Written by khaair
A kwana a tashi babu wuya wajen ubangiji. Fatima sai sam barka, dan kuwa tuni sun gama waec, har sun kusan karkare neco, paper biyu ya mata ragowa, murna kuwa takeyi sosai. Sunyi jamb, ta samu marks sosai, tayi applying nan umaru musa 'yar adua university.
Haduwarsu da kabir ya ragu sosai, dan kuwa yanzu sundays kawai take samun shiga islamiyya, saboda yanayin exams din, ranar da takeda da interval kuma tana zamanta gida tayi karatu. Sosai takejin dadin exams din. Duk kuwa ranarda zata je, driver ne zaya kaita, wani lokacin ya jirata, wani lokacin kuma yaje yayi 'yen hidindimunsa ya dawo ya dauketa.
Mukhtar ma yakan zo ya debe mata kewar Aliyu, dan sosai take kewar yayanta, inyazo, su kirashi a waya suyita hira, har sai ta gaji dan kanta sannan suyi sallama.
A bangaren mukhtar ma, wannan kusancin da yayi da fatima na 'yan watanni sai yaji duk ya saba da ita, shine sintirin gidan Abba kullum. A hankalin sabon ya rikide ya koma soyayya mai karfi wanda soyayyar tayi asali ne tun yarintar fatima. Hakan mukhtar yakejin bazai hakura ba da fatima.
Gashi mutum ne marar zurfin ciki sam. Aikuwa ranar jumua kamar yanda ya saba, yasan Abba yana gida, ya shirya, bayan an sauko masallaci, yayi hanyar gidan. Yaci sa'a babu kowa gidan sai Abba a kishingide parlonsa yana karanta jarida. Da fara'arshi ya amsa sallamar mukhtar tare da tashiwa zaune sosai, kusada kafar Abba ya zauna a kasa yana gaida shi, Abba ya mika masa hannu ya noqe."A'a mukhtar ba zaka bari mu samu tabari ba"
Dariya yayi yace
"Abba Allah kara girma dai. Mun sameku lafiya?"
"Lafiya kalau, ya gidan da mutan gida?"
"Duk suna lafiya Abba, suna gaisheku"
"To ina ansawa"
"Naji gidan shiru, basanan ne?"
"Eh wallahi, ita bilki din taje gida an mata rasuwa, Bintu kuwa yau take last paper dinta. Bata dade da fita ba"
"Allah sarki, Allah yaji kan musulmi, Allah bawa Fatima sa'a ita kuma, ai tanashan wuya. Allah dai kawai ya basu sa'a"
"Amin fa, kamar kasan kullum nan sai an isheni da complain, wai ita ta gaji da boko, wai wallahi zata koma wajen ummanta ne kawai"
Sosai muktar yayi dariya yace
"Ai fatima da wannan rigimar tata, saidai Allah."
"Kaima dai zaka fada, inda Aliyu ne kuwa, biye mata zaiyi suyi tayi, baya gajia da hidimar Bintu ko kadan, Allah dai yayi albarka."
"Amin Abba"
"To kai ya aikin naka?"
"Ai Abba aikinmu babu sauki, shari'a daya bayan daya, iri iri kuma, wallahi kasar nan dai Abba, matsalar aure, sata da fyade yayi yawa, cases zakana gani a kotu sunfi hamsin, amma kusan arba'in fyade, sata ko matsalar aure."
Girgiza kai Abba yayi cikin bacin rai yace"Ai wallahi ba wani sauki, rashin aikin yi ne da rashin wadatar zuci yake saka mutane sata, kaga yaro ya gama jamiar nan babu aikin yi, in kace zaka ba yaro kudi yayi jari ya fara ko sana'ar hannu sai yaro dora ma kanshi girman kai yace shi za'ace yana kaza, daganan fa sai shaye shaye, bin abokan banza, sata, fyade dadai sauransu. Aure kuma mazan ne bawai don Allah sukeson mace ba, da sunga kyakkyawa da jiki mai kyau, saisu liqe, su kuma matan son kudi, namiji mai kudi dai, iyayen yarinya kuwa da sunga an jibge kudi, ba bincike ba komai saisu bada yarinya, ina ka taba jin irin wannan? Ai dole bayan aure ayita samun matsaloli" ya ida maganar tareda da guntun tsokinshi
"Wallahi haka maganar take abba""Ai kasar nan tana cikin tashin hankali, Allah ya kara tsarewa dai"
"Amin Abba"Shirune ya biyo baya, muktar yanata wasa da yatsun kafarshi. Abba ne ya lura da hakan, yasan kenan akwai magana.
"Muktar da magana ne?"
Sosa keya yayi yana murmushi. Gyara zamanshi yayi yana kallon kasa, tareda bin zanen tiles dinda ke liqe da kasan parlour,
"Abba daman neman arziki nazo"Shima Abban gyara zama yayi, yace
"Neman arziki muktar? Wane arziki ne zaka nema a wurina ban baka ba. Menene bukatarka?"
Shiru kadan muktar yayi sannan yace
"Abba tunda na tashi kasan yanayin ciwona, shiyasa har yau, ban taba samun wata mace da nakeso ba, kowai wata mace ta birgeni ba, mata da yawa nasan suna sona, ni nasan bawai dan Allah bane, kodan kyau na, kodan abin hannuna ne, yanzu idon matan yanzu a bude yake" shiru yayi, sannan ya cigaba da cewa cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka,
"Abba tun fatima tana karama Allah ya azamun kaunarta, saina dauki hakan kamar sabo ne da mukayi nida ita, amma a sannu a sannu, abba soyayyar fatima tana neman zautani, in zaka tuno shekarun baya, akwai lokacinda na kauracewa zuwa nan, har saida kukayi meeting akaina, daga baya nake tambayar Aliyu wai shi yanason fatima ne, cewa yamun ya za'ayi yaso kanwarshi. Tunda na gane son 'yen uwantaka ne tsakaninsu, shine na dawo." A yanzun har siraran hawaye sun fara sintiri a fuskarshi. Dawowa yayi gaban Abban yanda zaya fuskanceshi sosai, ya tsaya akan guiwowinsa, tareda dafa yatsun kafar Abba.
"Abbana, kayimun rai ka bani fatima aure, soyayyarta na neman zautani. Inasonta fiye da yanda nakeson kaina. Kayi mun rai Abba"
ya fashe da kuka.
Sai duk Abba yabi yabi ya rude. Saukowa yayi kasa tareda kama hannun muktar"Menene haka muktar, akan fatimar ne kake kuka, ita ba 'yar uwarka bane iye? Kai kanka ka isa ka bada ita aure, ballantana ace kaida kanka kakeso, fatima kanwarka ce, kuma ni babanta na baka ita halak malak, bar wannan kukan da banason ma ciwo ya kama ka a wofi."
Murnace sosai a ran muktar wanda har ya kasa boyewa saida ta baiyana.
"Abba nagode, nagode Abba, Allah kara girma. Amma abba hanzari ba gudu ba, ni banaso a tilastawa fatima aurena, in dai akwai wanda takeso, zani hakura, dukda nasan abune wanda zaiyi mun wuya, in rayu babu fatima."
"A'a, kwantar da hankalinka, fatima batada kowa. Amma bazani ki ta taka ba, zani tuhumeta din naji, kasan yanzu zamani ne ya cenza, sai kayi zaton wuta a makera, sai ka ganta a masaka. In sha Allah, zamu zauna nida ita. Zamuyi magana. Kaji ko?"
"Toh Abba nagode sosai, Allah kara girma"
"Amin mukhtar"
Tare suka tafi masallaci. Daganan muktar ya wuce gida ranshi fal da farin ciki...Khaair❤
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
Roman d'amourFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...