Washe gari sai guraren qarfe goma ya tashi
Idanuwansa kawai ya bude ahankali ya sauke kan bedside clock yaga time.Lumshe idanuwansa yayi cikin wani irin zafin zuciya da takaici sbd yagane allaurar da akai Masa kasancewarsa qwararren likita..
Tashi zaune yayi Dan Babu Wanda yakeson ya amsa Masa tambayoyinsa kamar mum sbd idan ba itaba ya tabbata Babu Wanda zaisa ayi Masa alllurar bacci yanason yasan dalilinta nayin hakan.
Zuro qafafunwansa qasa yayi sai akan wayarsa da sauri yakai hannu Yana cewa,
No no no no please..
Kaca kaca screen 'din yayi ya shafe ba'a ganin komai kamarma ta mutu gabaki 'daya.
Yanda zuciyarsa ke tafarfasa ne yasa ya aje wayar tareda nufar toilet yayo alwala yayi sallar asuba Yana qara Jin zafin allurar d sbd irin yanda yayi lattin sallar.
Yana idarwa ya miqe tareda 'daukar wayar ya nufi gurin mum.
Yana shiga ya tararda suna rigima da taheer akan yanason Layla tunda Wanda ke nemanta ya fasa itakuma tace Sam ba'a zuriarta ba 'yar tsintuwa sbd tasan 'ya 'daya Tak Abba yakeda ita.
Basusan dashiba saijin tayi ya riqo hannunta yasaka Mata wayar idanuwansa taf da hawaye sunyi jajir Yana qoqarin rage zafin rai da tsananin fushin dayazo dashi yace,
Cikakken bayani zakiyimin akan abunda yasamu wayana bayan kingama fadamin dalilinki nasawa aimin allurar bacci.
Kallonsa tayi takalli taheer dashima fuskarsa ke 'daure sosai
Itakan wane irin masiface ke Shirin rufo Mata ta hanyar 'yayanta akan mata shi dawood Nur shikuma taheer Layla.Mai aikice ta qaraso da warm milk da mum tasa adafa Masa
Wata gigitacciyar tsawa ya daka Mata wadda tasa mum firgita tana kallonsa cikin tsananin mamakinsa tace,Mi'amor komai nayi I did it for your own good,,I mean can't you see hw stress and....
Meyasamu wayana?
I know you broke it mum,
Why?
Why? Did you realize wat you did by doing this...idan har kinyine danki rabani da ita then you are wrong,
You are wrong mum sbd har abada bazai ta6a faruwa,
You called me your love but I don't see anything like that anan mum,
Zan Baki shawara amatsayina na 'danki,
Kibarwa Allah komai yayi ikonsa ayanda yaso sbd idan Kika matsa akan haka ina gujemiki abunda zai biyo baya sbd Zaki iya rasa 'dan ki har abada..and one more thing maganar aure banayi bazanyi ba
And i'm leaving this house now coz I can't spend another minute hia,,I feel suffocated.Riqosa tayi niyaryi ya juya yabar gurin sbd hawayen idanuwansa zasu iya zubowa kowaneokaci.
Duk wani Abu dazai buqata ya ha'da ko wanka baiyiba ya fito har lokacin zuciyarsa zafi da ra'dadi take masa ba abinda yake son gani kamar Nur sbd ganintane kawai zai yaye Masa qunci da ciwon da zuciyarsa ke Masa.
Kallon taheer mum tayi cikin tashin hankali tace,
Honey please kaje karka barsa yatafi please don't let him leave....
Girgixa Kai yayi cikeda tausayin 'dan uwansa dashi kansa da Allah yabasu selfish mother da she can do anything to get wat she wants.
Fita yayi ya nufi gurin dawood Amma cikin rashin sa'a Bai tarardashiba ya wuce.
Gurin mum yakoma ya kalleta yace,
Yatafi and and I will follow his steps anytime soon nima zan iya tafiya idan Kika hanani samun Layla.
Juyawa yayi ya wuce yabarta da Baki sake,
Takaici da 6acin Rai taji yataso Mata Dan sunga tana lalla6asu sukeson su riqa yin abunda sukaga dama,
Zata nuna musu itace ta haifesu basune suka haifetaba.Taheer na Isa bedroom 'dinsa yakira aleeya yafada Mata shizai auri Laylan idan tabasa dama yayi alqawarin Bata farin cikin dazata manta komai.
Bata nuna Masa amincewaba tace yabari zatai magana da laylar tukuna.Daganan direct gurin dad yanufa yasanardashi shi yanason layla zai aureta
Mamaki sosai dad 'din yayi kafin yayi farin ciki ba 6ata lokaci ya 'daga ways yakira abban yafada Masa kusanma abban yafi dad din murna sbd koba komai 'yayansa zasuyi aure gida 'daya bazasu rabuba Nan suka yanke ha'dawa ayi tareda nasu aleeya ayi gabaki 'daya.Hamdala taheer yayi tareda rungume dad din yayi Masa godiya tareda fada Masa zaiyi tafiya zuwa gobe zaikoma Miami akwai wani aiki daya baro Bai qarasaba.
Washe gari da taheer da dad sukai tafiya akabar mum kadai sai ma'aikatan gidan.
Tun jiya takasa sukuni mafita kawai take nema ta raba dawood da son Nur ta cusa Masa na aleeya.
Shi taheer yasha da ita sbd Batada wani za6i tunda yafadawa dad 'dinsu tasan Babu abinda zai Hana auren zata Bari daga baya tayi maganin laylar matuqar ta yarda tashigo gidanta amatsayin suruka.,
Yanxu damuwarta da rashin sukuninta na dawood ne.Waye zai raba dawood da Nur????
Shine taketa kaida kawo tun safe tana fada.
Ajiyar zuciya tasake tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,
SARAAH..
wayarta ta 'daga Babu 6ata lokaci takirata.
Hello Mrs Damien"""tafada cikeda mamakin ganin Kiran mum awayarta.
Hey sweetheart hw are you?
M gud mum wannan surprised call 'dinfa I hope zakice nafadawa family na zakuzo ganinsu ne.?
Dariyar qarfin Hali mum tayi tareda cewa,
Yes sweetheart shine abinda nakeso muxo muga familynki akai qarshe ayi auren Nan naki da mi'amor but I don't think that will ever happen.
Wait Mrs Damien mekike fada ne I don't get wat you're saying.
Yes sweetheart idan harkinason mi'amor for your self Dole duk abinda kike ki aje kizo Nigeria.
Mum wai are you serious?
I mean like seriously..Yes darling kibari idan kinxo zan Miki bayani okay?
Ko amsa Bata bayarba ta datse Kiran tareda sallamar client 'dinta dake gabanta takira p.a dinta tace duk abinda yake ya aje yaje duk yanda zaiyi yayi Dole gobe ta sauka a Nigeria.
#mamuhgee
#vote
#comment.
