Tana Isa school din takira Wanda Abba yace zai tayata da komai yazo bakin mota yasameta suka shiga ciki.
Basu samu kansuba sai yamma Kuma still Bata gama musu registration din dukaba
A gajiye suka baro school din ta ajesa gidansu kafin ta wuto gida.Kodata Isa gida a Palo ta tararda ammy
Agajiye tace,Ammy kina kallo ne?
Eh wai news nake kallo akan yanayin weathern yau.
Ok to ammy Bari nashiga na'dan watsa ruwa yau na gaji sosai.
Tana shiga ta zame doguwar rigarta ta tu6e ta fada toilet.
Wanka da alwalar sallar magrib tayo tana fitowa wata handless gown tasaka Mara nauyi ko kadan ta 'daure gashinta tasaka hijab tayi sallar magrib tana idarwa ta cire hijab din tafito Palo lokacin ammy ta shige daki Nana kuma na kicin.
Abincin da Nana ta dafa ta 'debo kadan a plate tazauna a dining taci ta miqe tayi gurin ammy acan dakin tayi sallar Isha kafin ta fito ta nufi bedroom'dinsu ta kwanta takira number da aleeya takirata dashi 'dazu Amma baya zuwa ta kashe wayar ta rufe idanunta Nan take bacci yayi gaba da ita.
Daga airport wani family brother 'din maska ne yazo ya 'daukesa yakaisa lafiyayyan ha'dadden flat 'din maskar dake Nan Abuja yaso ya sauka gidansu Amma su mum dinsa are not around so bazai iya zama acanba tunda ba dadewa zaiyiba zaikoma he's just hia for a two weeks seminar Dan haka zai zauna gidan maska ne harya koma koba komai gidan da anguwar sun mishi sbd securitynsu and ba hayaniya.
Saurayin na ajesa gidan yajuya yatafi tareda Kama hanyar kaduna cikin Jin dadin yau ga Lamborghini car din Yaya maska ahannunsa Dole yaje kaduna ya yaqi friends dinsa sbd yayi tunanin shikenan dan already ya siyo duk wasu drinks da abubuwan da maska yace dawood 'din buqata duk da wasu abubuwan ma saidaya Sha uwar wuya kafin yasamesu.
Lafiyayyan babban bedroom din dake palon yashiga ya aje luggage 'dinsa ya tu6e Kai tsaye ya fada toilet..
Kallon shower creams da toothpaste dasu shaving creams 'din da aka jere a toilet din yayi ya 'dauke gira 'daya tareda tamke fuska yace,
Common simple words this fools basa ganewa I can't touch this tckless of putting it on my skin..
Bedroom din yakoma ya 'dauki wayarsa ya dannawa maska Kira
Yana 'dauka hankali kwance ba hayaniya yace,Maska do you plan to kill me ne anan....?
Kallonsu jass dasuke tare ne a wani vip bar ahankali yace,
That foolish boy ya kwafsa.
Look dawood I know ba lallai ne asamu dukkanin abinda kakeso acanba so please manage da abubuwan da'aka samu doc...
Tsaki yayi tareda kashe wayar ya jefar kan gado yanajin skin 'dinsa na Masa wani iri I need to shower yafada tareda miqewa kaman yayi kuka ya bude akwatinsa ya Ciro wani shower gel da foot 'dinsa kawai yake wankewa dashi ya koma toilet din dashi yayi wanka Dole.
Mansa ya fitar tareda oil na Neutrogena elixirs sai spray dinsa na possess ya shafa sai turarensa na tareda saka white trousers da white singlet ya Dora white jallabiya asama da white hula Nan take yakoma kamar wani kamilallen uztazun balarabe.
Sallah yayi Yana idarwa ya cire jallabiyar da hular ya nufi Palo Kai tsaye fridge ya bude ya 'dauko milkshake da aka jere Masa aciki da champagne sai bottle wata dasu samosas duk na ShopRitekitchen.
Kunna tv yayi tareda zaunawa ya canxu Tasha zuwa sports ya bude laptop dinsa Yana Kai milkshake din bakinsa.
Ahaka yayita aikinsa har dare yayi sosai yakashe komai yaje yasaka kayan bacci Masu tsananin laushi kamar wani mace ya kwanta bayan.
