17

10.1K 1K 103
                                    

Washe gari motar asuba tabi zuwa Lagos taso shiga jirgi Amma sbd karma ta tambayi ammy kudin ticket kamar yanda tasabab idan zata gudun kar ammy tace tayi zamanta yasa tashiga mota
Tunda suka dau hanya ta kwantarda kanta tareda rufe ido cikin ranta tana kissima yanda zata Hana auren Layla auren mijin yadawo kanta.

Lokacinda ya sauka a Abuja taheer ne da kansa ya daukosa daga airport cikeda murna da farin cikin ganin 'dan uwansa suka rungume juna sbd sun Dade Basu ha'du shi taheer baya zama sbd aiki shikuma Bai cika zuwaba tunda su mum suka tarki zama Nigeria.

Koda suka iso gidan anshirya Masa dishes na lunch kala kala cikeda farin ciki mum ta qarasa ta rungumesa atare itadashi sukace,

I missed you my love.

Itakuma tace,

I missed you more mi'amor.

Direct part 'dinsa da aka gyara aka zuba komai yanda akasan yanaso da duk sauran abubuwan amfaninsa duka mum tasiyo tazo dazu tun daga can aka Kai luggages dinsa.

Saida yayi wanka ya kwanta ya huta Yana tashi Nur yafara Kira tana ganin numbers ta Nigeria tasaki wani lallausan murmushi sbd farin ciki da wani irin kwanciyar hankali dataji ya shigeta.

Tana 'dauka taji lokacinda ya sake ajiyar zuciya ahankali tareda Kiran sunanta can qasan maqoshinsa Wanda dagashi har ita Saida tsigar jikinsu ta tashi.

Akasalance tace,

Do you really have to do this Everytime?

Lumshe Ido yayi tareda sake bu'de Baki daqyar yace,

you're my life Nur,,I love you and know all I'm feeling is I can't live a life without you in it,
Duk duniya yanxu Kece kawai abinda nake nake tsananin son samu so just tell su ammy su shirya I'm coming tomorrow.

Ajiyar zuciya tasake ahankali tanajin sabuwar qaunarsa da sonsa na qara shigarta murya qasa qasa itama tace,

Thank you.

Qasa qasan Shima daqyar yace,

Tell me how much you love me...

Words can't describe it just keeps one thing in mind har lokacinda numfashina zai bar jikin Kaine ka'dai zaka zauna azuciyata wannan matsayinkane Kuma alqawarine bazai ta6a canxawaba.

Shiru yayi jikinsa na qara mutuwa sbd yazamo cikin jininsa jikinsa yake  duk lokacinda muryarta ta sauka cikin kunnuwansa sai dukkanin jikinsa ya mutu saidai dayake dama baida hayaniya ko kazar kazar baza'a ganeba saisu jass kawai dadukasan halin abinsu.

Shiru sukayi dukkaninsu tsawon lokaci can Kuma murya a kasalance yace,

Do you miss Nur.

Murmushi tasaki kafin tace,

No.

Wat"""yafada da sauri tareda tashi daga kwancen zaiyi magana ta rigasa cikin murmushi Mai sauti tace,

Silly"""tafada ahankali tareda kashe wayar ta aje fuskarta na qara wanxuwa da murmushin data kasa dainawa.

Aleeya data sata gaba da kallo harda tagumi sai dariya take tana ganin ta kashe ta tashi zaune a tsakiyar gadansu tana leqa fuskar laylar dake nuna tsananin sonda zuciyarta ke Masa tace,

Hmmm anya Layla dawood 'dinnan Bai tafi da fiyeda rabinki ba yabar Mana saura.

Harara ta watsa mata still fuskarta 'daukeda murmushi batareda ta Bata amsaba.

Sake matsowa tayi jikinta ta kwantarda kanta a cinyar Layla din tace,

Layla koda Ni bansamu soyayyar mi'amor ba zan dawwama cikin farin ciki ke kinsamu soyayyar Wanda kikeso tunda bamu taru mun rasaba.

DAWOOD✅Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon