NOT EDITED
cikin dare suka isa cyprus suna isa gidan ta shige bedroom dinda ya nuna mata ta rufo qofa tareda sake ajiyar zuciya sbd atsananin takure take zama akusa dashi cikin jirgi da motarda takawosu gida.
saidata jima azaune shiru kafin ta miqe tashiga toilet cikin sanyin jiki tayo wanka da alwala tafito tasaka doguwar riga mai 'dan nauyi sbd kaf kayan datazo dasu masu 'dan nauyine da rufe jiki kaf.
saidata tayita sauke numfashi tasamu tafito daqyar palo daidai fitowarsa daga bedroom dinsa batareda ta dagoba ta tambayesa gabas,
murmushi yasaki ahankali tareda matsowa kusada ita ya riqo hannunta,
rawa jikinta ya dauka sosai ta rintse idanu sbd kar hawayen ciki su zubo mata.
sakinta yayi yana kallonta ganin yanda jikinta ke rawa sosai,
ajiyar zuciya ya sauke tareda sake riqo hannunta har cikin dakin ya nuna mata gabas matso da fuskarsa zai mata kiss a goshi tayi saurin durqusawa tana sosa qafarta da hannunta ke rawa.qaramin murmushi yasake tareda juyawa ya fice.
saidata share hawayen dasuka gangaro mata tasamu tayi sallolin tana gamawa ta cusa kai tsakiyar qafafunta cikin taraddadi da damuwar irin zaman dazasuyi da taheer.
ta dade sosai ahaka kafin yasake knocking yashigo 'daukeda kwalin kfc na order abinci dayayo musu ya aje mata ahankali yace,
kici abinci.
ya miqe ya fice.
coke din kawai tasha sai burger data gutsiri kadan ta ajiye sam batajin yunwar cin abinci.
kwashe kayan tayi takai fridge tadawo ta kwanta sbd zazza6i datake ji ahankali.
washe gari saida yayi mata order breakfask kafin yashirya ya fice,
baidawo gidanba sai magrib sosai baiji dadiba sbd wani aikine ya riqesa yayita bata hakuri duk da dai kamarma ya lura tafi nutsuwa idan baya kusa,
kwana biyu baicika zamaba shiyasa yayo mata shopping na komai na abinci duk lokacinda ta buqata taci sbd damashi rayuwarsa aikine kawai,
kullum kafin yafita zaiyi mata knocking yace mata zai fita hakama idan yadawo sbd sam bayason takurata,
kullum da damuwa take tashi da ita take kwana ga tausayin taheer din data faraji sbd sosai yake iya qoqarinsa na ganin ya kyautata mata bai takurataba,
duk lokacinda tayi waya da aleeya aleeyar na qoqarin danne tashin hankalinta da danuwarta ta nuna mata komai yafara sauqi tsakaninta da dawood sbd kawai ta kwantarwada laylar hankali,
tayi kuka tayi farin jin hakan shiyasa tafara sawa kanta dauriya tana dan fitowa palon gidan yanxu duk da tsananin damuwarta,
idan yadawo yanxu takan gaishesa batareda ta dago ta iya kallonsaba hakan ba qaramin dadi yakemasa ba shiyasa yanxu yake qoqarin rage ayuka yana dawowa gidan da wuri,
sannu ahankaki lokaci yafaraja sosai suna tana iya qoqarinta na danne ciwonta da damuwarta gurin fahimtarsa da kulasa duk da harlokacin doguwar magana bata ta6a shiga tsakaninsu ba saidai yana iya qoqarinsa yaga ya kyautata mata sb yagano tana girmamasa da hakan,
abu daya yasani yake kuma damunsa shine yagano har abada bazata ta6a daina son wanda takesoba,
sam arayuwarsa bai ta6a tunanin auren wadda wanine azuciyartaba.lokacinda suka cika kusan shekara guda agarin bata iya doguwar tsayuwa sbd rashin lafiya takeyi sosai,
aman jini takeyi saidai bata ta6a bari yasaniba,
wani irin haske da rama tayi sosai,
shi kansa baya cikin kwanciyar hankali yayi ramar sosai sbd ita,
komai ya tsaya masa sbd ita baisan ya zaiyi ya kawo sauyi arayuwar auren nasuba yayi iya qoqarinsa abu ya gagara qarshe dai yagano aurensu bazai ta6a zama kamar kowane aureba,
