Ranar ammy taso yazo Nan yaci abinci Taredasu Amma Layla tace aa sbd ganin ammyn sai 'doki takeyi.
Washe gari Dole ta qyale ammyn tasa Nana takirasa ya Dade kafin yazo tace yaci abinci dasu Bai musaba sukayi lunch tare duk ya hanata sukuni da shegen kallonsa ammy madai badan ta qoshiba ta miqe sbd shiyake kallon itakejin kunya.
Suna gamawa Bai tafiba suka zauna Palo su sufyaan suka Kira Yana dauka suka gano a inda yake sukace yabawa Laylan.
Kar6a tayi Cikeda wayewa da Raha suka gaisa da ita dukkaninsu kafin suka kashe.
Kallonsa tayi tana murmushi tace,
Your friends are nice.
Nafada Miki I have the best friends in the world.
Nima nafada maka I have the sweetest,the nice's friend and also a sister in the world.
Dariya sukayi dukkaninsu ahankali kafin ya miqe ya tafi.
Wani irin feelings sukeji Mai qarfi gameda junansu sbd sabo da shaquwar dayashiga tsakanisu cikin kwanakin ga uwa uba ammy data 'daure Masa ta hanyar koya Masa cin dishes kala kala wasu baima iya cinsuba haka zasu zauna ana koya Masa cinsu sometimes idan yanaci saiya kirasu sufyaan Yana nuna musu sunai Masa dariya sbd su San 'dan San wasu abubuwan sun Saba cinsu a gida.
Ta 6angarenta kuwa bata fadawa aleeya ba tabarshi as a surprise to her duk Randa suka dawo duk da dai yanada wuya su ha'du sbd yakusa kammala abunda yakawosa yakoma.
Wani irin so yake Mata dabaisan kalarsaba Dan kuwa jiyake there's no way dazai iya rayuwa babuta,
Sanyinta,da yanayin rashin son hayaniyarta kamarsa yasa baya iya sukuni Sam yanzu batareda yakirata ba takaima yafara zama kamar wani chewing gum 'dinta Dan kusan yawancin kwanaki tare suke zuwa school.Aduk lokacinda ko sunansa ta tuno sai murmushi da farin ciki sun sauka a zuciyarta musamman takejinsa wani babban 6angare na jikinta dabazata iya rayuwa Babu ba.
Yini sukeyi agida tare idan zata fita ya dinga binta da kallo kenan kamar Mara lafiya baida sukuni ko walwala saita dawo.
Ita Kam ammy ba abinda yafi Mata haka da'di yanzu aleeya kawai tarage itama kullum saita Mata adduar Allah yakawo Mata nata Dan tuni ta sanarwa abban Layla tasamu miji farin ciki sosai yayi saidai baitambayi komai akansaba yace abari saiya dawo Dan next week zasu dawo.
Da daddare daqyar tasamu yabarta ta waya sbd Dan yanda ya narke mata sosai ita har mamakinsa take sbd da gani mum dinsa ta 6atasa da gata kamar yaro ga yanda ya iya narke Mata akan saitayi masa firar soyayya yaji Dadi shi bai iyaba shi tasa kalar soyayyar ta Ido ce Dan kuwa idan ya zuba Matasu wani lokacin ko motsi Bata iyayi Kuma ba ruwansa da duk Wanda ke guri zuba Matasu yake ga idanuwan badai kashe jiki da rikita mutum ba.
Daqyar tasamu ya haqura ta kashe wayar tareda danna Kiran aleeya.
Cikin sa'a tashiga.
Tana dauka kusan atare suka saki ajiyar zuciya kowanne bakinsa da magana.
Cikin farin ciki aleeya tace,
Oh my...my layla I missed you so much na matsu nadawo I have alot to tell wlh.
Murmushi Mai sauti tayi tana cewa,
Dagajin muryarki kina cikin farin ciki is there anything I shud know.
Dariyar Jin Dadi tayi tareda gyara kwanciyarta a gadon bedroom 'din mum data dawo da kwana Nan sbd kawai hotonsa dake 'dakin ta shafi hoton tana lumshe Ido tace,
Inasonsa Layla,,,,
Ina tsananin sonsa infact ban ta6a son wani da tsanani hakaba kamarsa....Lumshe idanu Layla tayi sbd fuskar dawood 'dinta data Fado Mata a Ido.