NOT EDITED
koda ya isa adamawa ko hotel 'din dazai kwana bai isaba saida yanufi gidansu aleeya,
bai wani sha wahalaba ya isa gidan saidai cikin rashin sa'a mai gadi yasanar dashi suna lagos acan sukefin zama,
dafe goshinsa yayi cikeda damuwa kafin yayiwa maigadin godia ya wuce,
hotel room yakama yayi salloli tareda ordern ruwan lipton da black coffee sbd hakanan yakejin baya iyacin abinci mai nauyi.
shiru yayi tareda qurawa ruwan lipton din ido wannan shine karo na farko dabaiyi ordern giyaba tun girmansa,
yau kuwa sam baya shaawar shanta sbd tunda yaga result din dawood yafara shanta yaji ya tsaneta sbd yasan zataiwa amininsa illa dan haka koda zai hanasa shanta saiya fara raba kansa da shanta wannan alqawarine ya dauka bazai qara shantaba insha allah,kur6a biyu yayiwa lipton din ya ajiye sbd kwata kwata bayada apatite,
wayarsa ya 'daga yakira wanda yakeson gani yace yazo yasamesa a hotel,
cikin qanqanin lokaci wani babban saurayi ya iso yayi knocking room din yabude masa ya shigo,cikin girmamawa yace,
dr barka da isowa nigeria,
murmushin qarfin hali maskan yasaki tareda cewa,
thank you sambo,aiki zan baka kuma koma meyene inason samun aikina ta kammalu zuwa gobe zan biya ten times na amount din aiki.
washe baki sambo yayi yana kar6ar wayar maskan dayake nuna masa hoton Nur,
bude bluetooth dinsa yayi yatura hoton cikin wayarsa tareda miqawa maska wayarsa yana sake kallon hoton yace,
dr wannan aikin anriga angamasa kafin safe insha allah sbd yau komai dare saina gano komai gameda ita,
daga masa kai kawai yayi tareda miqa masa envelope,
kar6a yayi ya fice yana kiran wanda zaifara tayasa aikin.
washe gari qarfe goma sambo yagama hado masa duk wani tarihi akan nur har asalin inda tayi zaman bara kafin mahaifinta ya rasu da address dinsu na lagos.
lokacinda yakawowa maska bayanin da wasu sabbin hotunanta datake tareda aleeya a instagram,
shiru yayi tareda qurawa hoton ido zuciyarsa cike fal da farin ciki mara misaltuwa sbd yasamowa abokinsa farin cikinsa,
bai tsaya 6ata lokaciba ya harhada ya wuce airport ko takardun bayanan bai kar6a ba ya wuce sbd matsuwar yaje yaga nur da aleeya suyi magana atare,
tunda yakama hanyar airport yake kiransu jass amma babu wanda wayarsa ke shiga,
sukuwa sunacan hankali amatuqar tashe sbd jikin dawood aya rikice musu amai kawai yake shararawa mum tayi kuka har idanuwanta sunfara kumbura amma duk da haka batajin zata bari a 'daga bikin gwara ayi matarsa tayi jinyarsa idanma wata qasar za'a fitar dashi,
ganin yakasa samunsu saiya yanke shawarar kiran numbern nur da sambo yabasa,
qaramin tsaki yasaki lokacinda yaji wayar bata zuwa,
shiru yayi tsawon lokaci kafin ya yanke shawarar kiran numbern aleeya yafara fadamata komai ta waya kafin ya iso,numbernta da duka cikin binciken sambone aka samo yakira,
zaune take bakin gado ta tallafe kanta dake tsananin ciwo tayi zurfi cikin tunani,
ringing din wayar dake kusada itane yasa tadan juyo ahankali takalli wayar tareda lumshe idanuwanta dasukai jajir ahankali tasake ajiyar zuciya tareda dauke kai sbd hoton dawood ne kwance akan screen din wayar ta aleeya,