8

8.9K 1K 9
                                        

Lokaci yaja Ahankali tafara sabo da kowa na gidan Bilal kuwa ba ruwansa tuni yayi sabo da kowa musamman Abba kamar dama Nan aka haifesa ammy kuwa Layla takeji matuqar ji da it's duk da har lokacin takasa sakewa gabaki 'daya aleeya ce madai ta sake da ita sbd yanda take matuqar ji da ita Wanda Dan Dole kowa keji da Layla agidan sbd aleeya.

Wata 'daya sukayi agidan suka tattara suka koma Lagos sbd can dama suke da zama hutu da aiki sukazo yi duk da dai su Yan asalin Nan 'dinne.

Sosai su Layla sukayi mamakin ganin girma da kyawun gidansu nanan din Dan duk kyawun na adamawa wannan yafi.

Decorations din dakin aleeya aka canxa musu komai bibbiyu aleeya blue Layla pink Amma gadonsu 'daya.

Kaya sosai ammy ta 'dinka musu kusan komai iri daya sbd gabaki 'daya aleeya cewa tayi batason komai nata asiya musu sababbi iri daya da Layla.

Ba iyayenta da Masu aikin gidan kadaiba hatta ita kanta layla mamakin tsananin qaunarda aleeya ke Mata takeyi sbd kaf rayuwarta ba'a ta6a nuna Mata qauna irin wannanba saidai iyayenta.

Bilal kuwa 'dakinsa dabam da Mai kula dashi Shima komai ansaka Masa tundaga kan wardrobe kayan wasa dana karatu sbd suna dawowa Basu wani jimaba aka sakashi makaranta primary 1 Amma ana hada Masa da lesson sbd yayi saurin fahimta Dan na class na Masa wuyar ganewa tunda ba ta6a shiga aji yayiba.

Layla kuwa Mai lesson guda aka dauko Mata sunayi ba qaqqautawa ga malamin arabic dake zuwa har gida Yana musu su duka uku Dan dama aleeya Bata zuwa islamiya saidai malam yazo gida ya karantar da ita.

Kullum dare kafin su kwanta sai aleeya tayita nanata Mata karantunta na lesson na addini kuwa sai sunyi sallar asuba.

Ada aleeya Batada wata walwa ko sakewa kullum tana daki kwance Wanda hakan ke matuqar ta6a zuciyar iyayenta harsuka dauko siyama 'yar yayar ammy riqo Amma rawar kanta da rashin nutsuwarta yasa suka mayar da ita gashi Sam basa shiri sosai da aleeya kullum cikin fada suke da kokawa da komai sai anrabasu Amma yanxu zuwansu Layla yasa hankalinsu kwanciya matuqa sbd ganin farin ciki a rayuwar 'yarsu su kansu yanxu hankalinsu yaqara kwantawa ganin gidan yasake kammala da yara Dan kuwa dukkaninsu jinsu sukeyi kamar yayan dasuka haifa uwa uba yanda Bilal yasake musu Yana yanda yakeso kamar sune suka haifesa ba ruwansa.

Lokacinda su aleeya zasu rubuta junior waec aka kutsa layla cikinsu ta zana duk da batai wani kyauba Amma ba laifi tasamu 4 credit shima sbd antaimaka matane sosai gurin rubutawar hutun shiga senior class suka fara cikin farin ciki sbd next hutu tare zasu koma and this time around boarding school zasu duk da ammy bataso sune sukeso Abba yace kuma tunda sunaso sai ankaisu.

Kwance suke a 'daki suna kallon hotunan dasukai a wayar ammy Bilal yashigo hannunsa riqeda wayar ammy 'daya Yana game yace,

Ammy tace kubata wayanta.

Ba Wanda ya kallesa cikinsu aleeya tace,

Ka Kai Mata na hannunka wannan muna hotuna ne.

Juyawa yayi da gudu saidai suka jiyo ihunsa da qarfi Yana Kiran Layla.

Azabure suka fito suna kaiwa Palo suka tsaya kallon wadda ke tsaye da babban akwatinta da alama shigowarta kenan sukaci karo tayi wani mugun ball dashi.

Da sauri aleeya ta qarasa ta riqosa daidai fitowar ammy tana cewa,

Lafiya waye ya ta6asa aleeya kune ko....

Ganin siyama tsaye yasa sake fara'a tana cewa,

Siyama kece daga zuwanki Kika ta6amin 'da.

Wani 'dacin baqin ciki ta ha'diye daqyar ta qaqalo murmushi tace,

Wlh karo mukayi bamu luraba.

Nasan arina dama bayason tafiya kullum saidai gudu,
Sannunki da hanya tafiyar bazata Kuma fa ko 'dazu nakira antin mun gaisa Amma Bata fadaminba.

Eh wlh ammy ninace Dan Allah karta fada muku nafiso ku ganni.

To ai kin kyauta saiku wuce ciki ki huta kici abinci.

Dakinsu ta nufa da akwatinta batareda ta kalli ko gefenda Layla takeba sbd zata iya ha'diyar zuciya sbd baqin cikin ganin yanda harta zarta aleeya kyan gani duk da aleeya ma ba bayaba gurin kyau.

Ammy Jan Bilal tayi suka wuce dakinta layla kuwa na ganin haka tayi kicin gurin shafa'atu tana tayata aikin abincin dare.

Aleeya ma kicin din tazo bayan taje sun 'dan ta6a fira da siyamar ta zauna kan freezer tana kallonsu suna aiki sai surutu take musu na wani labari suna dariya hankalinsu kwance.

Da daddare ma kafinsu kwanta Saida siyama taso cin zarafin layla kamar ammy tasani ta Aiko Bilal yakira layla tace tayi kwanciyarta a 'dakinta itakuma ta wuce dakin Abba.

Tunda siyama tazo gidan yazamewa layla wani iri sbd tsangwama duk da alamu dayawa sun nuna su Layla sun fita matsayi agidan yanxu hakan ke qara Mata wata irin tsanar Layla har cikin jininta takejinta duk da layla da ammy sunqi Bata fuskar wulaqantasu laylar duk saitaji zama gidan yafita ranta daqyar tayi sati biyu ta tattara takomawarta gida ta shiryawa uwarta qarya da gaskiya akansu laylar Nan itama umman ta qullaci ammy akan wulaqanta siyamar da'akayi kan sadaka yallah 'yayan tsintuwa.

Siyama na tafiya gidansu yadawo yanda yake hankalinsu Layla ya kwanta gashi lokacin tafiyarsu makaranta yayi tuni akayi musu komai aka kaisu Bilal harda kukansa shima akaisa bording school akasamu aka lalla6asa bayan kwana biyu tuni ya manta da maganar bording yafara sabawa da kadaicinsu danma shafa'atu ta iya debe Masa kewa sosai idan Abba na gari kuwa shekanan yafi kowa farin ciki.
#mamuhgee



                          VOTE
                      COMMENT

DAWOOD✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora