muna soyewa, ko bacci ake?"
"Ina wannan dan rigiman zayayi baccin rana, na bashi toys ne dai yana parlour yana wasa."
"Baby please ki daukoshi mana. Ki banishi"
"Yanzu shi wannan me zaya ce maka?"
"Please ki daukoshi, i wanna feel my baby boy."
"Wallahi junior wajenka ya gaji rigima"
Tana jin dariyarshi ta saka wayan handsfree ta fito parlour.
Dukawar da fatima zatayi ta dauki junior yayi daidai da lokacinda Asiya ta kwarara soyayyen man gyadan. Ihun da fatima ta saki ya sa Asiya sakin frying pan din ba shiri.
Jikinta sai karkarwa ya farayi.
Ihun fatima ba karamin razana Aliyu yayi ba dayake sauraren fatima."Zarah, meyene? Zarah wani abu ya sami junior ne?"
Yakai minti biyar ya tsaya sauraren mi zatace.
Jin shiru ya kashe wayar tareda mikewa. Key din motarshi sai wayanshi kawai ya dauka.
Sauri sauri gudu gudu ya bar asibitin ko excuse bai tsaya badawa ba. Lafiyar iyalinshi tafi komai.A abinda bai wuce minti bakwai ba ya iso gidan.
Tun daga harabar gidan yaga Asiya sanye da hijabi zata fita duk a rude take.
Ganin Aliyu yasa ta koma cikin gidan da gudu.
Shida bama ta kanta yake ba ya shiga part din fatima da gudu.
Salati ya dinga jerowa daya bayan daya. Ganin fatima kwance kasa sumammiya.
Ga junior yanata shirgar kuka.
Junior din ya fara dauka yana rirrigashi.
Dakyar ya samu yayi shiru. Ya ajiye shi gefe.
Hannun dazai saka ya juyo da fatima yaji kamar ya wafto fatar jikinta ga jikin shane shane da mai, ga kasan carpet dinda yake tsakiyar dakin shima jike da mai.
A razane ya daga doguwar rigar dake jikinta.
Tuni tsikar jikinshi ta tashi ganin yanda bayanta ya rure duk wutar ta taso da kuma inda ya ciro bada saninshi ba.
Daga tsaye saida ya fadi kasa bai sani ba.
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
RomansaFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...