NOT EDITED
bayanta baffa dahiru yabi da kallo yana jinjina alamarin kafin ya nufi dakinsa ya zauna yana sake nazarin alamarin,
baifitoba sai maraice yayi alwala shidasu dawood suka wuce masallaci har lokacin sosai dawood yake cikin yanayi na jin zafin abinda laylar ke shirin yi duk da dai yasauki alqawarin kobataso saiya aureta yagaji da wannan azabar datake gana masa arayuwa.amasallaci bayan sallar magriba baffa yasamu mal liman yayi masa bayani akan rasuwar mijinta dakuma auren dasukeson adaura,
dogon naxari mal liman yayi kafin ya nisa yakalli baffa dasu dawood din yace,
tabbas zata iya aurensa tunda wancan qaninsa din kunce yarasu saidai dole sai bayan tagama takaba...
shiru baffa yayi na seconds kafin ya dago murya a tausashe yace,
eh to babu wani abu na aure daya ta6a shiga tsakaninsu hasalima basuyi rayuwar irinta zaman aureba kuma kafin rasuwarsa yabata sakinta ahannunta.
sake gyada kai mal liman yayi yasake cewa,
eh to zasu iya aure amma idan son samune zaifi subari zuwa gaba kamar......
katsesa sufyaan yayi dafara zayyano masa komai daga farko zuwa qarshe.,
mal liman yayi shiru tareda qurawa dawood ido yana jinjina kai yace,
sannu dauda.
kallonsa kawai dawood yayi da lazy eyes dinsa shidai fatarsa kawai ace zaa daura auren.
tabbas daura musu aure bai haramta ba dama dai nasone subari tayi kwana biyu kamar zaifi amma tunda abun hakane gobe takasance alhamis jibi ranar jumaa insha allah da safe sai a daura auren,allah yasa hakan shine mafi alkhairi arayuwarsu duka.
amin sukace dukkaninsu dawood najin wani sanyi da kasala na shigarsa sbd yasan babban burin rayuwarsa ne zai cika idan NUR dinsa tazamo matarsa,
godiya sukai masa sosai kafin suka miqe,basu koma gidaba saida sukai sallar isha suna komawa suka shige daki duk da zuciyarsa a tsananin takure takedason ganinta amma hakanan ya daure sbd yasan idan ya matse mata zatacene bazatai aurenba gwara yabata space har yasamu adaura auren,
yanaji inna halima nayiwa baffa complain taqi fitowa har lokacin kuka takeyi yayi zuru tareda mayarda dukkanin hankalinsa kan qofar dakin datake,
sufyaan dake qoqarin sanardashi maganarsu saraah ganin hankalinsa baya jikinsa yasa yabari harsai bayan auren idan hankalinsu yadan kwanta.da tsakar dare kasa kwanciya yayi sbd yana jiyo ajiyar zuciyarta alamun idanunta biyu sam bayada sukuni na jiki dana zuciya sbd rashin sanin halinda take ciki.
har asuba yana zaune ko gyangyadawa baiyiba sbd ita.,
suna fita sallar asuba itama tafito daqyar sbd ko gani batayi sosai sbd kumburin idanuwanta na kuka,
alwala tayi takoma ta tayarda sallah a zaunema tayi sallar sbd wani irin mugun jiri da zazza6i mai zafi dayake cinta,
tana gamawa ta dunqule gurin tana kakkarwa tareda wani irin wahalallen nishi.
hankalin inna halima ne yafara tashi ganin halinda take nan tazauna jiran dawowarsu baffa basu dawoba saida gari yayi haske sosai.
maganin zazza6i baffa yabayawa innar abata shima bayason matse mata dankarma ta tayarda maganar rashin son auren,
dawood ma ganin zai iya rasa nutsuwarsa yasa sufyaan jansa suka fita bayan gidan,
zama sukayi bakin wani dutsi ya rufe idanuwansa ahankali tareda jinginarda kansa jikin ice zuciyarsa na qara rasa sukunin halinda nur din ke ciki,
tabbas NUR itace rayuwarsa,farin cikinsa,baqin cikinsa,qaddararsa dakuma burinsa aduniya.
