Ranar dasuka Fara kwana a hostel aleeya na ganin dare yayi tsoro Yakamata tafara kukan neman gida murmushi Layla tayi cikeda tausayin aleeyarta tadawo kusada ita ta kwanta tana rarrashinta itakam data Sha kwana bola da titi sam bataji tsoron kwana anan dinba kawai dai sai kewar gida dasu Bilal da ammy.
Kuka sosai aleeya tayi duk sai laylar hankalinta yatashi itama saidatayi kukan.
Tun ranar kullum tare suke kwana a gado 'daya sbd kullum sai aleeya tayi kukan dare Kuma idan ba Layla kusada ita Bata iya bacci ahaka harsuka Fara sabawa da yanayin rayuwar makaranta sukadai,
Sam basuyi wasu qawaye ba sbd basason wani yashiga tsakaninsu Wanda ammy tayi musu fada sosai akan duk sukayi qawaye to saisun shiga tsakaninsu shiyasa Sam sinqi yarda suyi qawa ko 'daya Dan kar a rabasu sbd zuwa lokacin jisuke bazasu iya rayuwa ba junaba..(ha'di daga Allah).
Sosai aleeya ke dagewa tana fahimtarda Layla duk karantunda ake musu itama Kuma Layla itake dagewa kulada komai nasu gurin zamansu na hostel sbd duk wata wahala aleeyar Bata Saba da itaba.
Ahaka harsukai exams sukayi hutu
Ranar dasuka dawo Bilal da ammy murna kamar me Amma su ammy sunsha dariyarsu ganin yanda suka rame sukai duhu musamman ma aleeya da Bata Saba da wahala ba ko kadan.
Sukuwa mamakin ganin girman bilal sukayi Dan dama shi jikinsa irin Mai girman Nan ne.
Tunda suka dawo hutun gaske sukeyi Dan koina basa fita so biyu kawai suka fita 'daya tareda ammy 'daya Kuma sukadai direba yakaisu gidan qawar ammy gurin birthday party din 'yar qaramar 'yarta.
Kamar qyatawar Ido hutunsu ya qare suka koma school.
Sannu ahankali harsukai ss3 lokacin tuni 'yan matanci ya bayyana Dan kuwa kowaccensu tazama budurwa kuma ba laifi kowace nada sama da qasa daidai jikinta duk da dai dukkaninsu baza'a kirasu da sirara ba ko Masu qiba jikinsu saidai aleeya tafi Layla jiki kadan ita Kuma layla tafi aleeya tsawo kadan ta 6angaren kyawu kuwa saidai ace Masha Allah Dan kuwa 'yan matan na ammy sunadashi Layla kyawunta na buzayen asali yafito aleeya kuwa kyawun asalin fulanin adamawa.
Ranar dasuka gama makaranta ranar abbansu yayi musu kyautar manyan wayoyin da kyautar zuwa umrah gabaki 'dayansu gidan Nan suka hau murna da tsalle tsalle.
Bilal zuwa lokacin Yana js3 ne Amma girman jikinsa harya kusa kamosu Kuma lokacin tuni yarinta ta tafara tafiya yafara sanin kansa Dan har musabaqar qur'ani yashiga sabuwar islamiyar da aka kaisa bayan tafiyarsu makaranta Kuma yazo da uku kuma hakan ba qaramin alfahari yasa su Abba ba sbd zuwa lokacin kowa tunanin yake dukkaninsu 'yayansa ne.
Satinsu biyu suka wuce umrah dukkaninsu.
Lokacinda layla taganta gaban 'dakin Allah tayi kuka sosai sbd ko acikin mafarki Bata ta6a gangancin tunanin samun irin wannan rayuwarba saidai batasan Mai Allah yatanadar wa rayuwarsu agaba ba Ashe,.
Tayiwa mahaifanta dasu Abba addua ba iyaka kafin musamman ta roqi Allah karya kawo komai na duniya dazai shiga tsakanin qaunar dasukewa juna itada aleeyarta sbd aleeya wani 6angarene na rayuwarta dasai mutuwace zata rabata dashi duk da tasan qaunar da aleeya ke Mata bazama ta kwatanta da wadda ita take mataba.
Tana gamawa ta juyo ahankali ta nufi gurinda su aleeya da Bilal ke jiranta sbd ammy da Abba suna tareda baqi a masaukinsu yau Basu fitoba.
Fitowa sukayi daga masallacin suka tsaya wani tsadadden gurin Shan coffee da cake sbd shine yawanci Layla fitiso takasa iya cin abincin garin aleeya da Bilal kuwa komai rashin da'din abinci sai sun gwada cinsa.
Su aleeya ne agaba tana bayansu wayarta take dubawa kanta na qasa.
Karo tayi da mutum gabanta yayi mummunan fa'duwa saita kasa 'dagowa ta durqusa qasa ta 'dauki wayarta ta ta6a da sauri zata wuce......
I think you're taking what's mine miss...
Cak ta tsaya jikinta ya 'dauki rawa Nan take Sam hakanan takejin batason ha'da Ido da koma waye
Saurin kallon hannunta tayi taga ba wayarta bace ta 'dauka da sauri ta miqa Masa batareda ta juyoba..
Hannu yakai zai kar6a....
Dawood...aka kira sunansa daga bayansa kar6ar wayar yayi batareda ya sake kallon gefentaba ya juya Yana kallon maska daya kirasa..
Come on man the coffee will get cold.
Qarasowa yayi ya zauna suka Fara Shan coffee 'dinsu suna tsokanar sufyaan dayayi wani iri waishi missing Mariam 'dinsa yake amatse yake dasu koma gobe.
Murmushi dawood yayi yace,
You know you're unbelievable sufyaan Sam idiot baka gajiya da sex.
Dariya maska yasaki Yana sipping coffee 'dinsa yace,
Oh my see who's talking..I think gwara sufyaan sbd ko yaushe yaso zai daina idan yaso Amma kana tunanin that crazy girlfriend of yours zata barka gaba...
Tayani fada Masa maska and the idiot keep saying she's not my type I'm just managing Amma he's always inside her legs...
Murmushi yasaki Jin wulaqancin dasuke Masa yace,
Two idiots.
Amma deep inside sun tado Masa da kewar saraah dinsa taso biyosu yaqi yarda sbd matuqar tana kusa dashi bazai iya haquraba saidai har abada baya fatar aikata makamancin hakan gari Mai tsarki suda sukazo ibada.
Kallonsa maska yayi Yana cewa,
Ji Wanda kewa wani fada he's missing his chewing gum already.
Qyalesu yayi tareda lumshe fararen oily eyes dinsa yanajin yanayi na farin ciki na shigarsa.
Zama sukayi aleeya ta kar6o musu coffee da cake Fara Sha sukayi suna fira Wanda duk yawanci surutun aleeya da Bilal ne ita kuwa lumshe idanuwa tayi ahankali tana Shan coffee 'din tana sauke ajiyar zuciya ahankali sbd har lokacin jikinta sanyaye yake da kukan datayi gaban kaaba.
Ta cikin qatuwar mirror glass din dake cikin gurin ta hangosu zaune a table 'din bayansu,
Su ukune kowannensu na dukan kyau da hutu daya bayyana jikinsu qarara.
Ido ta qura Masa zuciyarta ta buga da qarfi tayi saurin sunkuyar dakai tareda aje cup din hannunta ta miqe tace,
Ta gama su tafi Dan dama Suma sun gama.
Tunda suka dawo masauki ta kwanta shiru tanajin numfashinta na fita da sauri daqyar tasamu bacci ya 'dauketa tattareda sabon alamari atareda ita.
#mamuhgee
VOTE
COMMENT
