NOT EDITED
girgixa kanta tayi tareda bubbugasa da hannu tana sake bude idanuwanta dasukai jajir tana qoqarin son qara fahimtar me taheer din yake fada,
kasa jurewa sauran zancen nasa tayi tai wurgi da cup din hannunta cikin bugaggiyar murya tace,
bazaka ta6a rabani da dawood ba kabawa wata,
dawood nawane nikadai,
nikadaice zan auresa,
babu wanda ya isa yarabani dashi...kicin tayi lalabo wuqa ta fito tana cigaba da cewa,
dawood nawane nikadai,,,
tana kawowa qofar dakin yana fitowa bata tsaya komaiba ta caka masa wuqar,
qara da salati mai qarfi yasake lokaci daya tareda zubewa qofar dakin tana ganin haka tayi dakinta da gudu daidai fitowar mum da gudu cikin tashin hankali kuma taga shigewarta 'daki da gudun amma batabi kantaba tayi tsakiyar palon inda tajiyo qarar taheer,
arikice layla ta taso tareda durqusawa gabansa tana kiran sunansa batasan sanda tasa hannu ta birkitosaba wani razannan ihu tasaki ganin wuqa da a gefen cikinsa bata tsaya komaiba ta zare wuqar daidai isowar mum gurin tareda kunnu wutar palon taganta da wuqa ahannu ga taheer din kwance cikin jini,
wani mahaukacin ihu da qara tasaki tareda jefar da wayar hannunta ta qaraso da gudu hartana faduwa ta damqosa tana kiran sunansa da qarfi cikin tashin hankali,
kuka layla keyi sosai nan su Nana da sauran masu aikin gidan suka fito arikice dan harsunyi nisa a bacci tuni,
cikin tashin hankali nana takirawo aleeya tana zuwa da gudu ta tsaya turus ganin abinda ke faruwa arkice ta matso cikin tashin hankali tace,
mum muje hospital tun kafin wani abu yasamesa.
kuka mum keyi sosai saidai aleeyarce tafita da gudu takirawo maigadi suka shigo shima arude ya daukar musu shi yasaka amota,
jiki na rawa takalli mum tace,
mum muje.
da sauri mum din ta miqe hartana hadawa da gudu suka wuce da mugun gudu dan har lokacin kamar yana numfashi,
tun ahanya takira dad tana kuka tasanar dashi masifar data samu taheer nan take ya katse kiran yace komai tsakar dare zai taso asuba ya iso sbd yana ghana.kasa miqewa layla tayi saida Nana ta dagata daqyar sbd rawar da jikinta keyi matuqa ga kukan tashin hankali datakeyi.
suna isa asibiti daqyar aka kar6esa da sharadin saisun kawo police sbd police case ne,
share hawaye mum tayi cikin wani irin zafi da 6acin rai mai tsanani tacewa aleeya tazauna ita zataje takira police,
daga asibiti direct office na commisioner of police ta nufa nan take aka bada motar police.
saraah kuwa tana shigewa daki jikinta yafara rawa dan tuni giyar tasaketa tsabar tashin hankali ta dora hannu akai tace,
na shiga uku menayi,
yanxu shikenan mum taganni na kashesa nima kasheni zaayi wayyo allah na shiga uku,birkice kayanta tayi ahaukace tafara neman passport dinta acikin daren zata gudu bazata bari akamata ba,
wayarta ta dauko hannuwanta na tsananin rawa ko zama wayar batayi dakyau ahannunta ta danna kiran siyama tana tsiyayo hawaye,
siyama na dauka ta fashe da kuka tace,
siyama ina cikin matsala wlh kasheni zaayi bansan ya zanyiba,
bansan meyasa nakasa riqe kainaba na kashesa,
siyama kitaimakeni na kashe taheer....tashi zaune siyama tayi daga kwancen datake tareda saukowa daga gado tace,
me kike cewa?
wlh siyama bana cikin nutsuwata ba kashesa nayi niyaba,,,fada mata komai tayi cikin tsananin kukan tsoro saijintayi siyama ta kashe mata waya.